Getting your Trinity Audio player ready...
|
Kasar Saliyo ta kasance a fargaba a ranar Lahadi 26 ga watan Nuwamba, bayan wani farmaki da aka kai da yayi sanadin tserewar wadanda ake tsare da su a gidan kaso. Wani gungun mutane ne dai ya kai farmakin a wurin ajiye makamai na barikin Wilberforce(Wilberforce Barrack) kana daga bisani suka kai farmakin a shelkwatar sojoji da ke Cockerill da wurin ajiye kayan makaman sojoji da ke garin Murray da gidan kaso
Wannan lamari ya haifar da cece-kuce. Akalla kwanaki biyu bayan aukuwar lamarin gwamnatin kasar ta Saliyo ta kira taron manema labarai inda ta yi wa al’umma bayani kan abin da ya faru bayan harin da aka kai a ranar 26 ga watan na Nuwamba. Kuma cikin mahalarta taron manema labaran sun hadar da shugaban rundunar soja ta kasar da sifeto janar na ‘yansanda da shugaban hukumar da ke lura da gidajen kaso na kasar.
Abin da muka sani kawo yanzu
Harin da aka kai a ranar Lahadi a hukumance an bayyana shi a matsayin yunkurin juyin mulki.”Muna gudanar da bincike kan yunkurin juyin mulki da ya gaza nasara.” A cewar Sifeto Janar na ‘yansandan kasar William Fayia Sellu. Da yake bayani kan abin da ya faru a ranar ta Lahadi Mista Sellu ya ce “Wani gungun mutane da ba a san ko su waye ba sun yi yunkurin kifar da halastacciyar gwamnati ta hanyar yi wa dokar kasa karantsaye.”
Gwamnati dai na taka tsantsan kan kalaman da take furtawa kan abin da ya farun ranar Lahadi. Ministan yada labarai Mohamed C. Bah, a yayin tattaunawa da kafar yada labarai ta BBC (BBC interview) ya ce jami’an tsaro za su ba da bayanan girman batun na juyin mulki.
Da yake magana kan batun wajen ajiyar makaman shugaban sojan ya ce “yace ba mu da na’urar CCTV, dole na fadi haka, wannan shine darasin da muka koya.”
Shugaban rundunar sojojin ya amince cewa lokacin farmakin an yi awon gaba da tarin makamai sai dai bai ba da cikakken bayani ba. Da yake amsa tambayar ‘yanjarida sai ya ce har zuwa (1:04:00 – 1:05:05) “Ba zan iya fada maku takamaimai adadin ba, amma da zarar, mun kammala bincike za mu ba da bayanai. ”
Wannan martani na shugaban ‘yansandan na zuwa ne kwanaki bayan kai farmaki rumbun ajiyar makaman. Shi kuwa ministan harkokin yada labarai ya kara da cewa. “Abu mafi kyau shine sojoji sun bayyana gaskiya kan wannan lamari, ba za su baku bayanai da babu sahihanci a cikinsu ba.”
“Har yanzu muna kan batun, jiya ma mun gudanar da wani aiki inda muka kori masu farmakin, Mun je Orugu mun kuma kwato motoci biyu da makamai da alburusai wadanda aka gudu da su. Mun kuma kwato bindigogi samfurin RPGs uku, da bama-bamai shida da bindiga samfurin AK47 guda 15.” A cewar shugaban rundunar sojan Peter Lavahun.
Wannan sake maido da makamai dai ya sake nunawa karara irin koma bayan tsaro da ke akwai a Wilberforce.
Fasa Gidan Kaso
Gidan kaso na maza wanda aka fi sani da suna Pademba Road Prison, shine mafi girma a kasar. Col. Sheik Sulaiman Massaquoi yace a ranar da aka kai farmakin suna da mutanen da aka tsare 1,919, sai dai akwai wasu da ake tsare da su a wasu wuraren wanda bai wuce kewayen mil guda ba.
Cibiyar gyara hali ta mata da cibiyar gyara hali ta maza sun kasance wurare biyu daga cikin wuraren da ke karkashin hukumar kula da gyaran hali ta kasar ta Saliyo. Duka an kai masu farmaki a wannan karo kuma wadanda aka tsare a cikinsu sun tsere.
Yanzu mun sani cewa a baki daya akwai wadanda aka tsare 2,213 idan aka hada wadannan wurare guda biyu. A cewar Col. Massaquoi, wanda gidajen kason ke karkashin ikonsa, cikin wadanda aka tsare sun hadar da sojoji da ‘yansanda wadanda aka tsare su a watan Agusta bisa zarginsu da yunkurin juyin mulki.
Amma yanzu an samu ci gaba. Maasaquoi yace a cikinsu akwai sanannan mawakin nan (LAJ,) wanda aka tsare shi shekaru tara bisa zargin hannunsa a fashi da makami da kai farmaki (robbery and assault.)
