African LanguagesHausa

Hotunan da ke nuna babban titin Legas zuwa Calabar da ake ginawa yawanci gaskiya ne

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa wasu hotunan da ya ce aikin da ake yi ke nan a sabon shirin da aka kaddamar na gina babban titin da zai hada Legas da Calabar.

Hotunan da ke nuna babban titin Legas zuwa Calabar da ake ginawa yawanci gaskiya ne

Hukunci: DUBAWA ta bi diddigin hotunan ta gano cewa daya daga cikinsu titi ne a Amurka yayun da sauran kuma ainihin hotunan aikin da ake yi ne a wurin. Dan haka akwai gaskiya a da’awar.

Cikakken bayani

Shekaru da dama bayan da aka amince da shirin, gwamnatin tarayyar Najeriya kwanan nan takaddamar  da ginin sashen farko na babban titin Legas – Calabar mai tsawon kilometa 700. Titin wanda aka dauko daga titin Ahmadu Bello Way a cikin birnin Legas, ana sa ran zai ci kimanin Nera triliyan 15 wato kimanin Nera biliyan 4 ke nan kan kowace kilometa kuma zai bi ta yankuna tara wadanda ke kusa da gabar ruwa wadanda suka hada da Lekki Deep Seaport (Tashar ruwan Lekki), da jihohin Ogun, Ondo, Delta, Bayelsa, Ribas, da Akwa Ibom.

Kwanaki kadan bayan an kaddamar da shirin, Olusegun Adeniyi, wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa hotuna guda uku inda ya ke bayyana matakin da aka kai wajen gina babban titin. “Wannan ne babban titin Legas -Calabar mai tsawon kilometa 700, a Najeriya,” wani bangaren rubutun na sa ya bayyana.

“Babban titi ne wanda ke da layi biyar a kowane bangare a tsakaninsu a wasu wuraren kuma akwai titin jirgin kasa. Ana yin shi ne da fasahar da ke amfani da siminti, da karafa kuma dan su karfafa abun ba ha’inci. Da zarar aka kammala, zai shafe akalla shekaru 40 ba tare da wata matsala ba. Najeriya na gina ababen more rayuwa dan habbaka tattalin arziki. Ku zuba jari a Najeriya.”

Wannan bayanin na Adeniyi ya sami alamar amincewa na Like guda 377 da tsokaci 116. Yayin da yawa suka yaba wa gwamnatin tarayyar , wata mai suna Success Emhabino ita ma mai amfani da shafin Facebook ba sanya alamar tambaya kadai ta yi kan sahihancin wadannan hotunan ba, ta ma bayyana shakkunta dangane da kasancewar shiri irin wannan ma baki daya.

A cewarta, “Akwai wani da ke zama kusa da wurin da zai iya tantance ko akwai wannan shirin ma. Ban yarda da gwamnatin Najeriya ba.

Ganin cewa akwai yiwuwar samun hotunan bogi daga cikin hotunan ko ma bayanai masu yaudara, shi ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tantance batun.

Tantancewa

Mun sanya hotunan cikin rukunnai dan fayyacewa kamar haka:

Hoton farko (1)

Hotunan da ke nuna babban titin Legas zuwa Calabar da ake ginawa yawanci gaskiya ne

Hoton farko ya nuna hanya ce wacce aka riga aka kammala har ma an fara amfani da ita, kuma tana da layuka biyar a kowani bangare da kuma layin jirgin kasa a tsakiya. Da muka sake kallon hoton da kyau sai muka sami damuwa. Na farko dai titin Legas Calabar bai dade da aka fara ba, dan haka ba za’a iya cewa an yi an gama har ma an fara amfani da shi ba. Haka nan kuma, ministan ayyuka na kasa, David Umahi ya riga ya fayyace cewa ko da shi ke akwai tanadin gina layin jirgin kasa, ba’a riga an fara ba.

Da muka yi amfani da manhajar tantance hotuna ya kai mu ga wata mujallar Amurka mai kwanan watan daya ga watan Nuwamban 2022. Bisa bayanan da aka yi cikin mujallar, hoton na wani layin jirgi ne da ke Ashburn a birnin Virginia na kasar Amurka.. 

Hotuna na 2 da na 3

Hotunan da ke nuna babban titin Legas zuwa Calabar da ake ginawa yawanci gaskiya ne
Hotunan da ke nuna babban titin Legas zuwa Calabar da ake ginawa yawanci gaskiya ne

Hotuna na biyu da na uku sun nuna yadda ake gina titi a wani wuri wanda ba’a bayyana ba. Ana iya ganin ma’aikatan suna amfami da abun sa siminti na SP 94 wanda ake amfani da shi wajen shafe saman titi.

Mun binciki hotunan da ke shafin Facebook na ministan ayyuka Mr Umahi dan tantance su. Ranar 29 ga watan Maris 2024, ya wallafa hotuna hudu na wurin da ake gina titunan, a ciki har da hoto na biyu. Sai dai bai bayyana ko ina ba ne, iyakaci dai ya ce “Ku yi imani da tsarin da ake bi kawai.”

Haka nan kuma, mun gano wani bidiyon da wasu masu dora shirye-shirye a YouTube suka sa inda suka wurin da ake gina titunan da kansu suka gudanar da bincike kan halin da ake ciki tare da Mr Umahi ranar tara ga watan Afrilun 2024. A cikin bidiyon mun ga hotunan da suka dace da hotunan da ke kan shafin Adeniyi.

Hotunan da ke nuna babban titin Legas zuwa Calabar da ake ginawa yawanci gaskiya ne

Mun hango wannan benen a cikin bidiyon.

Hotunan da ke nuna babban titin Legas zuwa Calabar da ake ginawa yawanci gaskiya ne

Ga kuma benen a cikin bidiyon

A Karshe

Yayin da hoton farko ya fito daga wani shirin a Amurka, bincikenmu ya nuna mana cewa hotuna na biyu da na uku hotuna ne da aka dauko daga daidai inda ake gina titin na Legas – Calabar. Wannan ne ma ya sa da’awar ya kasance cewa akwai gaskiya a yawancin abubuwan da aka bayyana.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »