Nnamdi Kanu . Hoto: DUBAWA
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X yayi da’awar cewa kasancewar Nnamdi Kanu na da takardar zama a Amurka wannan ya bashi damar Amurka ta tsoma baki kan batun tsare shi da aka yi a Najeriya.

Hukunci: Karya ce. Cewa kai dankasar ne a takarda ne kawai, baya ba da dama ta samun kariyar shari’a ko kariyar diflomasiya ko tsayawa don kare hakki karkashin dokar ta Amurka ko ta Najeriya.
Cikakken Labarin
Nnamdi Kanu dan Najeriya ne kuma dan Burtaniya kuma jagoran ganin an kafa kasar Biafra karkashin kungiyarsa ta (IPOB).
A ranar 20 ga watan Nuwamba, 2025 Mai Shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yanke hukuncin daurin rai da rai ga Kanu bayan samunsa da laifuka da dama da suke da alaka da ayyukan ta’addanci. Kawo yanzu yana ci gaba da zama a gidan gyaran hali da ke Sokoto.
A ranar 23 ga watan Janairu,2026 an ba da lambar shedar zama dankasa ta girmamawa ga Kanu a jihar Georgia da ke Amurka.
Bayanan da aka rubuta da ya samu rattaba hannun sakaren gwamnatin jihar ta Georgia Brad Raffensperger ya bayyana shi da samun “takardar zama dan kasa ta girmamawa” da kuma zama jakada na kwarai na jihar.
An ba da wannan takarda ne dai a yayin wani biki a Milledgeville, Georgia, kuma tsohuwar babbar jami’ar Najeriya a ofishin jakadancin Najeriya a Afurka ta Kudu Ambasada Uche Ajulu-Okeke ce ta karbi wannan takarda amadadin Kanu.
Ga ma wani bangare na abin da aka rubuta ke cewa. “ Ni Brad Raffensperger, sakataren gwamnatin jihar Georgia na bayyana a hukumance Nnamdi Okwu Kanu ya samu shedar zama dan kasa ta girmamawa …. Da fatan wannan girmamawa za ta ba shi damar samun mutuntawa da zama jakada na kwarai…”
Bayan fitar da wannan sanarwa wasu masu amfani da shafin X a ranar 25 ga Janairu,2026 sun rika fitar da tasu fahimta kala-kala inda wasu ke cewa wannan bashi takardar girmamawa za ta sanya Kanu ya samu wata kariya a dangane da tsarewar da ake masa a Najeriya.
Mai amfani da shafin na X @engrICO2015 ya rubuta cewa , “ Matsalar da hakan zai haifar ita ce Najeriya na tsare da dan kasar Amurka bisa kuskure, hakan kuma zai sa Amurka ta tura da tarin tambayoyi kan batun tsare shi da aka yi …kun ga wannan matsala….hmmmm.”
Ga wani ma mai amfani da shafin @iw42445, da abin da yake cewa “Idan Amurkawa za su je su dauko Nicolas Maduro, wacece kuma Najeriya me za ta iya yi idan an zo daukar Kanu. ”
Shi kuwa @kenny-kenzeen cewa yayi “Gwamnatin Amurka na kallon Najeriya… Kisan shi na nufin kisan dan Amurka, wannan kuma babbar matsala ce.”
Ganin cewa irin wannan da’awa na iya jawo rashin fahimta ta diflomasiya tsakanin Najeriya da Amurka DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike don gano ita wannan takardar shedar zama dan kasa ta girmamawa yaya take, shin ana iya amfani da ita wajen katsalandan kan harkokin shari’a a wata kasa.
Tantancewa
Me ake nufi da takardar shedar zama dankasa ta girmamawa?
Shedar zama dan kasa ta girmamawa alama ce da ake bawa mutane saboda abubuwa da suka cimma ko gudunmawar da suka bayar.
Kasashe da dama na ba da takardar girmamawa ta zama dankasa ta fuskoki da dama yayin da kasashe irinsu Amurka da Kanada da Girka da Ireland da Jamus suna da hanyar ba da takardar a hukumance dama wacce kawai ta biki ce wasu kasashen kamar Najeriya a tsari na shari’a ko kundin tsarin kasar ba haka lamarin yake ba.
