African LanguagesHausa

Karya ne! Bayanan Akpabio na yadda majalisar dokoki ta kasance a karkashin jagorancin David Mark 

Getting your Trinity Audio player ready...

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio bai fadi gaskiya ba lokacin da  ya yi wa ‘yan Najeriya bayani kan irin ayyukan da majalisar ta yi a majalisa ta  shida da ta bakwai wadanda suka kasance a karkashin jagorancin David Mark, kamar yadda wani cikakken binciken da PREMIUM TIMES ta yi ke nunawa.

Mista Mark,wanda birgadiya janar ne mai ritaya ya jagorancin majalisar dokoki tsakanin shekarun 2007 zuwa 2015 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya kasance sanatan mazabar Benue ta Kudu na tsawon wa’adi biyar, daga shekarar 1999 har zuwa 2019.

A wani zama a ranar Alhamis, Mista Akpabio ya bayyana cewa majalisar karkashin Mark na zama tsakanin karfe biyu zuwa biyar na yamma don samar da lokaci da zai zama abin da ‘yanmajalisa ke so, ko za su fi jin dadi.

Da’awar

Shugaban majalisar dattawa a Najeriya ya bayyana cewa lokacin zaman majalisa a hukumance zamanin Mista Mark na farawa ne daga karfe biyu na yamma zuwa karfe biyar na yamma. 

”Lokacin da mai girma shugaban majalisar dattawa Sanata Mark na jagorancin majalisa , kamar ma yadda ya samu a nayi , majalisa na zama ne daga karfe biyu zuwa biyar saboda suna amfani da lokacin safiya wajen tattaunawa da jam’ai na diflomasiya, su tattauna da ma’aikata sannan sai su fara zaman majalisa da karfe biyu na rana.”

“A hukumance suna fara zama ne daga karfe biyu zuwa biyar na yamma, kuma na sani cewa da dama a cikinku za ku so irin wannan lokaci, ku gana da wasu daga cibiyoyi, ku kammala, ku bayyana jin ra’ayin jama’a kafin zuwa a zauna, amma ba a bune da za a bayyanawa al’umma ba, saboda al’umma sun za ta cewa muna zama ne kawai mu kadai.” a cewar Mista Akpabio.

Shugaban majalisar ya bayyana haka ne a lokacin da ake muhawara kan batun sauya lokacin zaman majalisar daga karfe 10 zuwa 2 na rana ya koma daga 11 na safe zuwa 3 na rana. 

Bincike kan da’awar

Domin gudanar da bincike kan wannan da’awa da Mista Akpabio yayi jaridar PREMIUM TIMES ta yi amfani da tuntubar mutane da duba bayanai da aka tattara a hukumance.

Abu na farko shine Dokar Majalisa wacce ke zama tanadi na hukuma ta yi wanda shi ke jagorantar yadda majalisar ke gudanar da ayyukanta karkashin Mista Mark.

Wannan jarida ta kuma duba yadda ake zabe da zama a majalisar wanda shine abin da ake tattarawa kowace rana kan abubuwan da suka faru a majalisar a ranakun zamanta.

Sannan wannan jarida ta tuntubi danmajalisar dattawa a lokacin da Mista Marka ke jagorantar majalisar dattawan, haka nan an tuntubi  ‘yanjarida da kungiyoyi masu zaman kansu wadanda ke bibiyar zaman majalisar a wancan lokaci.

Abubuwan da aka Gano

Kamar yadda dokar majalisa ta nunar a zamanin majalisa ta shida zuwa majalisa ta bakwai  ana fara zaman majalisa ne daga misalin karfe 10 na safiya.

Doka ta 8 sakin layi na 2 a cikin baka na dokokin majalisar dattawan ya bayyana cewa: A ranakun Talata da Laraba da Alhamis majalisa za ta zauna da misalin karfe 10 na safe sai dai in an samu sauyi sai ta zauna karfe biyu na rana idan dai an bijiro da wata bukata daga shugaban majalisar ko sanata wanda ke kan kujerar shugaban  ‘anan ne majalisa ke iya sauya lokacin zama idan an bijiro da bukatar hakan na neman a zauna zuwa karfe 2. Shugaban majalisar na iya dage zama ba tare da wata tuhuma ba. 

Akpabio lies, misinforms Nigerians about Senate under David Mark

Senate at plenary (PHOTO CREDIT: @NGRSenate

A bisa nazari da aka yi kan zaman da majalisa ta yi karkashin jagorancin Mista Mark daga 2008 zuwa 2010 babu inda ya nuna cewa an fara zaman majalisa daga karfe 2 aka kammala da karfe 5 kamar yadda Mista Akpabio yayi da’awa. 

Akpabio lies, misinforms Nigerians about Senate under David Mark

Jadawali da ke nuna ranaku da lokutan zaman majalisa karkashin David Mark a 2008

Ranaku da lokutan zaman majalisa karkashin David Mark tsakanin Janairu zuwa Disamba 2009Jadawali da ke nuna ranaku da lokutan zaman majalisa karkashin David Mark a 2010

Enyinnaya Abaribe, sanata ne a majalisa ta bakwai ya tabbatar da cewa abin da wannan jarida ta gano gaskiya ne.

Mista Abaribe wanda a lokacin dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Abiya ta Kudu ya fadawa wakilinmu cewa a lokacin Marka majalisa na zama ne tsakanin karfe 10 na safe zuwa 2 na rana.

“Aa lokacin zaman majalisa a hukumance lokacin Mark na farawa ne daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana”a cewarsa.

Wani mai taimakawa Mista Mark wanda ya nemi kada a bayyana sunansa yace tabbas maigidansa bai taba jagorantar zaman majalisa daga karfe 2 na rana zuwa 5 na yamma ba a lokacin da yana mulki. 

