African LanguagesHausa

Karya ce! Kotu ba ta sauke gwamnan rikon kwarya na jihar Rivers ba

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Kotun Tarayya a Rivers ta sauke gwamnan riko tare da ba shi umurnin fita gidan gwamnati cikin sa’o’i 48.

Karya ce! Kotu ba ta sauke gwamnan rikon kwarya na jihar Rivers ba

Hukunci: Karya ce. Babbar kotun jihar Rivers ta musanta wannan labarin, inda ta ce alkalin da aka ce ya bayar da umurnin yanzu haka yana hutu.

Cikakken Bayani

Rikicin jihar Rivers na ci gaba da daukar sabon salo tun bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya dokar ta baci ya kuma nada gwamnan rikon kwarya a jihar na tsawon watanni shida domin daidaita al’amurra. 

Ana tsaka da haka ne wani labari ya rika yawo a yanar gizo da ke cewa wata kotu a jihar Ribas ta bayar da umarnin cire gwamnan na rikon kwarya gwamnatin jihar, haka kuma ta umarce shi da ya fice daga gidan gwamnatin jihar cikin sa’o’i 48. 

An wallafa wannan labarin a shafin Facebook mai suna Media Advert, hakama a shafin X da shafin yanar gizo na U24Reports da Southern Examiner da kuma Neptune Prime.

Rahotannin sun ce hukuncin da kotun ta yanke ya bada umurnin mayar da Gwamna Siminalayi Fubara kan kujerarsa, wanda hakan zai iya kawo karshen dokar ta-baci da Shugaba Tinubu ya kafa a jihar.

Wannan ikirari dai ya haifar da zazzafar muhawara da ce-ce-ku-ce kan halin da jihar Rivers ke ciki.

Zuwa ranar 17 ga watan Afrilun 2025, an yada labarin a shafin Media Advert na Facebook sau 373 yayin da aka yi sharhi 161 sai kuma alamar so har 1,100.

Ganin yadda labarin ya dauki hankali, ya sa DUBAWA yin bincike domin tabbatar da gaskiya da kuma ingancin bayanan da ake yawo da su.

Tantancewa

Matakin farko, DUBAWA ta yi amfani da shafin nema na Google domin gani ko wata jaridar ta wallafa irin wannan labarin.

Mun gano cewa wasu kafafen yada labarai masu inganci sun ruwaito labarin da ke cewa ba gaskiya ba ne batun sauke gwamnan rikon kwarya na jihar Rivers.

Jaridar Guardian Nigeria ta ce a wata sanarwa da babban magatakarda na babbar kotun dake jihar Rivers, David Ihua-Maduenyi ya sanyawa hannu, kotun ta fayyace cewa mai shari’a Boma Diepiri, wanda aka ambaci sunansa a cikin rahoton, alkalin babbar kotun jihar Ribas ne, ba babbar kotun tarayya ba.

“A halin yanzu Diepiri ya je domin yin hutun Esther, wanda ya fara a ranar 14 ga Afrilu, 2025, kuma alkali da aka sanya aiki na musamman kawai ke zaman kotu a wannan lokacin,” in ji sanarwar.

Kotun ta jaddada cewa babu wata babbar kotun jihar da ta bayar da wani umarni dangane da abin da ya shafi rahoton cewa an bai wa gwamnan rikon kwarya na Rivers sa’o’i 48 ya fice daga gidan gwamnati.

Jaridar Daily Post Nigeria ta ruwaito irin wannan labarin

A Karshe

Ba gaskiya ba ne, babbar kotun Rivers ta ce babu alkalin da ya yi wannan hukuncin.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »