Firaministan Ostiraliya Anthony Albanese Asalin hoton P.C. Pinterest
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook, Shop A3, yayi zargin cewa kasar Ostareliya ta ba da dala miliyan $50 a matsayin tallafi ga kasar Iran.

Hukunci: Karaya ce! Bincike da DUBAWA ta gudanar ta gano cewa gwamnatin Ostareliya bata ba da wani tallafi ba ga Iran sai dai kasar Afghanistan.
Cikakken Labari
Gwamnatin kasar Ostareliya ta dauki matsaya mai kwari na adawa da kasar Iran a yakin da ake gwabzawa tsakanin Iran da Isra’ila inda ta nuna cewa tana tare da Amurka da Isra’ila take kuma Alawadai da matakin da mahukuntan Tehran ke yi na haifar da hatsaniya a yankin Gabas ta Tsakiya.
Firaminista Anthony Albanes ya bayyana cewa Ostareliya ba za ta goyi bayan gwamnatin Iran ba ko ta wane hali, inda ya kafa hujja da “yadda take rikita yankin ta hanayar shirinta na makamai masu linzami da fatan kasar na ganin ta mallakai makamin nukiliya da daukar nauyin masu tada kayar baya.”
A wani sakon hadin gwiwa gwamnatin ta Ostareliya ta dauki bangaren Amurka da ke fafatawa da Iran, inda take bayyana cewa “za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da ganin Iran bata ci gaba da haifar da rashin zaman lafiya ba da rashin tsaro na al’ummar kasa da kasa.”
Ministan harkokin waje Penny Wong ya fitar da nasa sakon inda ya jaddada cewa halayyar Iran babbar barazana ce “ kai tsaye ga al’ummar da ke a wannan yanki dama zama barazana ga tsaron kasar Ostareliya.
Sai dai duk da haka mai amfani da shafin na Facebook Shop A3, yayi zargin gwamnatin Ostareliya da ba da tallafi na dala miliyan $50 ga kasar ta Iran.

Hoton da’awar da aka dauka
Da dama masu bin wannan shafi sun dauka cewa abin da yake fadi gaskiya ne

Tsokaci daga da’awar
Akwai ma wata da’awar irin wannan a nan. DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan da’awar don tabbatar da ganin cewa ba a yaudari al’umma ba.
Tantancewa
DUBAWA ta hanyar amfani da Google ta bincika ko da za a ga wata kafar yada labarai sahihiya da ta yi wannan labari amma babu ko da guda daya.
Na biyu da aka zurfafa bincike ma an gano cewa ba a ma fahimci bayanin da ake son isarwa ba. A cewar Ministar harkokin waje Penny Wong, akwai kudade dala miliyan $50 da aka ware don kai dauki na kayan agaji a Afghanistan.
Ya zuwa watan Maris 2026, gwamnatin Ostareliya ta bayyana matsayarta cewa ba za ta shiga yakin da ake yi da Iran ba, kamar yadda ministan harkokin waje Penny Wong, guda daga cikin kasashe da ke amfana da tallafinsu ita ce kasar Afghanistan ba kasar Iran ba kamar yadda mai da’awar ya nunar.
Karshe
Bincikenmu ya nunar da cewa Ostareliya bata ba da kayan tallafi na kimanin kudade dala miliyan $50 ba ga kasar Iran, sai dai ta bayar ga Afghanistan.