A Amurka ba da shedar zama dan kasa don girmamawa ba kasafai ake yi ba kuma akasari na biki ne kawai da ake warewa ga mutanen da ba asalin ‘yanAmurka ba wadanda suka yi wani abun bajinta ko aikin sadaukarwa ko yin tasiri a duniya.
Makasudin ba da ita shine girmamawa da mutuntawa don nuna ganin abin a yaba da wani yayi don taimakon al’umma ko a mataki na kasa da kasa.
Irin wannan tsari ya saba da tsarin shige da fice na Amurka ko dokar zama dankasa ta Amurka, ana bayyanata ne da girmamawa ta musamman. ba kasafai ake ba da ita ba, ana ba da ta ne ta hanyar ‘yanmajalisa ko masu zartarwa.
Ga misali kamar yadda aka shar’anta a dokar ‘yanmajalisa wanda kuma ta yiwu shugaban kasa ya mara baya, duk da haka babu wani hakki na shari’a ko hakki ko wani nauyi na kasancewa dan Amurka a tattare da ita.
A tarihance wasu mutane ne kadan aka taba basu irin wannan takardar shedar zama dankasa ta girmamawa kamar su Winston Churchill da Mother Teresa da Nelson Mandela abin da zai nuna karancin irin wadanda ake bawa. alama ce ta girma ba wai maganar shari’a ake ba ko wani abu da ya shafi hakki na dankasa.
Shin ba da takardar zama dankasa ta girmamawa na sawa mutum ya zama hakikanin dankasar Amurka?
Shedar zama dankasa ta girmamawa ba yana nufin hakikanin dan kasa ba ne a Amurka, karkashin doka ta Amurka ana samun takardar zama dankasa ne kawai idan an bi wasu matakai na doka.
Wannan ya hadar da haifar mutum a kasar ta Amurka ko iyayensa ‘yan Amurka ne ko kuma ya sauya daga wata kasa zuwa ta Amurka bayan cika sharudan zaman kamar nuna kyawawan halaye da mika wuya ga kundin tsarin mulkin Amurka.
Sashen tsaro na Amurka ya bayyana karara cewa ba da takardar shedar zama dankasa ta girmamawa baya nufin batu na hakki da wasu damarmaki ko wasu abubuwa da ke tattare da cikakken hakki na dankasa.
Wannan baya ba da dama ga mutum yayi zabe ko ya zauna a kasar a matsayin dankasa ko ya samu fasgo na dan Amurka ko katin dankasa ko samun wasu damarmaki daga hukumar shige da fice ga wanda aka bawa ko iyalansa.
Haka kuma ba ta dorawa mutum wasu hakkoki kamar sadaukarwa ko wasu hakkoki da mai cikakkiyar takardar shedar dankasa ke da su.
Domin kara samun fahimta a dangane da wannan batu DUBAWA ta yi tattaunawa da Francis Ochie, kwararren masanin doka kuma mai ba da shawara a jami’ar Veritas University.
A cewarsa “takardar girmamawar kawai ana ba da ita ne dalilin yin wani abu na bajinta kuma ‘yanmajalisa ke bayarwa don girmama wasu daidaikun mutane saboda tasirunsu a duniya ko ayyuka da suka yi wa al’umma. Ba ta da tasiri kan batun da ya shafi doka na dan kasa ko abin da ya shafi shige da ficensa.”
Ya kara da cewa wannan matsayi baa iya mika shi ga wani ko doka ta yi aiki a kansa kuma da zarar mutum ya mutu shike nan ta gama tasirinta.
DUBAWA ta kuma tattaunada da Divine favour Osomujie-Paul, wata masaniyar shari’a ta kamfanin Ndoma-Egba, Ebri & Co.
Tace ya kamata a fahimci cewa ba da takardar shedar zama dankasa ta girmamawa abu ne kawai da ake bayarwa na biki ba wai hakki ne da ya shafi shari’a ba.
“Girmamawa ce, ba hakki na matsayi ba ne,” ta kara da cewa.
