African LanguagesHausa

Ministar kudin Najeriya karya ta yi da ce harajin kayayyakin masarufi na VAT a Najeriya shi ne mafi karanci a duniya.

Zargi: Ministar kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed kwanan nan ta yi zargin cewa harajin kayayyakin masarufi na VAT a Najeriya da ke kan kashi 7.5 cikin 100 shi ne mafi karanci a duniya.

Sakamakon bincike: Karya! Akalla kasashe uku daga cikin wadanda muka tantance na da harajin na VAT kasa da abun da ake biya a Najeriya.

Cikakken Bayani

Yayin da Najeriya ke fama da hauhawan farashin shugabancin kasar, da karancin kudaden shiga, gwamnatin kasar na cigaba da neman hanyoyin samun kudaden shiga. Daya daga cikin wadannan hanyoyin ita ce harajin kayayyakin masarufi na VAT.

Kwanan nan, ministar kudin kasar, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, yayin da ta ke ziyara a tashar yada labarai na kasa da kasa ta Najeriya wato Muryar Najeriya, ta bayyana cewa Najeriya za ta iya samun karin kudi yanzu daga kudaden da take caza na VAT a kan kashi 7.5 zuwa 10 cikin 100.

Domin karfafa matsayarta, ministar cewa ta yi “VAT na daya daga cikin hanyoyin habaka yawan kudaden shiga kuma zamu kara VAT tunda a kashi 7.5 cikin 100 Najeriya ce ke da mafi karancin kudin da ake caza a duniya, ba Afirka ba, a duniya baki daya.”

Mene ne VAT? 

VAT haraji ne na kayayyakin da ake amfani da su wanda ake karawa kan farashin kayayyaki da ayyuka. A kan biya su ne sadda ake sayen kayayyakin ko biyan kudin aiki. Mai sayen kayayyakin ko neman a yi masa aikin ne ke da nauyin biyan kudin.

Abun da aka kaddamar da shi a Najeriya a shekarar 1993 dan ya maye gurbin harajin da ake samu kan kayayyakin da aka saida, amfanin VAT na cigaba da fadada musamman a airin gudunmawar da ya ke bayarwa ga kudaden da shiga Najeriya, abun da ake kiyasin ya kai N triliyan 1.2 a watanni shidan farko na shekarar 2022. 

VAT babbar hanya ce da gwamnatocin kasashen duniya ke samun kudaden shiga kuma suna bukatar masu sana’o’i su rika ajiye cikakkun bayanai na saye da sayarwarsu.

Babban mukamin gwamnatin da ministan ke rike da shi, da irin ikon da take da shi wajen yanke shawarwarin da za su yi tasiri sosai a rayuwar jama’a ya sa DUBAWA tantance gaskiyar wannan bayanin na malama Zainab Ahmed.

Tantancewa

Domin tantance zargin ministan, DUBAWA ta fara da duba shafin “tax summaries” wato takaitattun bayanan haraji – wanda shafi ne da daya daga cikin manyan kamfanonin kudin duniya suka girka, wato PricewaterhouseCoopers, ko PWC. 

Shafin na da cikakken jaddawalin kudaden harajin kayayyaki na VAT din da ake amfani da su a kasashe daban-daban.

Akalla kasashe uku – Thailand, Hadaddiyar Daular Larabawa da Oman – wadanda ke kan shafin na da kudin harajin VAT din da ke kasa da na Najeriya wanda ke zaman kashi 7.5 cikin 100 a shekarar 2023.

Domin sake tabbatar da sahihancin bayanan da ke shafin. DUBAWA ta sake shiga shafukan gwamnatoci wadanda ke bayanai kan kudi. 

A shafin kasar Thailand VAT na kan kashi 7 cikin 100. Bacin haka bayanin da ke shafin ma’akatar kudin Hadaddiyar Daular Larabawa VAT wanda aka gabatar a kasar a shekarar 2018 na kan kashi 5 cikin 100. Haka nan kuma, a babi na 5  sashi na 35 na dokar VAT a kasar Oman wanda ake iya gani a shafin Hukumar Kula da Haraji VAT na kan kashi 5 cikin 100 wanda bai kai na Najeriyar da ke zaman kashi 7.5 cikin 100 ba.

A Karshe

Binciken DUBAWA da kuma shafukan gwamnatocin kasashe uku sun nuna mana cewa kasashen Oman (5/100) Thailand (7/100) da Hadaddiyar Daular Larabawa (5/100) duk ba su kai Najeriya ba da  kudaden VAT (7.5/100)

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button