African LanguagesHausa

Karya! Kanar Goita bai yi barazanar kai hari Abuja ba 

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi: Kanar Assimi Goita na barazanar mamayar Abuja sa’annan ya yi alkawarin dora anihin zababben shugaban kasar Nigeria a zaben 2023 idan har ECOWAS ta dauki matakin soji a kan Nijar.

<strong>Karya! Kanar Goita bai yi barazanar kai hari Abuja ba </strong>

Sakamakon binciken: Karya. Rahoton da ya sanar da wannan furucin bai bayar da hujjojin da suka tabbatar cewa Kanar Goita ya yi wannan barazanar ba.

Cikakken bayani

Wani shafin Facebook da ke bayyana kansa a matsayin shafin jam’iyyar LP reshen jihar Filato, ya wallafa wata sanarwa wadda ake zargi shugaban wucin gadi na Mali ne ya bayyana cewa zai kai harin mayar da martani a babban birnin Najeriya wato Abuja idan har Ecowas ta dauki matakin sojin da ta ke barazanar dauka a kan birnin Yamai na kasar Nijar.

Haka nan kuma an yi zargin cewa shugaban mulkin sojin ya fadawa gwamnatin Najeriyar mai watanni hudu a mulki yanzu cewa suna sane da wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 kuma yana iya zuwa ya sanya “zakarar” a kujerar mulkin shugabancin kasar idan har ba’a yi hankali ba.

“Idan har ECOWAS ta kuskura ta shiga Yamai, Nijar, ba sa baki kadai za mu yi ba, da ni da dakaru na za mu shiga Abuja mu dora ainihin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 2023 bisa kujerar mulkin kasar,” wani bangare na sanarawar ya bayyana.

Wannan zargin ne mutane da daba suka sake rabawa a shafukansu na Facebook, a wuraren da suka hada da  nan, nan, nan, nan da nan.   

Ranar Asabar, 26 ga watan Yuli, sojojin da ke tsaron shugaban kasa suka anshe mulki a Jamhuriyar Nijar a karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani. Yayin da hambararren shugaban kasar kuma suka yi mi shi daurin talala a fadar shugaban kasar

To sai dai hambarrar da shugaban kasar da aka zaba bisa tsarin dimokiradiyya a kasar ta yankin Sahe, ta janyo suka sosai daga makotanta kasashen yankin yammacin Afirka da kasashen ketare wadanda suka hada da Amurka da Faransa. Ya kuma yi sanadin mahawarori a al’ummomin kungiyar Tarayyar Turai.

ECOWAS ta yi ta godo da sojojin ba tare da yin nasara ba, har ma ta hada da barazanar daukar matakin soji, wa sojojin tana kira a gare da su da su mayar da iko hannun gwamnatin demokiradiyyar da ta hambarar, bukatar da jagoran juyin mulkin JanarTchiani ya yi watsi da shi. Shugaban sojojin ya ma yi tayin cewa za su rike mulki na tsawon shekaru uku kafin a mika mulki ga farar hula a kasar wadda ke fama da rikici.

Tun da aka wallafa wannan batun a shafin Facebook zargin ya sami alamar Like 179 kuma an raba shi har sau 49, a ranar 27 ga watan Agustan 2023.

Tsokace-tsokacen da aka yi a karkashin batun ya zo daidai kurakuran da aka samu a zaben shugaban kasa wadanda suka sanya mutane bayyana rashin tabbas da rashin gamsuwarsu da sakamakon zaben da ya sa shugaba Tinubu a fadar Aso Rock.

“Gaskiya ne, ‘yan Najeriya sun san wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar,” a cewar, Ikyemye Aondoakula Michael.

“Tinubu ya sanya Najeriya cikin wani hali na ha’ula’i. Wannan abin kyama ne kuma mai tayar da hankali….” wani mai suna Bamijaiye Kolade Michael ya bayyana.

Ganin yadda zargi irin wannan ke da sarkakiya, da ma irin tsamin dangantakar da ke tsakanin Nijar da Ecowas yanzu, DUBAWA ta ga ya dace a tantance gaskiyar wannan lamarin.

Tantancewa

Mun gudanar da binciken mahimman kalmomin da ke da dangantaka da zargin kuma mun gano shafukan yada labaran da suka yi amfani da labarin, wadanda suka hada da Gist Mania, Kemi Filani News, News Now Nigeria (NNNG), da Ghana Web. Nairaland Forum shi ma ya wallafa amma daga baya ya dawo ya cire labarin. 

To sai dai wani abun da ya bayyana a rahotannin (Duk da cewa labarin iri daya ne) shi ne dukkansu sun ce shugaban Malin ya bayyana hakan ne sadda ya ke “ganawa da manema labarai kwanan nan.”

Mun nemi duka ganawar da kanar Goita ya yi kwanan nan da manema labarai, kuma mun gano wadannan labaran wadanda aka wallafa a kafar yada labaran Amurka Cable News Network (CNN), Nigerian Tribune, da Voice of Nigeria (VON). Rahotannin sun nuna cewa kanar din ya tabbatar da tattaunawarsa da shugaban kasar Rasha Validimir Putin, inda shugaban ya jaddada mahimmancin wanzar da zaman lafiya a kasar Nijar din da ke fama da dambarwar siyasa.

Mun kuma sake gano wani labarin a wata tashar Islam, Islam Channel inda Nijar  ke bai wa kasashen Mali da Burkina Faso damar sa baki da dakarun sojojinsu idan har wata kasar waje ta dauki matakin soji a kanta. Bisa bayanan rahoton, wannan martani ne ga taron da Ecowas ta gudanar a Ghana inda ta ayyana cewa dakarun kasashen kungiyar baki daya na kasa kuma a shirya suke su afkawa dakarun sojin da ke karkashin jagorancin Tchiani. “Da zarar aka na su umurni.”

Mun gudanar da bincike a sauran kafafen yada labarai masu nagarta dangane da batun, ko da zamu ga wani abu dangane da furucin Goita a kan shiga babban birnin Najeriya Abuja.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da labari makamancin wannan. Haka nan sum a sun ce furucin na bai daya wanda ministocin harkokin ketaren kasashen uku suka ayyana sadda suka gana a birnin Yamai.

 Voice of America (VOA) ta sake jaddada wannan batun.

Sai dai bacin haka babu kafar da a cikin rahotanninta ta ce kanar Goita ya fito ya ce zai kai har Abuja ko kuma dai ya yi barazanar cewa zai anshe iko ya baiwa  zababben shugaban kasar Najeriya.

A Karshe

Wannan zargin karya ne. Kafofin yada labarai masu nagarta wadanda suka yi wannan labarin ba su ce Kanar Goita ne ya yi wannan furucin ba. Daga karshe kuma, Mali ta sami wakilcin ministan harkokin wajenta sadda ita da takwararta na Burkina Faso suka  yi maganar marawa Nijar baya ko da an kai mata hari.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »