African LanguagesHausa

Gwamnatin Najeriya ba ta da niyyar kara albashin masu yi wa kasa hidima zuwa nera dubu arbain da biyar kowane wata

Zargi: Bayanai a shafukan soshiyal mediya irinsu Facebook da Tiwita na zargin wai gwamnatin tarayyar Najeriya za ta kara albashin ‘yan NYSC daga nera 33,000 zuwa 45,000

A shafukan soshiyal mediya musamman facebook da Tiwita, da yawa daga cikin masu amfani da su na cewa wai gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin kara yawan albashin masu yi ma kasa hidima daga nera dubu talatin da uku zuwa dubu arba’in da biyar. Kwanan nan ne aka fara yada wannan jita-jitan bayan da aka yi jinkirin biyan su albashin watan Janairun 2022.

A shafin facebook an yada batun sau da yawa ana amfani da kanun labarai masu daukar hankali. Misali “Gwanatin Najeriya na shirin kara albashin masu yin NYSC zuwa nera dubu 45. Masu yi wa kasa hidima, a wannan karon, kuna iya kara yawan kudin ajiya.”

A shafin Tiwita kuma batun tayar da mahawara ya yi. Mutane da yawa sun yi maraba da batun karin albashin har mu sun yayata.

Duk da cewwa a shekarar 2020 ne gwanati ta kara albashin masu yi wa kasa hidiman daga nera 18,00 zuwa 33,000, daga cikin masu yayata labarin babu wanda ya ambaci majiyarsa. Bacin rashin hujjar mutane da yawa sun yi ta tsokaci dangane da batun abin da ya nuna cewa sun yarda da labarin. 

Hasali ma yawancin mutane sun yi tunanin dabara ce irin ta ‘yan siyasa saboda karatowan zaben shugaban kasa na 2023.

A wani yunkuri na sassanta tsakanin ‘yan kasa da sake gina kasar bayan yakin basasa ne gwamnatin Najeriya ta kirkiro shirin NYSC a 1973

A cewar wani rahoton jaridar Premium Times, a shekarar 2011 gwamnatin Najeriya ta kara albashin NYSC daga nera 9,775 zuwa 19,800. Sai dai sakamakon sabon karin mafi karancin albashin da aka yi a kasa baki daya dole aka sake karawa da nera 19,800 zuwa 33,000 a shekarar 2020.

Ba da dadewa ba DUBAWA ta yi binciken da ya karyata wani zargin da aka gani a WhatsApp wanda ke zargin wai an dakatar da albashin ‘yan NYSC daga watan Janairun 2022 har zuwa wani lokaci da za’a tantance nan gaba.

Tantancewa

Abu na farko da DUBAWA ta fara la’akari da shi shi ne a duk inda aka yi wannan zargi (shafukan Facebok da Tiwita) babu majiya. Duk masu zargin basu yi bayanin mafarin labarin ba, sai dai kawai aka ga batun a sohsiyal mediya.

DUBAWA ma ta tambayi daya daga cikin wadanda ke yayata bayanan wata mai suna Precious Umezinwa amma ba ta bayar da amsa mai gamsarwa ba sai dai ta kada baki ta ce “gaskiya ne ba su dai fara aiwatarwa ba ne”, Sauran wadanda muka tambaya kuma ba su ma kula mu ba. Wannan rashin amsa ya nuna man cewa yawancin mutane sun yada ne kawai yadda suka sami labarin, kuma sau da yawa irin hakan ne ke janyo rashin fahimta.

Mun kuma yi la’akari da cewa labari irin wannan tabbas jaridu za su dauka amma da muka yi bincike ba mu ga labarin a kafafen yada labarai ba.

Daga nan mun tuntubi mataimakin darektan NYSC a fanin yada labarai da hulda da jama’a Emeka Rems Mgbemena har way au dan tantance batun. Ya amsa mu da gajeren sakon da ya karyata zargin mai cewa “Dan uwa na ba gaskiya ba ne.”

A Karshe

Zargin wai gwamnatin Najeriya na shirin kara albashin masi NYSC daga nera 33,00 zuwa 45,000 ba gaskiya ba

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button