African LanguagesHausa

Shafin IReV na INEC bai taba nuna cewa Peter Obi ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 a jihohi 19 ba

Zargi: Sakamakon zabe daga shafin INEC na IReV ya nuna cewa Peter Obi ya yi nasara a jihohi 19 har da babban birnin tarayya Abuja. 

<strong>Shafin IReV na INEC bai taba nuna cewa Peter Obi ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 a jihohi 19 ba</strong>

 Sakamakon Bincike:  Babu cikakkiyar gaskiya. A lokacin da aka hada wannan rahoton, ba a kai ga kammala hada sakamakon da aka samu daga rumfunan zabe a duka yankunan Najeriyar ba, bare har a dora su a shafin IReV.

Cikakken Bayani 

Biyo bayan bayyanar  Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, magoya bayan jam’iyyun adawa sun nuna takaicinsu da ma adawan da suke yi da sakamakon da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta INEC ta bayyana.

Hukumar ta sanar da Mr Tinubu, a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya bayan da ya sami jimilar kuri’u 8,794,726 wanda ya ba shi nasara kan sauran ‘yan takara 17n da suka nemi mukamin 

Yana biye da Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta  PDP wanda shi kuma ya sami kuri’u 6,984,520 yayin da  Peter Obi na jam’iyyar LP ya zo a mataki na uku da kuri’u  6,101,533.

‘Yan takara ukun, Mr Tinubu, Mr Obi, da Mr Atiku sun yi nasara a jihohi 12 kowannensu yayin da Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP shi kuma ya yi nasara a jiha guda.

To sai dai wadansu ‘yantakara a zaben sun nuna rashin gamsuwarsu da sakamakon da aka sanar. Ranar Litini, Mr Atiku ya jagoranci mambobin jam’iyyarsa a wata zanga-zangar da suka yi a gaban hedikwatar INEC a Abuja dan bayyana rashin gamsuwar ta su.

Mr Obi shi ma ya bayyana cewa shi ne ya ci zaben shugaban kasa kuma zai yi iya kokarinsa wajen ganin ya sami adalci a kotu. 

Babban abun da ya yi sanadin wannan takaddamar ita ce na’urar BVAS wadda ya kamata a yi amfani da ita wajen dora sakamakon zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

Wasu masu amfani da shafin Facebook wadanda ke goyon bayan masu rajin tabbatar da Peter Obi a matsayin shugaban kasa, wadanda aka fi sani da ‘Obidients’ sun yi zargin cewa Mr Obin ya yi nasara a jihohi 19 a kasar har da birnin tarayya Abuja. Sun kuma kara da cewa dan takaran PDP ya yi nasara a jihohi takwas ne kadai a yayin da APC ta ci a jihohi bakwai ita kuma jam’iyyar NNPP ta ci a jihohi biyu.

Wannan zargin ya bi kusan ko’ina a shafukan soshiyak medica abun da ya sa muka ga ya dace a tantance gaskiyar batun. Ana iya ganin wasu daga cikin labaran a nan, nan da nan.

Tantancewa

DUBAWA ta ziyarci shafin INEC na ganin sakamakon zabukan kasar. A lokacin da aka kammala hada wannan rahoton, karfe 05:47 na yamma 7 ga watan Maris 2023, sakamako daga runfunan zabe 164,233 ne kadai aka riga aka dora bisa IRev abun da ke zaman kashi 92.8 cikin 100 na rumfunan zabe 176,846 da ke kasar, wannan na nufin cewa ba riga an wallafa sakamakon runfuna 12,613 da yankunan daban-daban a duk fadin kasar ba.

Dan haka rudani kawai ake janyo wa idan har aka yi watsi da sakamakon da INEC ta riga ta gabatar aka koma ga zargin cewa Peter Obi ya yi nasara a jihohi 19 har da birnin tarayya Abuja.

Bacin haka, bincikenmu ya nuna mana cewa mai amfani da shafin Facebook din da ya wallafa wannan bayanin a Facebook, wato Mazi Chiemena Samuel, wanda ya nuna cewa jam’iyyar LP ta yi nasara a jihohi 18 da Abuja babban birinin tarayya ba daga shafin IReV ya samu ba. Ya dauko shi ne daga wani rahoton da ya yi hasashen yadda zaben zai kaya, wanda kungiyar Nextier ta dauki nauyin yi ranar 27 ga watan Janairun  2023

A karshe

Zargin cewa Obi ya yi nasara a jihohi 19 bisa sakamakon da aka bayyana a shafin INEC na IRev ba gaskiya ba ne a wani shafi daban aka sami wannan labarin kuma shi ma hasashe ne da aka yi tun kafin a gudanar da zaben ba abun da ya faru a zahiri ba ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »