African LanguagesHausa

Obama bai bayyana tutar yakin neman zaben Rochas Okorocha na zaben 2023 ba

Wani mai amfani da shafin Tiwita na zargin wai tsohon shugaban kasar Amirka Barack Obama ya bayyana tutar yakin neman zaben Rochas Okorocha domin nuna goyon bayan sa

Wani bidiyo da ke zagaya a WhatsApp na zargin wai tsohon shugaban kasar Amirka Barack Obama ya bayyana tutar yakin neman zaben dan siyasar Najeriya Rochas Okorocha a zabukan kasar da ke tafe a shekarar 2023 domin nuna goyon bayan sa.

Bidiyon mai tsawon dakiku 30 ya nuna Obama da mai dakinsa Michelle suna zaune a wani abin da ya yi kama da taro. Daga nan sai aka gayyaci tsohon shugaban da ya je gaban jama’a ya gabatar da wani hotona musamman da aka yi da yakin neman zaben na Rochas Okorocha.

Rochas Okorocha sanata ne da ke wakiltar mazabar yamma na jihar Imo a majalisar dattijai na tara. Ya kuma taba kasancewa gwamnan jihar Imo, sa’anan ya dade yana takarar neman shugabancin kasar.

Duk da cewa mun gaza gano tushen bidiyon. Shafin yakin neman zaben Okorocha na dauke da hoton da ake zargi Obaman ya bayyana  bidiyon. Masu amfani da WhatsApp da yawa sun musanta sahihancin wannan bidiyon. “An yi editing ne. Obama bai ma san Rochas ba,” a cewar wani mai amfani da WhatsApp.

Jama’a sun yi ta tambayoyi makamantan wannan amma a takaice dai abu daya suke so su sani: wai shin Obama ya bayyana tutar yakin neman zaben Rochas domin ya nuna goyon bayan shi?

Tantancewa

DUBAWA ta gano cewa an gyara bidiyon ne domin ya je daidai da labarin da ake so a bayar. Da gaske ne Obama ya halarci taron da ya bude wani hoto, a binciken da muka yi cikin manhjan tantance hotunan bidiyo na InVid mun gano cewa an dauki hoton Okorocha ne an dora a kan zanen hoton Obama da aka gabatar masa a shekarar 2018 a cibiyar gidan tarihin Smithsonian.

Ainihin taron da aka yi yana kan shafin YouTube din cibiyar Smithsonian tare da wannan bayanin:

“Gidan tarihin hotuna na kasa, Smithsonian na gabatar da hotunan Barack Obama da Mrs. Michelle Obama wadanda masu zane Kehinde Wiley da Amy Sherald suka zana. Masu jawabi sun hada da Tsohon shugaba Barack Obama, Mrs. Obama, sakataren Smithsonian David Skorton, darektan Smithsonian Kim Sajet da masz zanen Wiley da Sherald.

A karshe

Bidiyon da ake zargi wai Obama ne ke nuna goyon bayansa ga takarar Rochas Okorocha a 2023 na bogi ne. An gyara hotunan ne kuma ainihin abin da ke faruwa a bidiyon ba shi da wata alaka da burin siyasar Okorocha

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button