African LanguagesFact CheckHausa

Jawabin Boakai da ake yadawa a matsayin sanarwar zababben shugaban kasa, yaudara ce kawai

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi: zababben shugana kasar Laberiya Joseph Boakai ya sha alwashin shawo kan cin hanci da rashawa a gwamnatinsa. Wannan batun ya shiga ko’ina a kafofin sadarwa yanzu kuma ma har ya bayyana a shafin labarai na GNN.

Jawabin Boakai da ake yadawa a matsayin sanarwar zababben shugaban kasa, yaudara ce kawai

Sakamakon bincike: Yaudara! Bincikenmu ya nuna mana cewa tsohon jawabi ne wanda ambasada Boakai ya yi ranar 12 ga watan Yulin 2023 a shafinsa na Facebook lokacin ana ganiyar zabe. Haka nan kuma, shafin labarai na GNN ya goge batun daga shafin, yayin da jam’iyyarsa ta UP ita ma ta fitar da sanarwar da ke karyata batun.

Cikakken bayani

Hukmar Zaben Kasa NEC ta ayyana madugun adawa Joseph Boakai a matsayin wanda ya lashe zagaye na biy na zaben Laberiya.

Boakai ya yi nasara da kuri’u 814,428, wanda ya ba shi fiye da kashi 50 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada yayin da shi kuma George Weah ya sami kuri’u 793,910, kenan kashi 49.36 cikin 100. Tun kafin NEC ta sanar da sakamakon a hukumance,  shugaba George Weah ya kira abokin hamayyarsa ya taya shi murna

To sai dai ranar Lahadi 19 ga watan Nuwamban 2023, jaridar GNN ta wallafa wata sanarwa tana zargin wai sanarwar ta fito ne daga zababben shugaban kansa. Sanarwar wadda aka yi wa taken “Sanarwa ta musamman daga Amb. Joseph Nyumah Boakai Sr, shugaban jam’iyyar UP kuma zababben shugaban kasa na jamhuriyar Laberiya,” ya yi tsokaci kan bayar da fifiko wajen yaki da cin hanci da rashawa a ranarsa ta farko a kan kujerar mulkin kasar. 

Wannan sanarwar ta cigaba da bayyana hanyoyin da gwamnatin ta Boakai ta ke kyautata zaton za ta bi dan yaki da cin hanci da rashawa da kuma gurfanar da shugabannin da suka rika karbar hanci da rashawa a gwamnatin Weah. Wannan sakon ya yi sanadin cece-kuce tsakanin ‘yan laberiya.

Tantancewa

Garin tantance wannan labarin, DUBAWA ta gano cewa jim kadan bayan da ya wallafa wannan labarin, shafin GNN ya goge batun gaba daya a shafin.

Bugu da kari, wannan sanarwar, Amb Boakai ne da kansa ya wallafa wannan bayanin a shafinsa ranar 12 ga wtaan Yulin 2023, amma ba tare da ambatar cewa shi ne zababben shugaban kasa ba. A lokacin, ba’a riga ma an fara zaben shugaban kasa na shekarar 2023 ba.

Domin sake tabbatarwa jama’a cewa wannan bayanin da ake yadawa ba daga zababben shugaban kasar ya fito ba, jam’iyyar UP, ranar 19 ga watan Nuwamba ta fitar da na ta sanarwar tana karyata batun.

Sakataren jam’iyyar Amos Tweh ne ya wallafa sanarwra a shafinsa na Facebook  inda ya fayyace cewa wannan bayanin karya ce kawai irinta masu neman tayar da zaune tsaye.

A Karshe

Bayan tantancewar DUBAWA, mun gano cewa sanarwar da ake yadawa dangane da Amb. Boakai yaudara ce.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button