Divine ta kuma kara da cewa wanda aka ba wa wannan karramawa zai ci gaba da zama dankasarsa ta asali, za a bincike shi a wajen jami’an shige da fice na Amurka kamar kowane dankasar waje.
Shin Amurka za ta iya sa baki kan shari’ar ta Kanu don ya samu wannan takarda?
Samun irin wannan takardar dan kasa don girmamawa ba ta ba da dama ta shari’a ta yadda Amurka za ta shiga lamuran wani da ke zaune a kasar da ba Amurka ba.
Saboda ba ta da hurumi kan hakkin wani mutum ko damarmaki da yake da su kamar abin da ya shafi takardun tafiye-tafiye da wasu hakoki da yake mora wadanda suka shafi shige da ficen, ko ba da kariyar ofishin jakadanci, ba ta dorawa Amurka duk wani hakki da ya shafi shari’a.
Abu mai sauki da za a fahimta shine don Amurka ta baka takardar zama dankasa ta girmamawa wannan baya ba da kariyar diflomasiya ko wani abu na kariya daga bangaren shari’a. Ana iya cewa abu be na jeka na yika da Amurka kan kalla ta yi abin da ya dace.
Da ya kalli abin ta fuskar Najeriya Francis yace dokar Najeriya ba ruwanta da bawa wani irin wannan takardar shedar zama dankasa ta girmamawa ta kowace fuska kuwa.
Yace “Karkashin kundin tsarin mulkin Najeriya ana samun takardar zama dankasa ne ta fuskar haihuwar mutum ko ta hanyar auratayya ko kuma mutum ya cika wasu ka’idoji ya sauya kasa, babu wani abu wai shi takardar zama dankasa ta girmamawa.”
Yace akwai wasu kasashen Yamma da a wasu lokutan su kan ba da irin wannan takarda ta girmamawa ga daidaikun mutane saboda yadda suka yi wata bajinta a mataki na duniya ko a fanni na kare hakkin dan Adam da bautawa al’umma, wannan baya nufin kuma abu ne da ya shafi hakkin shari’a kuma na wata kasa.
“Abu ne kawai na girma da bashi da tasiri a fannin shari’a,” a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa ba za a yi amfani da takardar shedar zama dankasa don girmamawa ba don cusa baki a harkoki na diflomasiya.
”Idan Amurka ta ba wa mutum irin wannan takardar girmamawa ga dan Najeriya kuma wannan dan Najeriya na fuskantar shari’a a wata kotu ta Najeriya to babu abin da gwamnatin Amurka za ta yi akan wannan. Ba magana ce ta hakikanin dankasarta ba, a takarda ne kawai babu hakkin da ya shafi shari’a a tattare da ita, a cewar Francis.
Haka kuma Divinefavour ta fadawa DUBAWA cewa wannan takardar girmamawa ba ta da tasiri a fannin shari’a.
Tace “abu ne da ya tsaya a iya bikin kawai ba babu batu na ba da kariya daga kasar da ta bawa mutum kuma mutum ba zai iya samun tsoma baki na diflomasiya ba daga ofishin jakadancin wannan kasar.”
Kai tsaye ba da takardar shedar zama dankasa ta girmamawa ba dama ba ce da ke da alaka da shari’a ko tsoma baki.
Duk da irin wannan takardar girmamawa da ake bawa wasu mutane idan maganar shari’a ta tashi ana duba kasarsu ce ta asali wane tanadi ta yi a kai.
A Karshe
Batun da’awar cewa Nnamdi Kanu ya samu takardar shedar zama dan Amurka ta girmamawa. wannan ba zai ba wa Amurka dama ba ta shiga hurumin shari’a ko tsoma baki kan tsare shi da aka yi a Najeriya, don haka da’awar karya ce.
Takardar da aka bashi ta girmamawa a nan ta tsaya, babu wani tasirin doka a kanta, ba wai an bashi hakikanin takardar zama dankasa ba ne ko wata dama da Amurka za ta shiga ta yi kutse kan harkokin da suka shafi shari’a a Najeriya ba.
