Hoton Ini Okon. Asalin hoton: Nigerian Doctor on X
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Inibehe Okon, wanda ke ikirarin cewa shi kwararren likitan kwakwalwa ne ya shiga matsala inda ake zarginsa da zamba a harkokin iilimi, tare da tabbatar da cewa shi ba dalibin jami’ar Texas da ke Austin ba ne kamar yadda ya ke zargi, DUBAWA na da tabbacin hakan.
Ranar Talata 25 ga watan maris na shekarar 2025, Jami’ar Texas da ke Austin ta nisanta kanta daga Okon wanda ke zargin ya na da alaka da ita da wasu cibiyoyin ilimi.
Kwanan nan ne Okon ya yi suna bayan da hotunan da ke dauke da shi suka bayyana wajen kwatanta tsarin yadda ake daukar dalibai likitoci a Amurka a sunan wau shi ma likita ne a jami’ar Johns Hopkins.
Hoton Okon ya na dauke kasidar cewa shi ma dalibi ne. Asalin hoton: Chriseny on X.
Wannan hoton ya ja hankalin jama’a da yawa kuma suka rika sha’awarsa suna bayyana hakan a shafukan soshiyal mediya, wadansu masu amfani da shafin X sun sun wallafa hotunan irin bayanan da jama’a suka rika yi, inda har ma wasu ke tabbatar da cewa shi dalibi ne tun 2029.
Okon, wanda shafinsa a babban shafin masu bincike na ResearchGate ya bayyana sa a matsayin kwararren likitan kwakwalwa wanda ke da dangantaka da Jami’ar Texas na fuskantar zargin satar bayanan wani. Shafinsa na da’awar cewa ya wallafa kasidu 65. Sai dai bayanan da ake samu daga masu amfani da shafukan sada zaumunta, a ciki har da tsoffin daliban likita daga jami’ar Uyom inda ya ke da’awar cewa a can ma ya yi karatu, sun sanya alamar tambaya a kan sahihancin takardun kammala karatun da ya ke takamar ya samu.
DUBAWA ta tuntubi jami’ar Texas dan tantance sahihancin takardun na sa. Inda ta ce babu wani mai suna kamar nasa a jami’ar da ma sauran cibiyoyin da ke da alaka da ita.
“Jami’ar Texas ba ta da wani dalibi tsoho ko sabo wanda ke da wannan sunan da kuke neman karin bayani a kai,” Mike ROsen, mataimakin shugaban sahin hulda da kafofin yada labaran jami’ar ya bayyana wa DUBAWA.
DA DUBAWA ta tuntubi Okon a shafin WhatsApp, ya kaucewa tambayar ko ya taba halartar jami’ar ko bai halarta ba. A maimakon hakan sai dai ya kada baki ya ce ya riga ya tanadi daftarin da zai yi amfani da shi wajen sanar da na sa barayin labarin.
“A sane na ke da ko na yi ko ban yi ba. Zan yafe musu. Na shirya sanarwar da zan gabatar. Zan fito in bayyana cikakkiyar gaskiyar ba zan boye komai ba,” ya rubuta.
Ko daya bai amsa sauran tambayoyin da muka yi masa ba sadda muka bukaci karin bayani. Da muka yi kokarin kiransa a waya sai muka ga layin a kulle.
Mun kuma tuntubi jami’ar Johns Hopkins da Jami’ar Uyo dan tantance sauran zarge-zargen mu kuma sami karin bayani dangane da sahihanci ko nagartar takardun kammala makarantar na sa. Sai dai har zuwa sadda muka hada wannan rahoton ba mu sami amsa daga jami’o’in ba.
Tun bayan da aka fara zarginsa da aikata zambar, Okon ya rufe shafukansa na sada zumunta ya rage yawan mutanen da za su iya ganin shafin bare ma su yi ma’amala da shi.
