African LanguagesHausa

Kwararru sun ce turara al’aurar da mata ke yi na da hatsarin gaske ga lafiyarsu

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya rubuta cewa tafasa ganyayyaki masu kamshi tare da gishiri abu ne da kan warkar da cutar fibroids da warin al’aura da ciwon haila.

Kwararru sun ce turara al'aurar da mata ke yi na da hatsarin gaske ga lafiyarsu

Sakamakon bincike: Karya! Babu hujjojin da aka samu a kimiyance dangane da wannan batun. Likitocin mata kuma ba su goyi bayan turara farjin ba.

Cikakken bayani

Ciwon haila  ciwo ne na ciki can kusa da marar mace inda ta kan rika ji zafi mai radadin gaske a duk lokacin da lokacin jininta ya zagayo. Irin wannan radadin ya danganta da yanayin jikin macen akwai wadanda sukan zo da sauki babu radadin sossai, akwai wadanda kuma dole sai sun nemi magani kafin su sami sauki.

Wani mutumi mai suna Muhammad a shafin Facebook ya rubuta cewa mata na iya sa ruwan zafi cikin wani kwano sa’annan su zuba gishiri da wasu ganyayyaki masu kamshi dan rage cutar fibroids, tumbi, cututtukan da a kan dauka a bayi da ma ciwon haila. Daga nan ya kwatanta yadda ake turara farjin, inda ya ke cewa ya kama a yi shi a daidai sadda aka kammala haila. Ya kuma ce kamata ya yi mata su zauna a kan kwanon dan tururin ya shiga sosai. 

Wannan da’awar dai an raba shi sau 1,024, an latsa alamar like sau 402 sa’annan kuma an yi tsokaci sosai a karkashin batun tun bayan da aka wallafa shi.

Ganin yadda ya ke da nasaba da kariyar al’umma ne muka yanke shawarar tantancewa.

Tantancewa 

Mene ne turara farji?

Farjin mace gaba ce da ke mikewa wadda kuma ke da mahimmanci wajen haihuwa. Ana yawan jita-jitar cewa turara farji ya na taimakawa da radadi, kuma ya kan wanke farjin ya cire duk abubuwan da ba su da kyau har ma a mahaufa, sa’annan kuma ya rage kumburin ciki. To sai dai farjin mace yana iya wanke kan shi ta yadda zai iya daidaita sinadaran da ke wurin yadda ya kamata ba tare da wani tallafi ba. Dan haka duk wani salo kamar turarawa da sauransu ba su da amfani wajen tabbatar da lafiyar farji.

Tabbatar da tsabta a farji ta yadda zai kasance a bushe ba tare da wani mai ko turare ba shi ne kadai hanyar da ya fi dacewa wajen kula da farjin. Dan haka bai kamata mata su rika turara farji ba.

Turara farji na iya lalata sinadarin da farjin kan fitar dan kare kansa, wanda kuam shi zai iya bai wa kwayoyin cuta damar shiga su janyo ciwo. Bacin haka zai iya sauya yanayin fajin da yadda farjin zai fuskanci hatsarin kamuwa da cututtuka.

Fatar wurin na da laushi sosai dan haka ba wuya an raunata shi. Dan haka idan aka sa shi cikin tururi mai zafi, zai iya kona fatar. Wannan ba yana nufin cewa ganyayyakin ba su kawo waraka ba ne, suna iya kawo wa, amma babu wata hujja ta kimiya da ke nuna cewa turara farji na kawo sauyi.

Ra’ayin Kwararru

Gwyneth Paltrow, ta bayyana  cewa farjin mace (da mahaifa da al’aurar) abubuwa ne da ya kamata a rika wa kallon tanda irin wadanda ke wanke kansu sa kansu. Gabobin da ke sama da wadanda ke taimakawa wajen haihuwa daga kasa na da hanyoyi masu sarkakiya na kula da lafiyarsu.

A cewarta kuma, akwai yiwuwar cewa “tururin” da ke fitowa daga ganyayyakin da aka jika cikin ruwan zafin na dauke da sinadaran da ke da hadari ga al’aurar mace. Inda ta ce hanyar da za’a iya bi a kula da al’aura ita ce kawowa.

Dr Sesan Oluwasola, likitan mata a wata jami’ar koyarwa da ke kudancin Najeriya ya fadawa sashen binciken gaskiya na kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa turara farji abu ne da ba zai taba bayar da shawarar a yi ba. Dr Oluwosola ya ce yin hakan ya kan “lalata yanayin sinadaran da ke wurin dan kare farjin” kuma ana iya jin ciwo ko samun konewa. “Idan har wurin da ya kone ya warki zai iya kai ga abun da ake kira  vaginal stenosis (wato tsukewa),” ya bayyana.

Talia Crawford, ita ma likitar mata, ta bayar da shawarar cewa turara farji na da hatsarin gaske saboda ya na iya jin ciwo.

“Idan har ana so farji ya kasance cikin lafiya dole ya iya ajiye kwayoyi masu kyau,” a cewar Dr Crawford. “Dan haka, wankewa da sabulu ko wasu nau’o’in mai masu  kamshi na iya haddasa cuta. Amfani da ruwa kawai shi ne ya fi mahimmanci.”

Ta ce yawancin wadanda ke fama da ciwon al’aura ko wari duk ya kamata su yi magana da likita dan samun bayani dangane da matakan da ya kamata a dauka.

A karshe

Kwararru ko daya ba su goyin bayan turara farji ba saboda ya na da hadari. A maimakon haka, shawararsu ita ce a yi amfani da ruwa kawai a wanke, idan har ana fama da wata cuta ce kuma a tuntubi likita dan samun irin taimakon da ya dace.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button