African LanguagesHausa

Hoton yaron da aka ce ya kashe kan shi ba shi da alaka da zabukan 2023

Zargi: Wani mai amfani da shafin Twitter ya yi zargin cewa wani yaro da kashe kan shi ta hanyar rataya ya yi haka ne saboda Bola Tinubu ya kayar da  Peter Obi a zaben shugaban kasa.

Hoton yaron da aka ce ya kashe kan shi ba shi da alaka da zabukan 2023

Sakamakon Binciken: Karya. Wannan hoton yana shafukan intanet tun kafin zabe

Cikakken bayani

Hoton wani matashi wanda ya kashe kansa ya bulla a shafukan soshiyal mediya tare da labari mai sosa rai. Wani mai shafin da ya kira Peter Obi’s Kidney (Wato kodar Peter Obi (@Dalapflourish) ya wallafa hoton yana zargin wai yaron ya dauki ransa saboda ya kasa lamuntar yadda Bola Tinubu ya yi nasara kan Peter Obi a zabukan 2023 wadanda aka kammala kwanan nan. 

Mai amfani da shafin na Twitter ya yi labarin rayuwar matashin yayin da yake bayyana dalilin mutuwarsa a matsayin rashin kyakyawar makomar da hangar wa Najeriya bayan da Mr. Obi ya sha kaye a zaben.

“*LABARI MAI BAN TAUSAYI:” Ya rubutaHe tweeted, “Zan fada wa ubangiji cewa INEC ce ta kashe ni. Wani matashi daga jihar Filato ya kashe kansa bayan da Obi ya rasa zaben da aka yi magudi. Yaron mai shekaru 19 na haihuwa ya bar ‘yar gajeruwar wasika mai cewa – babu kyakyawar fata wa Najeriya a shekaru 20 masu zuwa tunda Obi bai ci zabe ba.” 

Labarin ya janyo ra’ayoyi mabanbanta a kan dandalin. Misali, (@Mrbalance13), 

Wanda ya yi imanin cewa labarin gaskiya ne, ya bayyana takaicinsa dangane da batun. “Labari mai ban tausayi,” ya rubuta. Wani shi ma mai suna Bernard Clifford Asoka (@AsikaClifford), ya yi tsokaci mai cewa, “Ya ubangiji ka yi mana jinkai.”

Wasu kuwa, kai tsaye suka ce labarin ba gaskiya ba ne. Samsonyte (@ogbebor_samson) na daya daga cikin su. Ya ce, “wannan ba gaskiya ba ne, dan Allah.”

A daidai lokacin da muke hada wannan rahoton mutane sun ga labarin sau 8,947 wsau 70 sun latsa alamar nuna amince na likes, 58 sun sake labarin  a yayin da wasu 10 suka yi amfani da shi cikin tsokacinsu a shafin. 

Irin sosa ran da wannan labarin ke da shi da yiwuwar yaduwa cikin sauri ta yadda zai yaudari jama’a ne ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tantance labarin dan kada a sami matsala nan gaba. 

Tantancewa 

DUBAWA ta fara da binciken hoton a google dan gano inda ya fara bulla da labarin da ya fita tare da hoton a lokacin da ya fito. Sakamakon binciken ya nuna cewa a shekarar 2016 wannan hoton ya fara bulla a duniyar gizo

Wata taska ta blog, mai suna Talk Glitz Media, ranar 26 ga watan Disemban 2016 ta yi wani labari da hoton matashin da ake zargi a ciki tare da kan labarin da ke cewa “Wani dan Yahoo ya kashe kansa a Warri”

Duk da cewa DUBAWA ba za ta iya tantance gaskiyar rahotannin da ke cikin wadannan taskokin blog din ba, labarin ya bamu tabbacin cewa hoton na kan shafukan yanar gizo tun 2016.

Jihar Filato (inda ake zargi lamarin ya faru) ‘yansanda sun karyata labarin cewa wani ya kashe kan shi sakamakon zaben shugaban kasa. DSP Alabi Alfred jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar ya fadawa ‘yan jarida cewa zargin karya ne kuma ba shi da tushe bacin haka yana iya haddasa tashe-tashen hankula a cikin jihar.

Mr Alfred ya kuma kara da cewa sun tuntubi duka hdikwatocin ‘yansandan da ke yankunan jihar kuma kowannensu ya tabbatar ba su sami wani rahoto haka ba.

“Domin tantance gaskiyar batun, ofishinmu ya tuntubi duka ofisoshin ‘yan sandan da ke jihar, kuma babu wani wanda ya kai irin wannan karar zuwa ofishin ‘yan sandan da ke jihar,” jami’in hulda da jama’an ya bayyana

A karshe

Wannan labarin ba gaskuya ba ne. Tun shekarar 2016 hoton ke yawo a kafafen sadarwa da labarai na yanar gizo. Ofishin ‘yan sandan jihar Filato, jihar da ake zargi lamafin ya faru, ya fito ya karyata labarin.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button