Zargi: Faransa za ta biya kasashen Afirkan da ta yi wa mulkin mallaka diyya
Sakamkon Bincike: Karya. Nazarin da muka yi, ya nuna cewa an gyara bidiyon da ke dauke da wannan bayanin ne domin ainihin bidiyon ba shi da wata alaka da abin da shugaban Faransan ya bayyana a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77.
Cikakken bayani
Wani bidiyon YouTube wanda ke nuna shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ja hankalin da yawa daga cikinmu saboda bayanin da aka rubuta a jikin bidiyon mai cewa “Faransa za ta biya diyya ga kasashen Afirkan da ta yi wa mulkin mallaka”
Faransa ta taba yin mulkin mallaka a wasu kasashen Afirka, wadanda suka hada da Senegal, Gambiya, Chad, Mali, Jamhuriyar Bene, Sudan, Tunisiya, Nijar, Jamhuriyar Kwango, Kamaru da Ivory Coast da ma wasu kasashen Afirka. Masu mulkin mallakan Faransan sun kama yankin farko a shekarar 1830 bayan da suka shiga kasar Aljeriya.
Bidiyon mai tsawon minti tara da dakiku biyar wanda
The nine minutes, five seconds video AlienJacketSatire ya wallafa, ya gwada sadda Mr Macron ke shiga dakin babban taron yana gabatar da jawabinsa.
Yayin da shugaban kasar Faransar ke gabatar da jawabinsa da harshen Faransanci, ana iya jin muryar wani namiji wanda ke fassara yana bayyana abin dashugaban ke cewa a harshen Faransanci.
Bidiyon ya nuna shugaban kasar Faransa mai shekaru 45 na haihuwa yana daukar alhakin irin wulakancin da Faransa ta yi wa kasashen Afirkan da ta mallaka inda ya nemi gafara.
Bidiyon ya karasa da Mr Macron yana alkawarin cewa kasarsa za ta maido da duka kudaden da ta dauke tare da farawa da “tattaunawa a bayyane kuma mai ma’ana”
Wannan bidiyon dai ya janyo martanoni daban-daban daga wadanda suka kalla yayin da wadansu suka rika tofa mi shi ashar suna nuna rashin amicewarsu da afuwar da ya ke nema, wasu kuma sun rungumi jawabin a matsayin wani abun da zai kawo gyara sai kuma wadanda suke kallon bidiyon da shakkun cewa da walakin goro a miya.
“Mu ba wawaye ba ne. Mun san cewa ba su yi nadaman komai ba. Halayyarsu ta saba wa neman gafara ta karyar da suke yi,” in ji daya daga cikin masu tsokaci, Makuwati Thokozani.
A wani tsokacin kuma cewa aka yi HALIN DA AKE CIKI DA GWAGWARMAYAR DA AKE YI…. “kusan kamar duniya yanzu ta fara sauya alkiblarta dangane da bakar fata a duniya baki daya”
“Bari mu ga ko aiki zai zo daidai da maganar fatar baki a wannan karon in ji Kasali Obanoyen.
Ganin yadda wannan batun ke da sarkakiya da ma irin martanonin da aka samu ya sa DUBAWA tantance gaskiyar wannan batun.
Tantancewa
Da muka saurari abubuwan da mai fassarar ke bayyanawa, mun lura da cewa a gabatarwarsa ya ambato cewa …. “Domin tsayawa a gaban ku yau, 30 ga watan Afrilun 2023 dan gabatar da jawabi ga wannan babban taron,” dan haka sai mzka nemi jawabin da Macron ya yi a gaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) wanda ya gudana ranar 30 ga watan Afrilun 2023, sai dai bincikenmu bai bayyana mana wani abu kamar haka ba.
Sai muka kara zuwa muka yi bitar jaddawalin shirye-shiryen da aka gabatar lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniyar da aka yi a watan Afrilun, amma nan ma mun ga cewa babu abun da aka yi ranar 30 ga watan Afrilu domin wannan ranar ma Lahadi ce.
Daga nan sai muka duba mu ga ziyararsa ta karshe a UNGA, inda mu sake ganin wannan bidiyon dai wanda AlienJacketSatire ya wallafa. Bidiyon mai tsawon minti 30 na dauke da kwanan watan 20 ga watan Satumban 2022, sadda Macron ya yi jawabi a babban taron UNGA karo na 77.
Da muka saurari wannan bidiyon sai muka gano cewa sabanin abun da AlienJacketSatire ya wallafa, mace ce ta yi fassara a cikin harshen turanci yayin da shugaban Faransar ya gabatar da na sa jawabin cikin harshen Faransanci.
Bacin hakan, batun da shugaban Faransar ke yi a bidiyon ya danganci al’amuran kasa da kasar da ke afkuwa a wancan lokacin wanda kuma ya shafi mahalarta taron da ke sauraron jawabin na sa.
Mr Macron ya ce ya fahimci burin wadanda suka yi gwagwarmaya dan tabbatar da cewa Faransa da sauran kasashen duniya suna cin moriyar ‘yan cin walwalar da suke da shi yanzu, irin su Majalisar Dinkin Duniya, kuma ya yi tsokaci dangane da yakin da ke gudana tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, da ma wasu karin batutuwa.
Wani abun da ya kamata a yi la’akari da shi a bidiyon shi ne, da shugaban Faransar ya ke jawabi, a duk sadda ya ambaci sunar wata kasa, sai kyamarorin su juya su gwado wakilan kasar da ke zaune a cikin dakin taron. Kyamarar ta yi haka sadda ya yi bayani dangane da kasashen Faransa, Rasha da Ukraine.
Idan ba ku manta ba a bidiyon da AlienJacketSatire ya wallafa, kasashen Afirkan da ya ambato ba su ma cikin dakin taron, dan haka me zai sa ya yi magana dangane da wadanda ba su ma halarci taron ba?
Bacin haka, bayani dangane da batu irin na yakin Rasha da Ukraine zai dauki lokaci sosai, musamman dan a lokacin ba’a kai shekara daya da yakin ba amma ya yi tasiri sosai a kasashen Turai.
Kuma ma zai kasance abun mamaki a ce duk lokacin da aka ba shugaban kasar Faransa ya yi amfani da shi wajen neman afuwa daga kasashen Afirka na abubuwan da shugabanin da suka yi shekaru gommai kafin shi.
Haka nan kuma, irin kalmomin da bayyana cewa shugaban kasar Faransar ya yi amfani da su wajen kwatanta abun da Faransawar mulkin mallakar suka yi a kasashen Afirka ba su yi kama da irin wadanda zai yi amfani da su ba idan ma da jawabin ya ke yi da gaske. Kalmomi kamar “amfani da hanyoyi masu kyama wajen satar ma’adinai, “ayyukan zalunci,” “mugunta,” “laifukan da ba za’a taba yafewa ba,” “bakin ciki,” “rashin kyautatawa,” “dabbanci,” da “haddasa talauci a zuri’u.”
Wannan ya yi nisa da diflomasiyya da gaskiya a fanin tattalin arziki a ce wai shugabanni wadanda aka san su da gudanar da taruka a matakin kasa da kasa za su yi amfani da irin wadannan kalmomin. Wadannan kalmomin a cikin bidiyon da aka gyara sun bayyana Macron a matsayin wanda ba ma wakiltar kasarsa ya ke yi ba idan ma a za’a ce hakan ya faru da gaske.
A Karshe
Wannan zargin ba gaskiya ba ne. Binciken da muka yi kan bidiyon ya nuna cewa an gyara shi. Bacin haka, bayanan da muka samu a shafin yanar gizo-gizo sun nuna mana cewa Majalisar Dinkin Duniya ba ta shirya komai a ranar da aka bayyana cewa an nadi bidiyon ba. Sa’annan bayanan da aka yi a bidiyon ba su shafi batutuwan da ake tattaunawa a duniya a wannan lokacin ba.