African LanguagesHausa

Hotunan da aka wallafa a Facebook da zargin wai wata makaranta ce a jihar Anambra ba gaskiya ba ne

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: An yi amfani da wasu hotuna biyar ana zargin cewa makarantar sakandare ta maza a Uga jihar Anambra ne.

Hotunan da aka wallafa a Facebook da zargin wai wata makaranta ce a jihar Anambra ba gaskiya ba ne

Sakamakon bincike: An dauko hotunan ne daga wurare daban-daban dan bayar da labarin karya da kuma yaudarar jama’a.

Full Text

The-Cyberprof Int’l, wani mai rubuce-rubuce a shafin Facebook ya wallafa wasu hotuna guda biyar wadanda ke nuna lalacewar abubuwan more rayuwar da ke wata makarantar sakandare ta maza a Uga jihar Anambra. Wannan labarin, wanda ya sami alamar like guda 129, ya kuma janyo ra’ayoyi mabanbanta daga masu amfani da shafin.

Alal misali, masu tsokaci irinsu Olarewaju Oluwadamilare sun bayyana shakku dangane da sahihancin labarin. “Wannan ba zai iya kasancewa Anambran da ake yawan kuri a kai ba,” ya bayyana.

Garin amincewa da labarin da ma sanya alamar tambaya kan alkiblar gwamnati dangane da ilimi, wani mutumin mai suna , Ogbiko Omozuhiomwen, ya rubuta cewa: “Ya kamata a ce ilimi ya kasance da mahimmancin gaske ga shugabanninmu.”

Makarantar sakandare ta maza ta Uga Boys makaranta ce da manyan mutanen wannan yankin su ka je. Sun hada har da gwamnan jihar Anambran mai ci yanzu,  Charles Soludo da Peter Obi, tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar AP. Dangantakar wannan makarantar da attajiran jihar ne ma ya kara haifar da cece-kuce na siyasa tsakanin masu amfani da shafin na Facebook.

A dalilin haka ne DUBAWA ta dauke nauyin tantance gaskiyar hotunan dan gano abun da ke faruwa.

Tantancewa

Mun bi hotunan dalla-dalla dan rage rudani

Hoto na daya 1

Hotunan da aka wallafa a Facebook da zargin wai wata makaranta ce a jihar Anambra ba gaskiya ba ne

Hoton farko a cikin hotuna biyar din da aka sa ya nuna wasu dalibai suna rubutu cikin wani ajin da ko filasta babu a bangon kuma babu wani rufi a kasa. Yayin da aka ga yawancinsu a zaune a kan benci, wasu biyu sun yi amfani da taya ne suka zauna dan yin gwajin da aka ba su a ajin.

Da muka duba hoton da kyau, sai muka ga akwai mace a cikin daliban saboda kitson da ke kanta. Wannan ne ya sa muka sanya alamar tambaya domin Uga Boys makarantar maza ne kadai, dan haka kasancewar mace a wurin zai yi wuya.

Daga nan sai muka yi amfani da manhajar tantance hotuna ta google wadda ta kai mu zuwa wani labarin da aka wallafa a jaridu biyu, wadanda suka hada da  Premium Times da Dailypost  ranar 6 ga watan Disemba. An dauko hoton ne a makarantar sakandaren Ajuwon da ke Akute a jihar Ogun lokacin jarabawar dalibai. Hoton na nuna yadda bai kamata dalibai su rika karbar darasi a Najeriya a “karni na 21” ba, kuma wani mutumi mai suna Deji Kolawole ne ya dauki hoton.

Tun wancan lokacin an yi amfani da hoton a shafuka da dama dan labarai daban da daban, kamar yadda za ku iya gani a nan da nan.

Hotuna na biyu da na uku

Hotunan da aka wallafa a Facebook da zargin wai wata makaranta ce a jihar Anambra ba gaskiya ba ne

Kamar dai hoton farko, su ma hotunan na biyu da na uku dalibai ne ke zaune azuzuwansu. Haka nan kuma suna zaune ne a kasa kowanne cikin rigar makaranta, yayin da akwai kujeru cikin ajin baki daya bai ma yi kama da wurin da ya kamata a ce za’a yi koyarwa ba. Kujeru da teburan ba yawa yawancinsu kuma suk sun karye. Sai dai kuma babbar tambayar da ta danganci bincikenmu ita ce: Yaya za’a yi a ce daliban da ke da shekaru tsakanin hudu da biyar su kasance a makarantar sakandare kamar yadda wadanda suka wallafa labarin suke so mu yarda?

Har ila yau, DUBAWA ta sake yin wani binciken cikin manhajar google dan tantance sahihancin hoton inda shi ma ta gano cewa hoton na cikin yanar gizo tun shekarar 2012. Mun ma gano wani labarin  da jaridarv Sahara Reporters ta rubuta mai taken “Photonews: Makarantar firamarin da ta fi kowanne lalacewa a jihar Ogun.” Hoton ya gwado dalibai makarantar firamaren karamar hukumar Obafemi Owode da ke jihar Ogun. Wanda ya dauki hoton dan jarida ne mai suna Steve Aborisade.

Domin tabbatar da wannan labarin, mun tuntubi shafin Mr Aborisade a Facebook, inda muka ga ainihin hotunan da ya dauka. Da kansa ya ziyarci makarantar ya dauki hotunan, wadanda mai shafin The-Cyberprof Int’l ya dauki biyu daga wajen ya yi amfani da su.

Hoto na hudu

Hotunan da aka wallafa a Facebook da zargin wai wata makaranta ce a jihar Anambra ba gaskiya ba ne

Hoto na hudun kuma sunan makarantar ne wanda kungiyar tsoffin dalibai reshen PH suka sanya. Shi ma wannan hoton mun gano wani hoton da rubutu iri daya amma wata kungiya mai suna Tracka, ce ta dauka, kungiyar da ta shahara wajen snaya ido a kan shirye-shiryen gwamnati.

Hotunan da aka wallafa a Facebook da zargin wai wata makaranta ce a jihar Anambra ba gaskiya ba ne

Da muka sa hotunan kusa da juna sai muka ga cewa a wuri daya aka dauki hoton. Na farko dai karfen da aka yi zanen a kai iri data ne. Bacin haka akwai wayoyin lantarki a daga samansu su biyu. Wannan ne ya tabbatar mana cewa an yi sabon fenti ne a hoto daya, dayan kuma yadda ya ke kenan kafin fentin. Haka nan kuma The-Cyberprof ya yi amfani da tsohon fentin ne.

Hoto na biyar

Hotunan da aka wallafa a Facebook da zargin wai wata makaranta ce a jihar Anambra ba gaskiya ba ne

Wannan hoton na karshe an yi amfani da shi ya fi a irga, saboda ma har ya fara kodewa. Shi ya sa ma muka gaza gano ainihin inda aka fara amfani da shi.

A Karshe

Yawancin hotunan da aka yi amfani da su a sunan makarantar sakanadaren maza ta Uga Boys an tattaro su ne daga kafofi daban-daban. Dan haka wannan zargin karya ne kawai.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »