|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Babangida ta hanyar shafin X an yi zargin yayi jinjina ga tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari saboda amincewa da Abiola a matsayin shugaban kasa, sannan ya yaba wa ‘yan Najeriya saboda damar da suka samu wajen gudanar da zabe mai cike da adalci.

Hukunci: Yaudara ce! Duk da cewa Babangida ya yaba wa Buhari kan yadda ya amince cewa Abiola shine yayi nasara a zaben 12 ga Yuni, 1993 a sabon littafi da ya wallafa, tsohon shugaban bai taba wallafa hakan ba a shafin X kasancewar bai mallaki wani shafi ba a kafofin sadarwar zamani.
Cikakken Bayani
A ranar 20 ga watan Fabrairu, 2025, tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Babangida ya kaddamar da wani littafinsa mai taken “A Journey In Service”, “Tafiya a rayuwar Aiki” inda yayi bayani kan rayuwar aikin soja da juyin mulki da ma irin dana sani da yayi a lokacin da yake jagorancin Najeriya karkashin mulkin soja a tsakanin 1985 zuwa 1993.
Babangida yayi jawabi sosai kan rushe zaben na 12 ga watan Yuni, 1993 wanda ya bawa Moshood Abiola nasara a zaben shugaban kasa.
Wannan mai amfani da shafin na X ya fakaice da wadannan bayanai ne na Ibrahim B. Babangida (@General_Ibbro), shugaban mulkin sojan Najeriyar a baya, da yayi jinjina ga tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya amince cewa Abiola shine yayi nasara a zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yuni, 1993, sannan ya yaba wa ‘yan Najeriya saboda bashi dama ya gudanar da zabe mai cike da tsari da ba almundahna.
Wallafar da ta fita a ranar 21 ga watan Fabrairu,2025 ga abin da take cewa “Nayi farinciki da gwamnatin Buhari da ta amince a karshe cewa marigayi MKO Abiola ya zama tsohon shugaban kasa kasancewar yayi nasara a zaben ranar 12 ga watan Yuni, 1993, masu tsara zaben shugaban kasa da ni kaina muna so mu godewa ‘yan Najeriya saboda bani dama ta gudanar da zabe mai inganci a tarihin Najeriya.”
Ya zuwa ranar Alhamis 27 ga watan Fabrairu, 2025, wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla 409,000 views, da wadanda suka nuna sha’awarsu 3668 likes, da wadanda suka sake wallafawa 481 reposts, da wadanda suka nuna alamar za su sake nazarta 233 da masu kafa hujja 190.
Bayan nazartar abubuwan da masu sharhi ke cewa wasu sun rika yaba wa tsohon shugaban, yayin da wasu ke cewa shine musabbabi na halin matsaloli da Najeriya ta samu kanta a ciki.
”Kai dan kama karya ne. Kokarin kare kai da kake yi ba zaa karba ba, Ina labarin Dele Giwa? Ina labarin Mamman Vasta? Ina labarin sojojin da suka yi hadari a jirgin sama? ” Duk wadannan tambayoyi ne da @Aluta_Panorama yayi.
Wani mai amfani da shafin, @OneMeOneMe, yayi nasa rubutun da cewa, “ Ka sani cewa kana da hannu a cikin matsalar rayuwa da muka tsinci kanmu a ciki a Najeriya a yau. Bara mu fada maka cewa kaine tushe na cin hanci da rashawa a dukkanin ma’aikatu na gwamnati. Ka sani cewa kai ne ka assasa yadda ake daukar masu kisan gilla ga ‘yanadawar siyasa.”
Shima, @egedeblessing5 ya fada cewa, “Ba don ka rushe zaben ba, duba da tsari da yanayi na tattalin arziki a duniya a wancan lokaci da Najeriya ta samu gagarimin ci gaba, amma son kai naka ya kai mu wannan hali da ake ciki.”
Duba da irin mutumin da aka bayyana da irin yadda mutane ke mayar da martani kan wannan wallafa, hakan ya sanya DUBAWA ganin wajibcin duba wannan da’awa.
Tantancewa
DUBAWA ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ta duba wannan da’awa inda sakamakon ya nunar da cewa tsohon shugaban mulkin sojan ya yaba wa Buhari saboda yadda ya girmama Abiola bayan rasuwarsa. posthumously recognising Abiola as the June 12, 1993 election winner. Sai dai yadda aka yi bayanin kamar yadda aka ce a bayan nan ya bayyana haka a littafin da ya buga, ba a shafin sada zumunta ya wallafa bayanin ba.
“Nayi farinciki cewa gwamnatin Buhari a karshe ta amince MKO Abiola tsohon shugaban kasa ne.” Saboda ta bamu dama ta ganin abin da muke fatan ganin mun sauya, sannan yace, kamar yadda na fada a baya, fadin haka zai taimaka amma dai ba dadi. Kamar yadda mai nazartar littafin Yemi Osibanjo ya bayyana a lokacin kaddamar da littafin.
DUBAWA ta duba shafin na X wanda ya fitar da wannan wallafa sai ta gano cewa shafi ne na kwaikwayo ko na bogi (parody account).

Screenshot of the X account’s profile.
Idan zaa iya tunawa a 2024, Babangida ya bayyana cewa bashi da wani shafi a shafukan sada zumunta (Babangida publicly clarified he does not own any social media handle) ya kuma bukaci al’umma da su kaucewa duk wani labari da ya fita daga wannan shafi da ake bayani a kansa da sunansa.
A Karshe
Binciken da DUBAWA ta yi ta gano cewa Babangida bai yada wata da’awa ba a shafin X har yake yabawa Buhari. Shafin da ake da’awar cewa na Babangida ne kirkirarsa aka yi.




