Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awar cewa amfani da albasa na da tasiri ga lafiyar mafitsara.

Hukunci: A kwai kanshin gaskiya a bayanin, ko da yake wasu bincike na masana a fanin lafiya sun tabbatar da albasa da tafarnuwa suna da muhimmanci kan abin da ya shafi lafiyar mafitsara, sai dai wannan bincike na da wasu tarnakai, wanda ke bukata a zurfafa nazari.
Cikakken Sako
Batutuwa da suka shafi lafiya na ci gaba da daukar hankali a shafin Facebook, wadanda wasu ke ganin hanya ce ta samun bayanai da suka shafi lafiya ta hanyar intanet. Wannan na karuwa yayin da a hannu guda ake kara samun yawaitar masu fada aji kan sha’anin na lafiya a shafukan sada zumunta, wadanda kuma ke zama sun cancanta su ba da shawara kan sha’anin na lafiya ko basu cancanta ba.
Duk da kokarin da masu aikin gano gaskiyar labarai suke da masu bincike kan irin labaran karya da ake bazawa a shafukan sada zumuntar, ana ci gaba da samun irin wadannan bayanai da suka shafi lafiya da ke ci gaba da bazuwa wanda kuma barazana ce ga lafiyar al’umma.
Saboda muhimmancin batu na lafiya ga dan Adam, duk wani bayani da ya shafi lafiya ya kamata a tabbatar da sahihancinsa kafin a amince da shi ko a yada shi.
A shafin Facebook, Dr Barbara O’Neill a baya-bayan nan tayi da’awa (claimed) cewa albasa na da muhimmanci ga lafiyar mafitsara da abin da ya shafi rashin lafiyar ta mara.
A hoton da aka wallafa an nuna mutum na rike da marainansa a gefe guda kuma ga albasa. Taken labarin na cewa ne: “Wannan zai sanya mafitsararka ta zama kamar sabuwa! A game da abubuwan da kakanni ko tsofaffi ke bukata! akwai kari….”
A makale jikin hoton ana sanar da masu amfani da shafin bayanai na irin amfani da ke tattare da albasa a jikin dan Adam.
Idan aka bi link da zai kai ga wannan makala (article) ta yi bayani cewa cin albasa zai kara lafiya ga al’aurar namiji musamman tana kunshe da sinadarin quercetin baya ga wasu nau’ika na vitamin da sinadarai da ke cikinta.
Marubuciyar ta kara da cewa tana shawartar idan za a yi amfani da albasar a hada da wasu kayan kamar tumatir da ke da sinadarin ( lycopene) da koran shayi wanda ke da (antioxidants) da kifi me mai da ke da sinadarin (Omega-3).
Wani mai irin wannan da’awar ma ya bayyana cewa amfani da albasar na yin maganin cutar kansar mafitsara kamar yadda aka gani a wadannan wurare: (here, here, da here).
Bayani game da lafiyar Prostate
Halittar ta prostate wata halitta ce karkashin matattarar fitsari kusa da babban hanji na maza wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen ba da damar haihuwa ga maza, Shine ke taimakawa wajen samar da ruwa-ruwa da ke kunshe da maniyi wanda kuma ke taimakawa wajen tunkuda maniyi lokacin da namiji ke inzali yayin saduwa.
Ita halittar ta prostate girmanta kamar gyadar bature da ake kira (walnut) ce, ana yawan ganinta ga mazajen da suka manyanta, musamman wadanda suka haure shekaru 40, ta kan girma fiye da kima, shine ake cewa mutum ya samu cutar da kan shafi mafitsara da aka fi sani da suna Benign Prostatic Hyperplasia (BPH). yayin da mutum ya kai shekaru 60 yana da yiwuwar nuna alamu ya kamu da cutar da kaso 50%, wannan adadi na iya kaiwa da kaso 90% yayin da mutum ya haure shekaru 80.
BPH, wannan yanayi da ake cewa prostate ta mutum ta girma, wannan baya nufin ace mutum yana fuskantar barazanar kamuwa da cutar dajin mafitsara amma zai zama yana da wahala yayi fitsari koma yayi masa wahala fitar da maniyi yayin saduwa.
Wasu cutukan da ke da alaka da ita prostate din sun hadar prostatitis (kumburinta) da cutar kansar mafitsarar da ake kira da (prostate cancer).
Shin akwai alaka tsakanin maganin cutar da kan shafi halittar ta Prostate da amfani da albasa?
Wata makala (article) daga Harvard Health a shekarar 2009 ta fitar ta ba da rahoto cewa idan aka hada albasa da tafarnuwa suna da tasiri ga BPH, sai dai wannan bincike na wata cibiya a Italiya an yi shine ta hanyar tambaya kan abincin da mutanen ke ciki sai aka gano cewa mazaje da suke da BPH suna cin tafarnuwa kadan da cin albasa kadan a cikin mako idan aka kwatanta da mutanen da basu da cutar ta BPH.
Wannan nazari na da iyaka, bai yi bayani ba kan wace irin albasa ko tafarnuwa suke ci ba, ko hanyar da ake hada su ko akwai wasu nau’ikan kayan lambun da suke ci ko bayani kan sauyin abinci da suke amfani da shi ba a tsawon lokaci.
A wani nazari (study) da aka yi a 2020 don gwajin tasirin ruwan albasar a maganin cutar da kan shafi prostate inda aka yi amfani da beran (Wistar Rats} sai aka gano cewa akwai raguwa ta kwayoyin halittar ta prostate, ko da yake an lura da cewa akwai karin wasu dalilai da ka iya tasiri kamar tsari na rayuwa.
A wani binciken (study) da aka yi an gano tasirin jar albasa a kan bera (Wistar rats) da aka fidiye, an fahimci cewa yawan sinadarin albasar da aka sa masa ya nuna irin yadda prostate din ke girma ko yake raguwa a jikin beran.
Nazarin ya fahimci tasirin wannan sinadari da ke rage yiwuwar kumbirin cikin halittar ta Prostate a mafitsarar. Nazarin dai ya kammala da cewa ya danganta da adadi na yawan sinadarin da aka tatsa daga albasar aka sanyawa beran.
A Karshe
Yayin da aka samu bayanai na masana a fannin lafiya da suka nuna tasirin albasa da tafarnuwa kan lafiyar da ta shafi prostate din da ke a mafitsara, ya kuma ja hankali da gargadi cewa duk mutum da ke fama da matsalar wahalar yin fitsari ko kumburi na prostate a mafitsararsa, ya je ya tuntubi likita kafin ya fara shan wasu maguna na gargajiya da ke zama hade-hade da gabje-gabje.