Connect with us

Hausa

NPHDA za ta dauki ma’aikata na musamman domin kaddamar da shirim samar da allurar rigakafi a kasa baki daya

2 mins read

Zargi: wata sanarwa na zargin cewa Hukumar Lafiya ta kasa (NPHCDA) tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi masu zaman kansu za su dauki matakan karfafa bayar da allurar rigakafin COVID-19 a kasar baki daya. 

Wata sanarwar da ake yadawa a shafukan soshiyal mediya na zargin wai Hukumar Lafiya ta Kasa (NPHCDA) tare da hadin kan wadansu kungiyoyin da take kawance da su za su kaddamar da wani shirin rigakafin COVID-19 a duk fadin kasar.

Sakon ya ce duk ‘yan Najeriyan da suka cancanta na damar neman aikin, ko a matsayin masu allura, ko masu daukan bayanan jama’a ko kuma masu tabbatarwa, wato wadanda suke da kwarewa a fannin kiown lafiya kuma sun iya bayar da allura.

Sakon ya kara da cewa za’a dauki wadanda suke da akalla karatun sakandare kuma cikin su wadanda suka yi allurar COVID-19 ko da guda daya ne za’a fara zaba.

An yada wannan labarin a WhatsApp kuma da yawa na shakkun sahihancin labarin, har ma wani mai amfani da shafin ya yi tsokaci kamar haka, “Ku daina sanya irin wannan bayannan a nan. Ba gaskiya ba ne, Ku na so sai mun fada mu ku ne?”

Ba wannan ne karon farko da Dubawa ke karyata zargi irin wannan ba, wato sanarwar da ke zargin wai gwamnati na neman ma’aikata. Lokacin COVID-19 na kololuwarta bayan an sanya dokar hana fita a 2020, irin wadannan batutuwan sun yi sanadiyyar fadawar jama’a da dama cikin tarkon masu yaudara. Shi ya sa Dubawa ta dauki nauyin tantance wannan labarin

Tatanacewa 

Lokacin da Dubawa ta tuntubi jami’in sadarwar NPHCDA, Muhammad Onitoto ya tabbatar mana cewa sanarwar na neman ma’aikata gaskiya ne. Ya ce: “Gaskiya ne. NPHCDA ta shirya ta gudanar da gangami na allurar rigakafi. Duk wanda ya cancanta zai sami wannan dama,” a cewar Mr. Onitoto da muka zanta da shi ta wayar tarho.

Sanarwar na kan shafin NPHCA kuma tana kira ga duk wadanda suka cancanta da su sa takardar nuna sha’awa.

A Karshe

Zargin wai NPHCA tare da hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu na neman ma’aikata dan kaddamar da allurar rigakafi a kasa baki daya gaskiya ne.

Click to comment

Leave a Reply

More in Hausa