African LanguagesHausa

Me yasa jin zafi ko ciwo ke haifar da fitar maniyi ko inzali ga dan Adam

Getting your Trinity Audio player ready...

Cikakken bayani

Jin zafi da jin sha’awa abubuwa ne guda biyu da dan Adam ke jinsu, sai dai wasu bayanai na nuni da cewa wadannan abubuwa guda biyu basa rasa alaka da juna ko daya na iya sadar da samun daya.

Wani mai amfani da shafin X da aka fi sani da Twitter ya bayyana yadda ya kadu bayan da yaga ya kawo maniyi yana tsaka da yi n aiki mai wahala. Wannan mai aiki da shafin na Twitter mai suna Napaul (@LifeOfNapaul), ya yi amanna cewa jin yanayi na inzali yayin da aikin wahala ya kai wata kololuwa shine abin da dan Adam ke ji.

Wace alaka ke da akwai tsakanin jin zafin ciwo da jin dadi irin na fitar da maniyi?

Wendy Strgar, wanda ke rubutu a mujallar HuffPost, yayi bayanai kan alakar da ke akwai tsakanin jin wahala da yin inzali a daya daga cikin makala da ya rubuta. Ya nunar da cewa yadda ake jin dadi ko akasinsa a tsakanin cinyoyi har yanzu ba a kai ga warwarewa ba, yayin da jin wahala ya ke kaiwa ga fitar da maniyi ko kuma saduwar ta kai ga fitar da maniyyin.

Mr Strgar ya rubuta cewa jin zafi da saduwa da shiga tashin hankali duk wasu abubuwa ne da sinadaran da suke kai wa a same su suna da alaka da juna a jikin dan Adam.

Asalin inda ake samo jin dadin ko wahalar na fitowa ne daga sinadarin halittar  endorphins. Kuma Endorphins wasu kwayoyin halitta ne masu sadar da bayanai da ake samo su daga pituitary gland da hypothalamus, wadanda ke matsawa kwakwalwa sai ta sadar da jin dadi irin na sha’awa.

Wani abun mamakin shine dukkanin jin ciwo ko wahala na jawo Serotonin da melatoni  su rika sakin wani abu zuwa kwakwalwa wacce ke juya wahala ko jin zafi ya zama abin da ke kai mutum ga gamsuwar saduwa.

Haka nan kuma kwayoyin halittar epinephrine da norepinephrine, wadanda kan bayyana yayin da jiki ke jin zafi kan jawo fitar da inzali da kawo jin dadi ko nishadi a lokaci guda. 

Me bincike ke cewa ne kan wannan?

Mujallar kimiya ta The Harvard Gazette ta fitar da bayanai kan yadda masu binciken lafiya a babban asibitin lafiya na Massachusetts General Hospital ya gudanar da bincike ta hanyar amfani da masu aikin sadaukarwa takwas ko ‘yansakai, an bugi ko daki hannunsu sosai yadda suka ji zafi, yayin da ake wannan ana nazartar kwakwalwarsu don ganin yadda tsarin kaikawon kwakwalwa ke aiki.

Jikinsu ya dau zafin da ya kai  106 degrees Fahrenheit kadan ya rage a zafin da duk halittu wadanda ke haihuwa tun daga bera zuwa mutum kan iya ji ko dauka. Wasu kuma zafin da aka ji ya kai 115 degrees a ma’aunin zafi na Fahrenheit zafin da za a ji dau ba tare da ya kona fata ba.

Zafin da ake ji na sadar da bayanai zuwa kwakwalwa wacce ke fitar da wani sinadari na kashe zafi, duk da cewa na faruwa daf da lokacin da ya dace daukar zafi ta faru, bangaren kwakwalwa da ke jawo jin dadin da ake ji yayin cin abinci ko saduwa sai ya dau aiki a wannan lokaci.

Bangaren wannan kwakwalwa shi ake kira da suna  “nucleus accumbens” yafi kusa da kwakwalwa idan aka kwatanta da jijiyoyin da suke hada bangarori na kwakwalwa da ke haifar da jin zafin ko ciwo.

A cewar wani binciken masana a babban asibitin Massachusetts ‘yan halittun na nucleus accumbens na kawo wuta ne “lights up” lokacin da mutane ko dabbobi suka sami kai a yanayi na jin dadi dalilin wani abinci da ganin abin da fuska ke son gani.

A cewar wani bincike na Jami’ar Michigan sinadaran da kan haifar da jin dadi a kwakwalwa dopamine, an alakanta su da jin dadi da rashin jin dadi a jikin dan Adam. Sinadaran na Dopamine, da ke sadar da bayanai cikin kwakwalwa (neurotransmitter),  na da alaka da halayyar dan Adam wacce ke azalzala daukar mataki ko yin wani aiki.

Binciken na su ya gano cewa sinadarin na Dopamine na fara aikin a cikin kwakwalwa lokacin da mutane suka samu kai a yanayi na rashin jin dadi.Wani sakamako da aka gano daga hoton kwakwalwa da aka dauka da yadda jijiyoyin da ke jikinta ke halayyarsu lokacin jin zafi ko rashin dadi ya nunar da cewa kwakwalwar na sakin sinadarin na Dopamine lokacin da mutane ke a yanayi na rashin dadi ko jin zafin ciwo.

