Sojojin Amurka da Najeriya. Asalin hoto: US Army.
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani bidiyo da ya bazu ya yi ikirarin cewa sojojin Amurka da Sojojin Najeriya sun ceto mutanen da aka sace a wani farmaki na haɗin gwiwa a Jihar Zamfara.

Hukunci: Ƙarya. Bidiyon na ƙirƙirar AI ne. Babu wata shaida da ke nuna cewa sojojin Amurka sun shiga wani aikin ceto na haɗin guiwa a Zamfara.
Cikakken bayani
A yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar Najeriya, musamman a yankin Arewa maso Yamma, wani bidiyo da ya bazu (an adana shi a nan), da ke yawo a Facebook, ya nuna cewa sojojin Amurka da na Najeriya sun ƙaddamar da wani farmaki na haɗin gwiwa don ceto mutanen da aka sace a Jihar Zamfara.
Da’awar ta bayyana ne bayan hukumomin Najeriya sun sanar da cewa Sojojin Amurka za su tallafa wa Najeriya wajen magance matsalar tsaro.
Bidiyon mai tsawon daƙiƙa goma ya nuna wani soja na Amurka yana sanar da cewa dakarun Amurka da na Najeriya sun ceto mutanen da aka sace a wani “aikin haɗin gwiwa da aka tsara” a Zamfara.
Zuwa ranar Litinin, 23 ga Fabrairu, 2026, bidiyon ya samu sama da kallo 665,000, fiye da martani 10,000, sharhi 958, an kuma raba sau 501.
Ra’ayoyin masu amfani da shafukan sada zumunta sun kasu gida biyu, inda wasu suka nuna shakku kan sahihancin bidiyon.
Wani mai suna Ezea Gozie, ya rubuta: “Bidiyon ya yi gajarta sosai ace na gaske ne. Ina zargin AI ne ya ƙirƙira shi.”
Sai dai wani mai amfani, David Chigozie, ya nuna goyon baya, yana cewa: “Allah ya albarkaci sojojin Amurka kuma ya albarkaci Donald J. Trump.”
Saboda muhimmancin wannan batun, DUBAWA ta yanke shawarar bincikar sahihancin bidiyon da da’awar.
Another user, David Chigozie, however, responded positively, saying “God bless the U.S. military and bless Donald J. Trump.”
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da nazari ta hanyar duba hotunan bidiyon. Mutanen da ake ikirarin an ceto da ke a bayan fage, suna zaune kawai ba tare da wani motsi ba, abin da ya nuna rashin daidaito.

Hoton bidiyo da aka zaƙulo.
Bugu da ƙari, DUBAWA ta yi amfani da manhajar binciken fasahar AI. wato Hive AI ya nuna cewa bidiyon kashi 100% na ƙirƙirar AI ne.

Hoton sakamakon Hive.
Wani manhajar mai suna Truthscan, ta nuna yiwuwar kashi 42% cewa bidiyon ƙirƙirar AI ne.

Hoton sakamakon Truthscan.
DUBAWA searched official communication channels, including the Nigerian Defence Headquarters, the Nigerian Army’s verified social media accounts, the US Department of Defence’s Africa Command (AFRICOM) press releases, and other credible media outlets, but found nothing related to the claim.
No official statement, press release, or credible report confirmed the operation.
DUBAWA ta bincika shafukan sadarwa na hukuma, ciki har da Hedikwatar Tsaron Najeriya, shafukan sada zumunta na Sojojin Najeriya, shafin rundunar AFRICOM ta Ma’aikatar Tsaron Amurka dake Afrika, da kafafen yaɗa labarai masu inganci, amma ba ta samu wata shaida da ke tabbatar da da’awar ba.
Babu wata sanarwa ta hukuma ko rahoto mai inganci da ya tabbatar da bidiyon.
Haka kuma, Hedikwatar Tsaron Najeriya ta jaddada a bainar jama’a cewa jami’an sojan Amurka a Najeriya ba za su shiga a yi yaƙi da su ba.
“Jami’an sojin Amurka ƙwararrun ne da ke aiki a matsayin masu ba da shawara da horo,” in ji Daraktan Yaɗa Bayanai na Tsaro, Samaila Uba.
A Ƙarshe
Binciken DUBAWA ya nuna cewa bidiyon na ƙirƙirar AI ne. Saboda haka, da’awar ƙarya ce.
