Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Ukraine ta na tura wa Najeriya hatsi
Sakamakon Bincike: Gaskiya. Kafafen yada labarai masu nagarta sun yi rahotannin cewa Ukraine, ta hanyar shirin Abinci na Duniya na Majalisar Dinkin Duniya wato WFP ta bai wa iyalai sama da miliyan daya hatsi, musamman wadanda rikicin yankin arewa maso gabashin Najeriya ya daidaita.
Cikakken bayani
A tsakiyar hauhawar farashin kayayyakin abinci a Najeriya, musamman saboda rage darajar takardun nera, wata taskar rubuce-rubuce na blog mai suna Instablog, ta wallafa cewa gwamnatin Najeriya ta shigar da hatsi zuwa kasar da ke yankin yammacin Afirka.
Labarin wanda daka wallafa a shafin Instagram, na cewa “Rashin tsaro a fuskar abinci: Rahotanni sun ce Ukraine ta tura wa Najeriya hatsi.”
Ya zuwa ranar Juma’a daya ga watan Maris 2024, an yi tsokaci 2,094 a kan labarin kuma mutane da dama sun yi ma’amala da shi.
Wasu daga cikin martanonin da aka yi sun nuna irin mamakin da mutane suka yi na kan cewa Ukraine wadda yaki ya daidata za ta iya turawa Najeriya hatsi wadda a na ta bangaren rashin shugabanci nagari ne ya addabe ta.
“Kasar da ke yaki ne ta ba mu abinci? A cewar Sirflow_15 cikin turankin burokun.
“Ukraine da yaki ya daidaita? Thefoodnetworking2 ya tambaya
Domin gano gaskiya, DUBAWA ta dauki nauyin tantance sahihancin wannan zargin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da binciken mahimman kalmomi inda ta yi karo da wani labari a shafin conducted Arise News ranar 29 ga watan Fabrairun 2024, wanda ke bayanin cewa tan 25,000 na alkama wanda ake bukata a matsayin agajin gaggawa wa iyalai miliyan 1.3 wadanda ke fama da rikicin yankin arewa maso gashin Najeriya ya iso kasar da Ukraine.
Rahoton ya bayyana cewa tallafin abincin WFP na Majalisar Dinkin Duniya ce ta dauki nauyin shi. Har ila yau, shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce shirin “hatsi daga Ukraine” ko kuma “Grain from Ukraine” na wakiltar gudunmawar Ukraine ga ayyukan jinkai a duniya. WFP zai kasance alfani ga Najeriya, inda farashin kayayyakin abincin yau da kullun suka yi tashin gwauron zabi, ya kuma zama abun da wasu ba su iya tabawa.
Jaridun Vanguard, Daily Trust, da Leadership am duk sun dauki labarin.
DUBAWA ta kuma tuntubi ma’aikatar noma ta kasa ta manhakar sakonni ta WhatsApp, sai dai ba ta sami amsa ba.
A karshe
Wannan da’awar gaskiya ce. Kafofin yada labarai masu nagarta duk sun dauki labarin.