Asalin hoton: The Whistler
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook @Yusuf Maishanu Mayanchi, ya wallafa wani hoton gawawwaki ya na da’awar wai ‘yan bindiga sun hallaka mutane 52 cikin sa’o’i 48 a jihar Sokoto.

Hukunci: Yaudara ce! Hoton ya nun matafiyar da aka kona yayain da suke kan hanyar zuwa karamar hukumar Faskari a jihar Katsina ba wai wasu mutanen da akahallaka a Sokoto ba.
Cikakken bayani
Wani mai amfani da shafin Facebook, Yusuf Maishanu Mayanchi, ya wallafa hotunan gawawwakin wasu mutanen da aka sakaya da ganyayyaki yayin da jama’a masu jaje suka kewaye su. Hoton da ya wallafa ranar shida ga watan Yunin 2026 na da’awar cewa cikin kasa dasa’o’i 48 ‘yan ta’adda sun kashe mutane 52 a jihar Sokoto.
Labarin (wanda aka wallafa a nan) an yi masa take a hausa kamar haka, “Aƙasa da awanni 48 Fulani yan ta adda sun kashe mutane 52 a sabon birni jahar Sokoto. Wa’yannan sune mutanen dasuke cewa suda hausawa sun zama ɗaya MAISHANU.”
Wannan da’awar dai daga 7 ga watan Yuni, mutane sama da134 sun yi ma’amala da shi, ya sami tsokaci 17 an kuma sake rabawada sauran shafuka sau takwas. A karkashin wannan labarun masu tsokacin sun mayar da martani da add’uo’i tare da bayyana mamakin da lamarin ya ba su
Wani mai amfani da shafin Rabi’u Uzo cewa ya yi “Bari Ubangiji ya jikansu da rahama ya kuma sama mu su adalci.”
“Mu na Allah ne kuma a gare shi za mu koma. Allah ya gafarta mu su ,” in ji Shamsu Bn Musa Kawaye.
Wani mai amfani da shafin shi ma Idris Aliyu cewa yayi, “Allah ya kawo karshen Fulani ‘yan ta’adda, masu ta’addancin jini a kasar Hausa.”
Ganin yadda wannan batun ke tattare da sarkakiyya da kuma yadda tsokace-tsokacen da aka yi ke nuna cewa wasu sun yarda da labarin ne ya sa DUBAWA tantance gaskiyar lamarin.
Tantancewa
Mun fara da tantance hoton kuma binciken ya kai mu ga labarin da aka fara wallafawa da hoton wanda rahoto ne na sadda aka kona wasu matafiya har lahira yayin da su ke kan hanyarsu ta zuwa jihar Katsina.
Ranar 23 ga watan Disamban 2021, shafin thesteeetjournal.org ya rawaito cewa ‘yan bindiga sun kona wasu matafiya da ransu cikin wata motar da ke kan hanyarta ta zuwa Katsina tare da wannan hoton.
Haka nan ita ma jaridar, Gist Mania, ranar23 ga watan Disamba, a shekarar 2021, ta yi rahoto tare da hoton da wannan labarin dai na matifar da ‘yan bindiga suka kona a karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina.
DUBAWA ta kuma sake gudanar da binciken mahimman kalmomi dangane da batun inda ta gano wani rahoton da aka wallafa a shafin HumAngle, wanda ya nuna cewa hoton ya mi fi haka dadewa tunda a wannan shafin an wallafa shi ne ranar 15 ga watan Yunin 2021.
“Mutane shida a ciki har da wasu ‘yan sanda da ma’aikatan ofishin NSCDC biyu sun hallaka ranar litinin 14 ga watan Yunin 2021 bayan wani harin ta’addancin da aka kai kamfanin PGP a Birnin Tudu da ke karamar hukumar Bakura a jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya,” gabatarwar labarin ya bayyana.
Mun kuma sake binciken mahimman kalmomi inda a wannan karon muka sa “‘yan bindiga sun hallaka mutane 53 a Sokoyo” dan mu ga ko akwai wani labarin da ke alaka da hakan amma ba mu ga komai ba
A karshe
Da’awar wai ‘yan bindiga sun hallaka mutane 53 a Sokoto yaudara ce kawai. Hoton da aka yi amfani da shi tsoho ne tun shekarar 2021 aka yi amfani da shi wajen wani labarin harin da aka kai kan wasu matafiya a Katsina.
Cibiyar samar da sabbin dabaru da ci-gaban aikin jarida (CJID) ke aiwatar da wannan shirin na horas da ‘yan jarida tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.
