|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook, IG Wala, yayi da’awar cewa wasu mazauna Sokoto na kauracewa muhallansu, suna tsallaka kogi saboda masu fashin daji.

Hukunci: Gaskiya ne, DUBAWA ta gano cewa bidiyon ya nuna yadda mutane suke ta kokarin guduwa daga yankin da ke Gabashin Sokoto bayan wani farmaki na ‘yanfashin daji.
Cikakken Bayanin
A ranar 4 ga watan Augusta,2026 wani shafin Facebook mai suna IG Wala, ya wallafa wani bidiyo kamar yadda za a iya gani a wannan (link) ya nuna yadda mutane ke tsallaka kogi inda yayi da’awar cewa al’umma ce a Sokoto suke kauracewa muhallansu saboda dalilai na ayyukan ta’addancin ‘yanfashin daji.
An rubuta taken labarin da cewa “Wannan ba bidiyon mutane ba ne a bakin ruwa suna shakatawa face mutane ‘yan Najeriya masu biyan haraji suke kauracewa ayyukan ‘yanfashin daji a Gabashin jihar Sokoto.
“Suna kauracewa muhallansu ba tare da sanin Ina ne za su je ba. Haba jama’a.”
Ya zuwa ranar 9 ga watan Augusta, 2026, wannan bidiyo ya samu wadanda suka kalla 12,000 da wadanda suka sake yada bidiyon 447 da masu tsokaci 433.
Tsokaci da ake yi kan wannan wallafa ta nuna yadda mutane ke nuna bacin rai a dangane da tabarbarewar tsaro a yankin Arewacin Najeriya inda wasu ke nuna gazawar shugabanni na addini da siyasa da gazawa wajen ba da kariya ga al’umma.
Maxwell M. Tanko yayi tsokaci da cewa “dakarun addini suna iya kashewa saboda addini amma sun gaza bawa kansu kariya. Za su ce ya sabawa addininsu.”
Wani mai amfani da shafin, Godfrey Agia, ya rubuta cewa
”Hausawa me kuke jira ne bayan da komai ya bayyana a fili? Me kuke jira da Fulani, ku dena siyar masu da komai a kasuwanni da hana masu hawa motar haya.”
Nasiru Abubakar yayi nasa tsokaci da cewa “Sannan gwamnonin Arewa basu damu ba, babu abin da suke magana sai Tinubu ya maimaita, Allah ya Isa.”
Wannan bidiyo dama hotunansa an yada shi a shafukan Facebook da dama kamar yadda za a iya gani a wadannan wurare nan da nan da nan da nan.
DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan wannan da’awa ganin yadda wannan bidiyo ya yadu sosai a shafin na Facebook inda suke da’awar cewa al’ummar Sokoto na gujewa muhallinsu saboda dalili na ‘yanbindiga.
Tantancewa
DUBAWA da ta gudanar da bincike kan asalin inda wannan bidiyo ya fito sai ta gano an wallafa shi a shafin Instagram na Northern Trend da shafin Facebook na Nasarawa Daily News. Dukkanin wadannan shafuka labarin iri daya ne: Al’umma a Sokoto na kauracewa muhallinsu saboda an kai farmaki a yankinsu.
Wannan bidiyo mai tsawon mintuna shida da dakika 29 an wallafa shi a shafin YMB Hausa TV a ranar 7 ga watan Agusta,2026.
DUBAWA ta kuma gano wannan rahoto a jaridun PUNCH da Vanguard da SaharaReporters da The Whistler da Daily Trust da PM News Nigeria dukkaninsu kan yadda al’umma a Sokoto suka kauracewa muhallinsu dalilin ayyukan ‘yanfashin daji. Wadannan rahotanni an wallafa su a ranakun 4 ga Agusta da 6 ga Agusta, 2026.
Rahoton da jaridar PUNCH tayi karin bayani kan wannan lamari inda tace wani tashin hankali inda wasu mazauna wani kauye suka yi kokarin tsallake wa tashin hankali bayan samun labarin cewa mahara na kokarin tunkaro inda suke zaune a garinsu.
A cewar rahoton wasu shedun gani da idanu sun bayyana cewa sun ga yadda wani jirgin kwale-kwale ya kife da fasinjoji 25, bakwai daga cikinsu an gano su, yayin da 18 ake ci gaba da lalubensu.
Wannan bayanin ya tabbatar da abin da ake fadi a dangane da wannan bidiyo cewa mutane na gujewa muhallinsu yayin da suke tsallaka kogi bayan da suka sami labarin cewa an kai hari a kusa da su.
Domin tabbatar da abin da ake fadi a bidiyon, DUBAWA ta tuntubi Muhammad Mu’azu wani danjarida da ke magana da harshen Hausa a gidan rediyo na Albarka Radio Bauchi.
Muhammad ya tabbatar da cewa harshen da yanayin maganar da ake iri daya ce da ta mutanen Sokoto da Kebbi da Zamfara. A irin fassara da yayi daya daga cikin mutanen da suke magana a bidiyon yace ya ji yana cewa:
“ Babangida, kana jina, kana ina ne? Ina nan amma ba zan iya ganinka ba, ka tsallake kogin yanzu? Ina neman mai kwale-kwale nima na tsallaka kogin.”
Fassarar ta nuna cewa mutanen da ke cikin bidiyon suna tattaunawa ne kan kokari na tsallaka kogin, zuwa daya bangaren kogin.
Abubuwan da DUBAWA ta gano sun yi daidai da abin da kafafan yada labarai suka nunar na cewa, mutane a gabashin Sokoto na kauracewa muhallinsu bayan farmaki na ‘yanta’adda.
A karshe
Da’awar gaskiya ce, rahotanni masu zaman kansu sun nunar a wannan lokaci cewa mazauna kauyen da ke gabashin Sokoto sun kauracewa muhallinsu bayan farmaki na ‘yanfashin daji.
