Getting your Trinity Audio player ready...
|
Zargi: A dangane da sakamakon zabe da ake dako na kotun sauraren zaben shugaban kasa (PEPC) Goodluck Jonathan yayi gargadi ga Shugaba Bola Tinubu kar yayi katsalandan kan harkokin shari’a.
Sakamakon bincike: Jawabin ba daidai ba ne, yada bidiyon an yi shine don yada wata manufa. Mista Jonathan yayi jawabinsa ne kai tsaye ga ‘yan siyasa a wani taro da aka yi watan Janairu, 2023. Labarin yaudara ce.
Cikakken sakon
Tessy Update, wata mai yada bayanai a shafin Facebook a baya-bayan nan ta wallafa wani bidiyo na minti hudu da sakan 45, wanda ta ce tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yayi gargadi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ka da ya sake yayi amfani da kujerar mulkinsa wajen sauya hukuncin kotun sauraren korafin zabe na shugaban kasa (PEPC).
Wannan ‘yar fafutuka ta blogger ta kara rubutu kan bidiyon da cewa: “LABARI DA DUMI-DUMI!! Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya wargaza ko’ina bayan da ya gargadi Tinubu da ahir kada yayi amfani da kujerar da yake kai a sauya hukuncin kotun sauraren karar zabe, ya ce matasa na kallo.”
Wannan bidiyo ya samu masu kallo 479,000 da wadanda suka nuna sha’awa (likes) 12,000 da masu yadawa (shares) da masu tsokaci 1,300 babu wanda ya nuna tantama kan sahihancin labarin.
Kotun sauraren karar zaben da ta fara saurare a ranar 8 ga watan Mayu kan sauran ‘yan jam’iyyu da ke kalubalantar nasarar shugaban na Najeriya a zaben da aka yi da hukumar zabe INEC ta bayyana na daf da cika kwanaki 180 da aka ware mata, a hannu guda ana ci gaba da samun kace-nace masu amfani da shafukan sada zumunta na amfani da shafukan don yada manufofunsu.
Duba da tasirin da tsohon shugaban ke da shi a tsakanin ‘yan Najeriya da barazanar da yada irin wannan labari ke da shi ya sa DUBAWA shiga aikin bincike kan kalaman.
Tantancewa
Bayan duba na tsanaki kan bidiyon da aka sassauya, babu inda Mista Jonathan ya bayyana sunan Tinubu, sai dai ya yi gargadinsa da cewa “ya ku ‘yansiyasa da jami’an tsaro da ma’ikata” kada ku yi amfani da mukamanku ku hana fannin shari’a yaci gashin kansa.
Mun kuma lura cewa wadda ta wallafa bidiyon ta dauko shine daga shafin BM Motions, kamfanin da ke harkokin gidajen kallon fim inda tayi amfani da shafinsu na Tiktok. Sai ta dauko tsohon bayanin Jonathan ta dora murya kafin ta sanya kalaman da take ikirari yayi. Sauran abubuwan da take wallafawa a shafinta ma haka suke.
Bayan mun ga bidiyon na asali daga BM Motions, mun gudanar da bincike ta hanyar amfani da Google. Mun gano labari da jaridar Sun ta wallafa mai taken “Kada ka yi amfani da karfin mulkin siyasa ka cukwikuya fannin shari’a, da al’umma-Jonathan.”Wannan labari an dauko shi daga wancan bidiyo amma ba a fadi inda abin ya faru ba da lokaci da Mista Jonathan ya ba da bayanin.
Wani abin mamaki irin wannan labari aka wallafa watanni bakwai da suka gabata, kamar yadda aka gani a shafin The Cable da The Guardian, tsohon shugaba yayi jawabi a lokacin kacddamar da littafi don girmama Kate Abiri yanzu (marigayiya) tsohuwar alkaliyar alkalai ta jihar Bayelsa a birnin Yenagoa, bayan da ta yi ritaya. A jawabinsa ya yi janhankali ga ‘yansiyasa da su guji haifar da rudani ga sha’anin shari’a. Wannan taron an yi shine a ranar 13 ga Janairu,2023 kafin babban zabe.
Domin tantance bidiyon da ke yawo wanda aka dauko a yayin taron, mun dauko bidiyon da alakanta shi da hotunan shafin Facebook na wadanda suka je taron.
An lura da irin kwalliyar da aka yi ta kawata wajen taron inda aka yi amfani da kaloli guda biyu fari da janbaki. Haka kuma Mista Jonathan ya bayyana da irin kayan dauke da makirho da launin shudi a kasanta.
A lokacin bincikenmu, mun gano cewa Mista Jonathan yayi jawabin ne a watan Janairu, ko da dai an yi wa jawabin nasa kwaskwarima, amma a kafatanin jawabin babu inda ya kama suna sabanin yadda aka yi zargin yayi.
A Karshe
Bayanan da ake cewa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya yi gargadi ga Shugaba Bola Tinubu kan tsoma baki kan sakamakon hukuncin shari’ar zaben shugaban kasa ba gaskiya bane. Mai wannan ikirari ko da’awa ta yi kwaskwarima kan tsohon bidiyo don ta yada labarin yaudar