“Ba daidai bane ”haka ya fada wa PREMIUM TIMES. 

”Daga shekarar 2011 zuwa 2015 babu wani lokaci da aka sauya na zaman majalisa, idan ma akwai bukatar haka shugaban majalisar zai sanar ”ya bayyana.

Shugaban kungiyar Campaign for Democracy (CD), Ifeanyi Odili, yace majalisa karkashin Mista Marka bata taba zama ba tsakanin karfe 2 na rana zuwa 5 na yamma.

Mista Odili yace ya zauna da bibiyar zaman majalisa ta bakwai da ta takwas.

Wani mai aiki a majalisa da shima bai so a bayyana sunansa ba, saboda ba shi da hurumi na yin magana kan  majalisa dama wasu ‘yanjarida da suke bibiyar zaman majalisa sun fadawa jaridar cewa, babu wani lokaci da Mista Mark ya sauya daga lokaci da ranakun da majalisar ke zama.

Wakilin jaridar ThisDay Newspaper a majalisa Sunday Aborisade,yace Mista Mark a ko da yaushe ya kanzo majalisa a kan lokaci kamar yadda zaman majalisar ya saba.

“Ban taba gani ba lokacin da Mark ya zauna tsakanin karfe 2 na rana zuwa 5 na yamma, yana zama ne daga karfe 10 zuwa 2 na rana, na kan bibiyi zaman majalisar saboda ko da yaushe akwai sabon abu wanda babu kafar yada labarai da za ta so a bar ta a baya.”

“,Hakan ba zai yiwu ba kasancewar shi mutum ne mai mutunta lokaci ba ya fashi, mutum ne da ke da dattako” a cewar Mista Aborisade.

Uwoma Pius wani dan jaridar me bibiyar zaman majalisar a lokacin Mark yace tsohon shugaban majalisar yana zuwa majalisa mintuna 10 kafin a fara zama karfe 10 na safe a lokacin zaman majalisar zamaninsa.

“Lokacin zaman majalisa a wancan lokaci na farawa ne daga 10 na safe zuwa 2 na rana lokacin jagorancinsa shine mafi kyau ga mutunta lokaci” a cewar Mista Pius.

Hukunci

Karya ne! Bayanan Akpabio na yadda majalisar dokoki ta kasance a karkashin jagorancin David Mark 

Da’awar da Mista Akpabio yayi cewa majalisa karkashin jagirancin Sanata David Mark na zama daga karfe 2 na rana zuwa 5 na yamma ba gaskiya ba ne.

An samu tabbaci ne na hakan bayan tattaro bayanai da aka alkinta dama ji daga mutane da wannan jarida ta yi nazari.

Maimaita ba da bayanai wadanda ba na gaskiya ba

Irin wannan ba da bayanai wadanda ba na gaskiya ba, wannan ba shine karon farko ba da Mista Akpabio ke irin wadannan kalamai inda yake yaudarar abokan aikinsa da ‘yan Najeriya.

A wani zaman majalisa a watan Fabrairu, Mista Akpabio yayi da’awa (claimed) cewa gwamnonin jihohi na karbar (received) Naira miliyan dubu 30 daga asusun tarayya don rage tsadar kayan abinci a jihohinsu, amma da aka bincika wannan da’awa tasa ba gaskiya ba ce.

Gwamnonin sun caccake shi (governors criticised) daga bisani ya fito ya nemi afuwar ( apologised) kalaman da yayi.

Abubuwan da kalaman na Akpabio ka iya jawowa

Mista Odili yace ba da kalamai wadanda ba na gaskiya ba daga shugaban majalisa wanda shine na uku a tsarin shugabanci na kasa, hakan zai taba kima da darajar majalisa. Sannan ‘yankasa da masu bincike da jami’an diflomasiya za su rika kin amincewa da shugabanni na Najeriya.

“Rashin ba da bayanai sahihai ko na yaudara na iya jawowa a dauki mataki bisa kuskure wanda kuma zai iya babbar illa ga kasa a gaba. Hakan na iya haifar da rashin gasgata juna a tsakanin mambobi da masu ruwa da tsaki da al’umma. Abin da ke zama klubale wajen cimma matsaya da amincewa da kudiri. Yana iya kuma haifar da rudani, abin da ka iya jawo tsaiko a harkokin majalisa, ya jawo cikas kan hanyoyi da majalisar kan bi wajen warware wasu matsaloli masu sarkakiya.”

Ya kara da cewa “Idan bayanan da ke fita daga majalisar marasa inganci ne na iya haifar da barna, a rika ganin majalisar a matsayin mara daraja.”

Mista Odili na  Campaign for Democracy (CD) ya kara da cewa ita kanta dimukuradiyyar kasar na fuskantar barazana idan aka ci gaba da fitar da bayanai wadanda ba sahihai ba.

”Aikata yaudara na jawo durkushewar dimukuradiyya. Idan shugaban majalisar dattawan Najeriya na fitar da kalaman yaudara mafarkin da kasar ke da shi a fannin ci gaban dimukuradiyya ba zai cika ba.”’

“An samu abubuwa na ci gaba da martaba a majalisar dattawan Najeriya lokacin da Sanata David Mark ke mata jagoranci, akwai aiki tukuru da jajircewa. A fadawa ‘yan Najeriya cewa a lokacin Mark majalisa na zama daga karfe biyu zuwa biyar yaudara ce da neman lalaci a majalisar dattawan, a cewar jagoran na CD.

Jawabin Edita: Wannan bincike ya fara fita a jaridar Premium Times.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »