African LanguagesHausa

Karya! Mataimakin shugaban Najeriya bai yi sharhi ba kan al’ummar Igbo da ke harkokin kasuwanci a Legas ba

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X, Simon Ekpa, yayi wata wallafa inda ya nunar da cewa wani sakon murya da ake zargin muryar mataimakin shugaban Najeriya ce Kashim Shettima yayi sharhi kan lamuran da suka shafi harkokin kasuwanci na al’ummar Igbo a jihar Legas.

Karya! Mataimakin shugaban Najeriya bai yi sharhi ba kan al’ummar Igbo da ke harkokin kasuwanci a Legas ba

Hukunci: Karya ce! Bincike da DUBAWA ya gudanar ya gano cewa wannan muryar ba ta mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ba ce, bai yi wannan sharhi ba kan al’ummar Igbo da ke harkokin kasuwanci a Legas ba.

Cikakken Sakon

Simon Ekpa, wanda ke bayyana kansa a matsayin firaministan Biafra da ke gudun hijira ya wallafa (posted) wani sakon murya a shafin X a ranar 13 ga watan Afrilu, 2024, inda yake da’awar cewa muryar mataimakin shugaban Najeriya na yanzu Kashim Shettima ce.

Sakon muryar da aka wallafa a matsayin bidiyo na da tsawon mintuna biyu da dakika ashirin, wanda ya nunar da yadda yake sharhi ko tattaunawa kan harkokin kasuwanci na al’ummar Igbo a jihar Legas da ma wasu batutuwa da suka shafi siyasa. 

 “Idan kun manta wannan muryar mataimakin shugaban Najerya ce Boko Haram Shettima kamar yadda ya wallafa .

Ya zuwa ranar 21 ga watan Yuni, 2024 wannan wallafa ta samu wadanda suka sake yadawa (reposts) 2,208, da wadanda suka kalla (views) 49,000 da wadanda suka nuna sha’awarsu (Likes) 2,476 da wadanda ke kafa hujja (quote) 76.

Bayan yin filla-filla da hotunan da muryar ta hanyar amfani da Google Lens, DUBAWA 

ya gano cewa wannan sakon murya an taba wallafa shi (posted ) a shafin facebook a ranar 6 ga watan Nuwamba,2022 a kan wani shafi mai suna  Africa Facts, inda yake cewa “Da kamar wuya a amince wannan wani sakon murya ne da ya fita na Shettima da abin da yake cewa kan al’ummar Igbo. Shin wannan da gaske ne ko karya ne?” 

DUBAWA ya shirya gudanar da bincike kan wannan da’awa ganin yadda ake tsokaci kanta a shafin na X ga kuma yadda wasu ke nuna tantama a Facebook.

Shin waye Simon Ekpa?

Simon Ekpa dan fafutuka ne ta ganin an kafa kasar Biafra. A watan Maris 2024, an ga rundunar sojan Najeriya ta wallafa sunansa cikin jerin mutane masu laifi da ake son kamawa ruwa a jallo (wanted list) tare da wasu mutanen 96 daga sassa daban-daban na Najeriya. Saboda wasu laifuka da suka hadar da ta’addanci da manyan laifuka da barazanar ballewa daga kasa.

Ekpa da ke zaune a Finland,  shi ke jagoranci na wani bangare na masu fafutukar ganin sun balle daga Najeriya da kafa  kasar Biafra (Indigenous People of Biafra (IPOB),) ’yan fafutukar nan da ke a kudancin Najeriya da ke sanya mutane suna zaman gida a ranakun Litinin a yankin.

Tantancewa

DUBAWA ya gano cewa asalin muryar ta mutane biyu ce wadanda ke tattaunawa, bayan nazari tsakanin muryoyin biyu mun gano babu inda suke kama da muryar mataimakin shugaban Najeriya bayan nazartar inda yake maganganu a wuraren taruka na aiki kamar anan  (here) da nan (here.)

Haka kuna DUBAWA ta tuntubi mai taimaka wa mataimakin shugaban na Najeriya Kashim Shettima kan harkokin yada labarai — Stanley Nkwocha.

Mai taimaka wa mataimakin shugaban ya  ce babu inda mai gidansa yayi magana a cikin sakon muryar.

“Wannan tsabar farfaganda ce, wannan ba muryar mataimakin shugaban kasa ba ce, shi baya irin wannan magana mara kan gado, ba shi bane ai yana da ilimi da wayewar da ba zai yi irin wannan kalamai ba,” a cewarsa.

Ya kara da cewa wannan sakon murya baya kan intanet a lokacin yakin neman zabe na 2023.

Haka nan DUBAWA ma ya gano cewa babu wata muhimmiyar jarida da ta dauki wannan labari  ko wani abu mai kama da haka, wanda aka danganta shi da mataimakin shugaban Kashim Shettima.

Karshe

A binciken da DUBAWA ya gudanar ya gano cewa muryar da ke cikin sakon ba ta mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima ba ce, bai yi wadannan kalamai da ake zargin yayi su kan al’ummar Igbo da ke harkokin su a Legas ba. 

An fitar da rahoton  karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 da shirin kwararru na Kwame KariKari  da hadin gwiwar The Informant247, don dabbaka “gaskiya”a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin kasar.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »