Zargi: Wani sako a shafin tiwita na zargin wai an gano hanyar warkar da masu fama da kwayar cutar HIV ta hanyar amfani da sabuwar fasahar dasa kwayoyin halittan da aka sarrafa a dakin gwaji/kwalba
Gargadi: Babu maganin warkar da cutar HIV kuma wannan dabarar ta dasa kwayoyin halitta daga CCR5 yunkuri ne da ke hasashen samar da kyakyawar makoma ba wai an sami amsa takamaimai ba. Dan haka wannan ikirari yaudara ce kawai.
Kwayar cutar HIV ya kan janyo ciwon da ke lahani ga kwayoyin jinin da ake kira CD4 cells a turance wadanda dama su ne ke yaki da cututtuka a jikin dan adam su kuma ingantan garkuwar jiki.
A shekarar 2020 ana kiyasin cewa mutane sama da milliyan 37 ke rayuwa da HIV kuma kwayar cutar na cigaba da kasancewa karfen kafa ga lafiyar jama’a ko’ina a duniya tunda kawo yanzu mutane sama da milliyan 36 suka hallaka a dalilin cutar.
Wani mai amfani da shafin Tiwita mai suna Pride(@masi_nonxuba) na zargin wai mutane uku sun warke daga cutar, bayan da suka yi amfani da sabon salon na dashen kawyoyin halittan.
An dade ana neman maganin da zai kawar da wannan cutar daga doron kasa, shi ya sa tantance gaskiyar wannan labarin ke da mahimmanci.
Tantancewa
Wannan sako da aka wallafa ranar alhamis 17 ga watan Fabrairu ya dauki hankali sosai. Sai dai duk da haka mutane sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta wajen yin tsokaci. Misali, wani mai amfani da shafin mai suna Mr Closet (@Reeuq11) ya ce ana dai kan hanyan samun magani amma ba’a riga an kai ga yin hakan ba.
Wani mai amfani da shafin kuma tambaya ya yi ko akwai rahoton da ya nuna hujja. Sai wanda ya wallafa labarin ya amsa da adireshin shafin news24.com mai dauke da labarin da kamfanin dillancin labaran Reuters ya rubuta, mai taken “macen da ta fara warkewa daga HIV bayan da aka yi mata dashen bargo.”
A cewar rahoton wanda aka wallafa ranar 16 ga watan Fabrairu, batun wani bangare ne na babban binciken da ke samun goyon bayan Amirka, a karkashin jagorancin Dr. Yvonne Bryson daga jami’ar Carlifonia Los Angeles (UCLA) da Dr Deborah Persaud na jami’ar John Hopkins da ke Baltimore.
Da muka yi binciken mahimman kalmomi mun ga cewa kafofin yada labarai da dama sun dauki labarin. Kafofi irinsu BBC, New York Times, Muryar Amirka, Reuters Aljazeera da Sauransu.
Da muka yi bincike kan rahotannin mun gano cewa wata mace mai shekaru 64 na haihuwa wadda ake wa maganin cutar sankarar bargo ta warke daga HIV. Hakan ya faru ne bayan da aka dasa mata wasu kwayoyin halitta na musamman. A yanzu haka matar ta cika watanni 14 ba tare da kwayar cutar ta HIV ba.
Wannan matar ce mutun na uku da ke samun waraka daga cutar. Sauran mutane biyun farko maza ne (Timothy Ray Brown da Adam Castillejo)
Timothy Ray Brown wani mazaunin Berlin shi ne ya kasance mutumin farko wajen cin moriyar wannan sabon fasahar. A shekarar 2007 aka dasa mi shi bargon sakamakon sankarar da yake fama da ita. Wanda ya ba shi kyautan bargon ya na dauke da wata kwayar halitta a jinin shi mai suna CCR5 wanda ba safai ake ganin irin ta ba. CCR5 kwayar halitta ce da ke hana mai shi kamuwa da cutar HIV ko da kuwa me aka yi.
A shekarar 2020, Castillejo wani mazaunin Landan shi ma mai fama da cutar HIV ya kasance mutun na biyu da ya sami waraka sakamakon dashen bargon da aka yi mi shi a dalilin sankarar da ya ke da shi.
Ko da shi ke, a na sa dashen an yi amfani da jinin da ke igiyar cibiya ne wanda aka ce yana da hadari kuma bai da ce a yi amfani da shi a kan wadanda ke dauke da kwayar cutar HIV ba.
Mene ne kwayar halittar CCR5?
Daga rahoton mutun farkon da ya sami waraka mun ga cewa ya sami jini ne daga wani wanda ke da kwayar halittar CCR5 wanda ba safai ake samu a jikin dan adam ba.
Me wannan ke nufi?
A shekarar 1996, masu bincike sun gano cewa CCR5 yana iya juya kafar da HIV ke amfani da shi ta shiga jinin mutun daga farkon kamuwa da cutar kuma wadanda su ke da irin wanann kwayoyin halittan guda biyu (wanda ake kira allele a turance) ba su da irin wannan kafar dan haka kwayar cutar ba za ta iya mu su lahani ba.
An sami irin wadannan kwayoyin halittan a jikin wadanda suka yi ma’amala da cutar ba tare da sun kama ba. Dan haka ne ake ganin cewa wanann wata dama ce ta samu a cigaba da neman maganin cutar da ake yi.
Me Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ke cewa?
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce babu wani maganin da ke warkar da HIV. Mai dauke da cutar zai iya daidaita kiwon lafiyarsa ta hanyar kula da kai da shan magungunan ARV kala biyu zuwa uku.
“Magungunan da muke da su (ART) bas u warkar da cutar HIV suna takaita yaduwar kwayoyin cutar ne kawai a cikin jinni ta yadda garkuwar jikin mutun za ta iya inganta kanta ta sami karfin yaki da cututtuka masu hatsari …..” a cewar daya daga cikin daftarorin aikin WHO.
Tun shekarar 2016 WHO ta ba da shawarar cewa a baiwa duk masu fama da HIV magungunan da za su yi amfani da su na tsawon rayuwarsu. Wannan ya hada da kananan yara, matasa, manya maza da mata, mata masu juna biyu da shayarwa, ba tare da yin la’akari da yanayi ko yawan ciwon da ke jikinsu ba.
A watan Yunin 2021 kasashe 181 sun dauki wannan shawarar kuma kashi 99 cikin 100 na duk wadanda ke fama da cutar a duniya na cin moriyar tallafin magungunan.
Duk da cewa an dade ana neman hanyar shawo kan cutar, babu wata hujjar da ta nuna cewa an yi nasarar yin hakan. Tun shekarar 2007 ake amfani da salon da marubucin tiwitan ya wallafa, kuma mutane ukun da suka warke an yi amfani da salon dashen ne dan cutar dajin da suke dauke da shi, sai maganin ya kawar musu da cutar HIV amma ba HIV din ake da burin warkarwa ba, kuma salon na da hadarin gaske ba kowa ne zai sami nasara ba.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce har yanzu dai babu maganin HIV kuma dabarar amfani da CCR5 ba’a riga an gama bincikenta ba.