African LanguagesHausaMainstream

Da gaske ne! Dakarun Kwango sun hallaka masu zanga-zanga a birnin Goma

Getting your Trinity Audio player ready...

Zargi: Dakarun sojin Kwango na FARDC, sun kai hari kan fararen hulan da ke zanga-zanga a birnin Goma

Da gaske ne! Dakarun Kwango sun hallaka masu zanga-zanga a birnin Goma

Sakamakon Bincike: Gaskiya. Kafofin yada labarai masu nagarta sun yi rahoto kan batun, kuma kafar yada labarai ta kasa da kasa ta Aljazeera ta tabbatar da sahihancin bidiyon da ake yada wa dangane da tashin hankalin.

Cikakken bayani

Wani shafin Facebook mai suna perspective Kantangaise  da Faransanci wato ra’ayin Kantanga ya wallafa wani bidiyo na dakarun Jamhuriyar dimokiradiyyar Kwango (FARDC) a matsayin wadanda ke da alhajin kisar da aka yi na fararen hula a Goma, birnin da ke Jamhuriyar dimokiradiyyar Kwangon.

“Shaidun gani da ido sun kwatanta yadda yanayin mai ban tsoro ya kasance, inda dakarun,a  maimakon zuwa  su yi gwagwarmaya da ‘yan tawayen da ke buya a tsaunaka kamar yadda ya kamata suka gwammace dawo wa cikin al’umma su yi harbin kan mai uwa da wabi a kan titi suna kashe duk wanda suka gamu da shi a kan hanya,” wani bangare na bidiyon ya bayyana.

A bidiyon mai kusan minti biyu, an hango manyan motocin sojoji da dakarun suna tsaron hanyoyi da tituna. To sai dai har yanzu ba’a kai ga tantance ko su ne ke da alhajin kashe mutanen da aka gansu suna kwashe gawawwakinsu daga wurare daban-daban suna lodawa a kan  manyan motocin ba.

Bidiyon ya kuma kara da cewa lamarin “ya bar mazauna cikin fargaba” musamman ma saboda rashin “martani mai kwari” daga kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasa da kasa, da manyan kungiyoyin siyasa wanda ke cigaba da ta’azzara yanayin firgicin da mazaunan ke ciki.

Bidiyon ya kuma kara jaddada zargin da cewa da yawa na sukan wannan cin zarafin da sojojin suka yi a abun da ake wa kallon “take hakkin jama’a maimunin gaske.”

Bidiyon ya kuma gwado rahotannin da aka yi a baya na cewa FARDC ita ce da ma ta fi kowa aikata laifukan da ke take hakkin bil adama a kasar da ke fama da rikici da rashin daidaito. Wannan kashe-kashen da dakarun suka yi ya kara karfafa batun tunda suna aikata ayyukan nasu ne ba tare da wata fargaba ko la’akari da lafiyar jama’ar al’ummar ba.” Bidiyon ya bayyana.

Masu amfani da shafin sun kalli bidiyon sau 477 views, mutane 17 lsun latsa alamar like, mutane biyu sun yi tsokaci a kai kuma an raba sau 16, daga sadda aka wallafa labarin zuwa biyar ga watan Satumban 2023.

Saboda mahimmancin wannan zargin ne ya sa muke so mu tantance sahihancin shi.

Tantancewa

Mun gudanar da binciken kalmomi na musamman, wannan da ya kai mu ga rahorani da dama a ciki har da wani wanda kungiyar kare hakkin bil adamd ta Human Rights Watch ta wallafa. 

Human Rights Watch ta sanar cewa “jami’an tsaron kasar Kwango sun harbe mutane da dama har lahira sadda suke zanga-zanga.” Rahoton ya kuma kara da cewa hakan ya faru ne ranar 30 ga watan Agustan 2023 a birnin Goma.

Daga nan sai muka sake amfani da wata kalmar da ke da mahimmanci a batun wadda ita kuma ta kai mu zuwa shafin kamfanin dillancin labaran Associated Press inda suka bayar da labarin a cikin wannan rahoton

“Mun sami labarin wata arangama tsakanin dakarun sojin Kwango da mambobin wata kunguyar addini, wadanda ke zanga-zanagr nuna adawa da wata kungiyar yamma inda suka hallaka akalla mutane 26,” wani bangaren rahoton ya bayyana.

Rahoton ya kuma sake cewa tashin hankali ya barke ranar Laraba a birnin Goma wanda ke yankin gabashin kasar inda mabiya Wazalendo — sunan addinin, duk da cewa an magajin garin ya hana su shigowa birnin suka turje suka shigo suna zanga-zangar nuna adawa da tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyin kasa da kasa.

Sai dai mu mun so mu samu tabbacin cewa lallai hotunan da aka nuna a cikin bidiyon sojojin Kwangon ne suke kwasar gawawwakin wadanda suka kashe kuma hakan ne a zahiri. Dan haka sai muka nemi mahimman kalmomin da ke da alaka da kowani irin bidiyo mai kama da wannan.

Daga nan sai muka sami wani bidiyo mai kama da shi wanda kafar yada labaran Aljazeera ta wallafa a shafin bidiyoyinta da ke tashar YouTube, inda muka ga cewa hotunan iri daya ne da wanda aka muke kokarin tabbatar da sahihancin shi, a cewar Al Jazeera “ana kyautata zaton cewa gawawwakin mutanen da dakarun kwango suka kashe ne sadda suke zanga-zangar nuna adawa da Majalisar Dinkin Duniya.”

A karshe

Wannan zargin gaskiya ne. Rahotanni daga kafafen yada labarai masu nagarta sun tabbatar da sahihancin bidiyon, kuma tashar Al Jazeera ta sanya bidiyon a shafinta ta tabbatar da sahihancin shi.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button