Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da BBC dan shirin da ta yi kan TB Joshua
Sakamakon bincike: Karya. Nazarin da DUBAWA ta yi ya nuna cewa bidiyon ba ku daya ma ba shi da wata alaka da bayanin TB Joshua, kirkiro shi kawai aka yi dan yaudarar jama’a.
Cikakken bayani
Bayan fitowar shirin BBC a kan marigayi tsohon shugaban cocin Synagogue Church of All Nations (SCOAN), Temitope Joshua, wanda BBC ta yi, wani mai amfani da shafin Instagram ya wallafa wani bayanin da ke cewa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai n da BBC saboda hadi irin wannan shirin da ta yi.
A bidiyon wanda ke da tsawon kusan minti daya, wanda mai amfani da shafin, rSylvester Lumenchristi_eboh, ya wallafa, ana iya jin shugaba Tinubu ya na karyata sahihancin bidiyon ya na kuma kokarin kushe BBC saboda yadda suka la’anta mutuncin malamin addinin, duk da cewa dai muryar da ma ainihin abun da ke faruwa inda aka dauki bidiyon ba su bayyana sosai ba.
“A matsayin na na shugaban Najeriya, na yi Allah wadai da duk wani shiri da ma hujjojin da BBC ta bayar a kan wannan bawan Allahn. Prophet T B Joshua mutun ne mai kirki, kuma ya kawo mutanen ketare da yawa zuwa jihar Legas sadda na ke gwamna. Sun tsane shi ne kawai saboda daga kasar bakar fata ya fito,” aka jiyo shugaban na cewa.
Mutane 666 suka latsa alaman like kuma a ranar Juma’a 19 ga watan Janairun 2024, an yi tsokaci 25. Ra’ayoyi sun banbanta a tsakanin wadanda suka yi tsokacin, a yayin da wasu suka amince gaskiya ne wasu nan da nan suka ce ba yadda za’a yi hakan ya faru.
“Ya yi daidai Mr President,” a cewar Sanusirufus.
“Wannan ba muryar shugaba Tinubu ba ce. Ku dai ba za ku daina irin wadannan abubuwan bogin ba ko,” a cewarmThis is not (President) Tinubu’s voice. You guys (won’t) stop all this fake news,” Ismailyusuf913.
Saboda rikicin da bidiyon ya janyo da ma irin sarkakiyar da batun ke da shi ya sa DUBAWA tantance sahihancin labarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da yin nazarin bidiyon sosai inda ta gane cewa an yi dabara ne an sa hoton Tinubu an gyara labarin yadda zai yi kama da shi a zahiri. Abin da mutun zai fi gani ma shi ne irin hasken jikin shugaban kasar a hoton da ya kan kode ya yi duhu kamar dai yadda ake gani a hotunan bogin da ake hadawa. Bacin haka kuma hotunan ba su fita da kyau ba, ko daya ba su da inganci, sun yi kiyashi-kiyashi yadda dai mutun zai san an gyara ne yadda zai yi saukin turawa a shafukan soshiyal mediya.
Har ila yau, DUBAWA ta kuma gano shi ainihin bidiyon da aka datsa aka yi amfani da shi, inda ya yi wa kasa jawabin barka da shiga sabuwar shekara. Ko daya shugaban bai kira sunan malamin addinin ko ma shirin BBCn a cikin jawabin na sa ba. Bacin haka ainihin bidiyon, cikin makwanni ukun da suka gabata ne aka dauaka, ranar daya ga watan Janairun 2024, tun ma kafin BBC ta fara watsa shirin.
Sauran alamun da ke nuna cewa an yi ha’inci ne shi ne rashin daidaiton da ake gani tsakanin muryar da hotunan domin muryar shugaban kasar ba ta zo daidai da motsin da bakinsa ke yi wajen magana ba. Har wa yau wani abun da ya kamata a yi la’akari da shi shi ne akwai inuwar hotunan a cikin bidiyon wanda shi ma alama ne na gane bidiyon da aka kirkiro da nufin yaudara.
Daga karshe, DUBAWA ta kuma yi la’akari da cewa babu wata kafar yada labaran da ta dauki labarin. Idan da da gaske shugaba Tinubu ya yi wannan furucin dangane da shirin da dama ya dauki hankali, dole da kafafen yada labarai masu sahihanci sun dauka.
A Karshe
Wannan zargin karya ne. Cikakken nazarin bidiyon ya bayyana cewa bidiyon na bogi ne kawai.