Col. Massaqoui yace ya zuwa ranar Talata akwai wadanda suka dawo gidan kaso su 144 wadanda suka tsere daga gidan gyara halin na maza, wanda ke tsare da masu laifi sama da dubu daya. Akwai wadanda aka tsare mata 16 da suka dawo daga cikin su 100, akwai wasu 16 mata wadanda akansu suka dawo daga cikin 100 da suka tsere. Akwai kuma biyu daga 14 da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki suma sun dawo.
Shugaban sojojin Peter Lavahun yace suna ci gaba da aiki don sake kama wadanda suka tsere da ma kama wadanda suka kai farmakin. An sanya ladan Le50,000 kimanin Dala ($2000) ga duk wanda ya ba da bayanai da suka kai ga kama wadanda suka kai farmakin, an kuma ware Le10,000 kimanin Dala ($400) a matsayin ladan da za a ba wa duk wanda ya ba da bayanai da suka kai ga kama wadanda suka tsere.
Mutum nawa aka kama ko aka kashe?
“Mun sani akwai dakarun sojan Saliyo RSLAF su 14 wadanda suka rasa rayukansu, akwai dansanda daya da jami’in hukumar kula da gyaran hali guda daya da maharan uku da wani farin kaya da ke aiki da wani kamfanin kula da tsaro mai zaman kansa guda daya. Akwai kuma wata mata guda daya da ta rasu wacce har yanzu ba a kai ga gano dalilan ganin gawarta cikin wadanda suka rasu ba acewar (Minister Bah).
Kawo yanzu jami’an sun bayyana cewa an kama mutane 14, 13 daga cikinsu sojoji da farar hula daya .
Yayin da ake gano dalilan rasa rayukan, har kawo yanzu an gaza gano dalilan mutuwar dan asalin kasar Kanada wanda kuma danjarida ne a kasar ta Saliyo. Stephen Douglas rahotanni na cewa ya rasu dalilin cutar bugun zuciya a ranar Lahadi a kusa da iyaka da Congo. Anan ne aka garzaya da shi zuwa asibitin sojoji na (34 Military Hospital) inda anan ne aka bayyana cewa ya rasu.
Ministan harkokin yada labarai da wasu majiya ta soja sun bayyana cewa ya rasu ne dalilin bugawar zuciya, sai dai an bar baya da kura, bayan da wakilin BBC Umaru Fofana ya ba da rahoto cewa sun gano jini a jikin Steven.
“Za mu bukaci bayanan gawarsa da dalilin mutuwarsa wanda daga nan ne za mu san inda muka dosa. Tuni mun fara wannan aiki kuma muna tuntubar jakada Macaulay. Mun tura wa babban jami’in lafiya Dr Owizz wanda zai gudanar da aikin binciken zuwa gobe Laraba.” A cewar IGP Sellu.
Wa ke da laifi?
Jami’an soja na taka tsan-tsan, ka da su dora alhakin dalilin mutuwar kan kowa. Sai dai shugaban sojan Lt. General Lavahun, ya ce alamu na farko sun nunar da cewa akwai hannun mutanen da ke da alaka da tsohon Shugaba Ernest Koroma.
Ya ce wasu daga cikin wadannan mutane sun kasance cikin masu ba da tsaro ga tsohon shugaban, Leatherboot da Sorieba da wasun su. Za dai mu ci gaba da bincike har sai mun kai ga samun isassun bayanan kammalawa. Mun ga takardar manema labarai da tsohon shugaban ya fitar.”
Mr. Koroma ya ci gaba da cewa ba zai kai ga kammala cewa suna da gamsassun shedu da za su alakanta abun da tsohon shugaban kasar ba, ta yiwu sun yi aikin a radin kansu. Ya kara da cewa za su ci gaba da gudanar da bincike.
‘Yannadawa na All Peoples Congress sun fitar da tasu matsaya (statement) inda suke nesanta kan su da wannan farmaki har ma wasu na ci gaba da yin Allah wadai da farmakin (attack.)
Duk da wannan ci gaba da ake samu, mazaunan na Freetown na cikin fargaba kan mai zai je ya dawo nan gaba, sanin cewa da dama cikin maharan da wadanda suka tsere daga gidajen kaso ba a kai ga kama su ba. A aikin neman maharan da aka yi a ranar Talata mutane a birnin (Murray Town,) sun shiga fargaba dalilin jin harbe-harben bindigogi (gunshot exchanges.) Minisftan ya tabbatar da cewa jami’ai ne suka yi musayar wuta da daya daga cikin maharan, bayan da suka yi yunkurin kama shi ya bude wuta, don haka ”Lamura sun daidaita a birnin na Murray domin nima na kai ziyarar gani da ido kafin na zo nan don jawabi ga manema labarai. Ka da ku ji fargaba ku je ku ci gaba da harkokinku” Bah ya fada gaban manema labarai.
Wannan tobacci da ya bayar bai gamsar ba ga da dama, kasancewar mazauna Jui sun ba da rahoton cewa sun ji karar harbe-harbe a daren Talata daga bisani dokar hana fita ta ci gaba duk da cewa an sauya lokacin inda dokar kan fara daga karfe tara na dare zuwa shida na safe a ranar 28 ga watan na Nuwamba.