Binciken har ila yau ya gano cewa wannan na iya bayuwa ga halayyar dan Adam na shan magunguna lokacin da suke jin matsi, shi yasa ake ganin wasu daidaikun mutane na nacewa shan wani maganin wata cuta da tayi masu mugun kamu. Shi yasa ake ganin banbanci na yadda wasu ke mu’amalantar kwayoyi ba wai dalilin gado ba ko sa kai ba.

Me kwararru ke cewa?

Jon-Kar Zubieta, Farfesa a fannin ilimin sanin kwakwalwa da ilimin daukar hoton sassan jikin dan Adam a kwalejin ilimin aikin likita ta Jami’ar Michigan ya ce sinadarin dopamine shike hadewa tsakanin matsi da ciwo da shauki da wani aiki da ake da kwakwalwa da ma na jiki wadanda ke haifar da samun abu mai dadi ko mara dadi.

Mista Zubieta yace dopamine “na dabi’antuwa da mayar da martani ga abubuwan da hankali bai kai kansu ba cikin sirri , abu ne mai muhimmanci ga daidaikun mutane  ga yadda yake aiki a jikinsu.”

Wani bincike da aka yi kan mutane 25 maza da mata ya gano bangaren kwakwalwar da sinadarin na dopamine kan shafa ana kiransa da suna “basal gangalia.” Kuma abin sha’awa shine wannan bangare ne kuma ke mayar da martani lokacin abin da ake so kamar jima’i ko cin abinci .

A wata gabar lokacin da aka yi wa wadanda ake binciken akansu alurar sinadarin an ga yadda suka rika nuna halaya mabanbanta a bangaren na basal gangalia. A cewar bincike idan mutum ya kara fahimtar cewa yawan sinadaran da aka sa masa da zai haifar da fargaba da matsi yawan dopomine da za a gani a yankin na “nucleus accumbens” shine kuma irin abin da ake samu a bangaren kwakwalwa da ya saba da shan wani magani ba kakkautawa.

Muhimmin abu kenan da aka gano a bangaren kwakwalwar ko da lokacin da masu binciken suka soka allurar a naman kwanjin mukamumi don ganin tasirinsu.

Masu binciken sun gano cewa a yankin na basal gangalia, dopamine shi ake amfani da shi a ga yanayi na zafi ko rashin jin dadi da aka samu, haka nan kuma nucleus accumbens, yana da alaka da yawan shauki da aka samu lokacin jin zafin ko ciwon. 

Kwarraren masani kan halayyar jikin dan Adam kuma masanin kimiyar wasanni Ian Gillam (MD) yace endophins da ke sa mutum ya ji dadi “feel good”sun fi tasiri kan morphine” idan aka sanya shi da yawa. Endorphins na fin yawan aiki ne lokacin da aka shiga aiki na zahiri da jiki ko yin wani atisaye mai yawa saboda suna warware gajiya da sanya jin nishadi.

Yayin zantawa da mujallar New York Post, Mista Gillam 

Ya ce sinadarin endorphins na sauka bayan lokaci mai tsawo na yin atisaye, yace idan aka dauki kimanin mintuna 45 ana atisaye na jawo samar da sinadarin na endorphin ga jikin dan Adam.

Mutane na iya ci gaba da yin atisaye zuwa wani lokaci mai tsawo don su sami sinadarin na endorphins a jikinsu, idan akwai wadannan siunadarai a jikin na dan Adam cikin rashin sani zai ji ya samu kai a yanayi na takura ko matsi a lokacin da mutum ke ci gaba.

Wannan dabi’a kusan irinta ce idan mutum ya shiga mu’amala ta saduwa zai rika jin wasu abubuwa daban-daban da yake so ya kai gare su , wadannan abubuwa kuwa sun hadar da son ya ji zafi ko ciwo ““feel” pain.”

A dai wannan wallafa ta New York Post, masaniya kan halayyar jima’i  mai kuma ba da shawarwari ga ma’aurata Jacqueline Hellyer tace aikata saduwa cikin hanzari kamar karya gwatso, tamkar mutum ne da ya fita gudu. Abin da take nufi har sai mutum yaji a jikinsa cewa ya wartsake “invigorated.”.

Miss Hellyer ta kara da cewa kaguwa ta gano ko ana jin zafi ko kokarin ganin kai wa ga jin dadin lokacin na yin jima’i ko saduwa. 

Ga bangaren masu son samawa kai gamsuwa ta jin zafin, mutane kan ji wa jikinsu ta yadda za su cire shaukin da basa bukata,a cewar masaniyar halayyar kwakwalwa (according to psychologist Georgia Ray) ta yi amanna cewa mutane na jiwa kansu ciwo don kawai su ji su wasai. Wasu kuma na yi saboda wasu al’amura na zamantakewa don su samu tallafin zamantakewar. 

Wadanda kan jiwa kansu ciwon daga bisani sukan ji cewa sun gamsu sun samu nutsuwa a zukatansu.

A Karshe

Yayin da mutum ya shiga yanayi na matsi saboda yadda yake motsa jiki kamar na tafiya wannan na jawo sanadi na fitar da wasu sinadarai da ka iya haifar da samun jin dadi na gamsuwa.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »