Shugaban ‘yan bindiga. Mallakar Hoto: YouTube/BBC Africa Eye
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da X ya yi iƙirarin cewa ‘yan ta’adda sun tabbatar sun karɓi Naira miliyan 60 daga gwamnatin Najeriya, duk da cewa gwamnatin ta musanta biyan fansa.

Hukunci: Yaudara ce. Binciken DUBAWA ya gano cewa wannan iƙirari ya karkata ne kan wani tsohon bidiyo daga shirin BBC na shekarar 2022.
Cikakken Bayani
Wani iƙirari da ke yawo a shafin X da Facebook (an adana shi a nan) na cewa ‘yan ta’adda sun tabbatar da karɓar Naira miliyan 60 daga gwamnatin Najeriya, lamarin da ya saba da ikirarin Gwamnatin Tarayya cewa ba ta taɓa biyan fansa ga Boko Haram ko wasu kungiyoyin masu dauke da makamai ba.
Wannan zargi ya samu karɓuwa bayan wani shahararren mai amfani da X, OurFaveOnlineDoc (@OurFavOnlineDoc), ya mayar da martani kan wani rahoto inda Gwamnatin Tarayya ta musanta biyan fansa domin a saki waɗanda aka sace.
“Gwamnati ta biya mu Naira miliyan 60 domin mu saki ‘yan matan; mun yi amfani da kuɗin muka sayi bindigogi,” mai amfani da X ya ambato wani ɗan ta’adda na cewa.
Ana ganin cewa wannan zargi ya biyo bayan wani binciken kamfanin dillancin labarai na AFP wanda ya yi iƙirarin cewa an biya biliyoyin naira a matsayin fansa domin a saki yara har 230 da ma’aikata da aka sace daga wata makarantar Katolika a Jihar Neja.
Yayin da muhawarar ta ƙara ƙamari, an wallafa irin wannan iƙirari a Facebook (nan da nan), inda wasu shafukan yanar gizo da jaridu suka ƙara yaɗa zargin.
Zuwa ranar Juma’a, 27 ga Fabrairu, 2026, sakon ya samu sake wallafawa 5,417, tsokaci 214, da kuma alamar so 9,815.
Wannan ya sa wani mai amfani da X, Nwoji AlgoTrader (@H2Wealth365), ya yi sharhi cewa, “Yayin da kafafen yada labarai ke cewa an biya biliyoyin naira ga ‘yan ta’adda, ainihin masu garkuwar sun ce an biya su Naira miliyan 60.”
Wani kuma, Onyekachukwu Aduaka (@AduakaO1999), ya jaddada wannan ra’ayi, yana cewa gwamnati na “tallafa musu ta kaikaice.”
Saboda muhimmancin wannan zargi, DUBAWA ta gudanar da bincike.
Tantancewa
DUBAWA ta yi amfani da shafin binciken hoto na Google Reverse Image Search ta hanyar cire wasu hotuna daga bidiyon da ke yawo a X.
Binciken ya nuna cewa bidiyon ya samo asali ne daga wani shirin bincike na kafar yaɗa labarai ta ƙasar Burtaniya, BBC Africa Eye mai taken “The Bandit Warlords of Zamfara.”
An fitar da shirin a hukumance ranar 25 ga Yuli, 2022, inda ya yi zurfin bincike kan matsalar ‘yan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya. Shirin ya kunshi tattaunawa da shugabannin ‘yan bindiga, masu shiga tsakani, wadanda abin ya shafa, da jami’an gwamnati na yankin.
DUBAWA ta gano ainihin sashen bidiyon da ake yaɗawa. Ana iya samun gajeren bidiyon a minti 38 da sakan 5 cikin shirin mai tsawon mintuna 50.
A cikin bidiyon, an nuna wani mutum sanye da riga shuɗi tare da rufe fuska, yana magana kan kuɗin fansa da harkar satar mutane.
Binciken karin kalmomi da nazarin shirin ya nuna cewa Naira miliyan 60 da aka ambata a bidiyon na da alaka da sace ‘yan makarantar sakandaren gwamnati ta mata ta Jangebe a Jihar Zamfara a shekarar 2021, lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A cikin shirin na BBC, dan bindigar da aka rufe fuskarsa ya yi bayani kan yarjejeniyar biyan fansa, inda ya ambaci Naira miliyan 60 dangane da sace ƴan matan a baya.
A lokacin sace ‘yan matan Jangebe a 2021, gwamnan Jihar Zamfara na lokacin ya musanta cewa an biya fansa.
A Karshe
Bidiyon da ake yaɗawa ba sabon ba ne, kuma ba shi da alaka da sace mutanen a Jihar Neja da rahoton AFP ya ambata. Saboda haka, wannan iƙirari yaudara ce.
