African LanguagesHausa

Ngige bai hana APC bukin nasarar cin zaben shugaban kasa ba

Zargi: Tsohon gwamnan Anambra, kuma ministan kwadago yanzu, Chris Ngige ya shawarci jam’iyyar APC kada ta yi murnar nasarar da ta yi a zaben shugaban kasa saboda tarhin da yake da shi da na zuwa kotu da Peter Obi kan zabe

Sakamakon bincike: Karya! Mai magana a madadin Ngige ya karyata wannan zargin ya ce Ngige bai bata yin wani bayani makamancin wannan ba

Cikakken bayani

Al’ummar Najeriya na cigaba da mayar da martani tun bayan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta INEC ta sanar da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu

Wadansu daga cikin martanonin gaskiya ne kamar a wadannan shafukan, wato a nan, nan da nan. Wasu lokuta kuma duka zargi ne kawai kuma babu gaskiya cikin barun, kamar a nan, nan da nan  

Daya daga cikin irin wadannan zarge-zarge shi ne wani labarin da Gabriel Chima (@gabrielchimam) ya wallafa a shafin Twitter ranar 21 ga watan Maris  2023. Mr Chima ya yi zargin cewa Ministan kwadago, Chris Ngige ya ce ya fadawa jam’iyyar APC ka da ta yi murnar nasarar da aka ce ta yi a zaben shugaban kasa tukuna, bisa tarihin da ya ke da shi na ziwa kotu da Peter Obi.

Shafin ya yi amfani da hoton Mr Ngige yayin da ya ke hira da manema labarai dan kar bai wa labarin nagarta. “Na fadawa APC ka da ta yi murnar sakamakon zaben shugaban kasa tukuna domin ni kadai na san abin da na gani a wajen Peter Obi lokacin da muka je kotu,” aka ambato ministan kwadagon na cewa.

Idan ba’a manta ba, bayan da INEC ta sanar da Mr Ngige a matsayin wanda ya yi nasarar zaben gwamna a jihar Anambra a zaben gwamnonin da aka yi ranar 19 ga watan Afrilun 2003, lokacin Ngigen na jam’iyyar PDP, Mr Obi, wanda ya yi takara a zaben ya kalubalanci sakamakon a kotu wanda shi kuma a wancan lokacin ya yi takara a inuwar jam’iyyar APGA. 

Ranar 17 ga watan Maris na shekarar 2006 ya sake karbar mukamin gwamnan, bayan da kotun daukaka kara ta yanke hukuncin cewa Mr Obi ya yi nasara a zaben 19 ga watan Afrilun 2003. Ana iya samun cikakken bayani dangane da gwagwarmayar da ‘yan siyasan biyu suka yi a kotu cikin wannan rahoton  da Premium Times ta hada. 

A ranar 22 ga watan Maris 2023 kawar sakon @gabrielchimam ya dauki hankalin jama’a inda mutane 3,000 sun yi ma’amala da shafin. To dai dai wasu daga cikin wadanda suka yi tsokaci a shafin sun bayyana rashin yardarsu da batun. Wannan tababan da muka ga wasu na yi a shafin Twittern ne ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar batun.

Tantancewa

Mun yi binciken mahimman kalmomi inda muka so mu ga ko sauran kafofin yada labarai masu nagarta sun dauki labarin. Mun kuma dauki furucin da ake zargi Ngigen ya yi muka kwatanta da sauran shafukan sada zumunta da na labarai nan ma ba mu ga komai ba.

Daga nan ne ma muka gano cewa Mr Ngige ba shi da shafin kansa a manhajojin Twitter da Facebook.

DUBAWA sai ta tuntubi mai magana da yawun ministan, Emmanuel Nzomiwu, ta layinsa ta WhatsApp, wanda ya karyata zargin. Mr Nsomiwu ya kuma kara tabbatar mana ta wayar tarho cewa lallai Mr Ngige ba ya shiga soshiyal mediya. 

“Labarin bogi. Ku yi watsi da shi. Nagode da kuka tuntube ni,” Mr Nzomiwu ya ce.

A Karshe

Bincikenmu da sakon da muka samu daga mai magana da yawun Chris Ngige, Emmanuel Nzomiwu ya buna mana cewa furucin da ake dangantawa da Mr. Ngige ba gaskiya ba ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button