African LanguagesHausa

Abubuwan da kundin tsarin mulki ya tanada game da dakatarwar Sanata Natasha

Getting your Trinity Audio player ready...

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya umarci jami’an tsaro su fitar da Natasha Akpoti-Uduaghan daga cikin zauren majalisar a ranar 20 ga Fabrairu, 2025, bayan ta ki zama akan kujerar zama da aka ware mata. 

A ranar 25 ga Fabrairu, 2025, majalisar ta mika wa kwamitin da’a, da karbar koken jama’a don binciken halayyar da ta nuna domin ladabtarwa. Babban mai tsawatarwa na majalisar ya ce dokokin majalisar na 24 da na 6, sun bai wa shugaban majalisar dattawan damar sake wurin zama ga dan majalisa kuma sanata zai iya magana ne kawai daga kan kujerar da aka ware masa.

Kwanaki kadan sai lamarin ya ta’azzara, inda Natasha ta je a wani gidan talabijin na kasar inda ta zargi Akpabio da neman yin lalata da ita a lokacin da ta kai masa ziyara a gidansa da ke Uyo a jihar Akwa Ibom. 

Duk da cewa majalisar dattawa, da Akpabio, da kuma matarsa ​​sun musanta zargin cin zarafin da Natasha ta yi, hakan ya haifar da cece-kuce tare da haifar da muhawara a fadin kasar.

Ga abin da muka sani dangane da batun.

Tarihin zarge-zargen

Wannan dai ba shi ne karon farko da su biyun ke fadawa cikin irin wannan dambarwar ba. Reno Omokri, wanda tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne, ya bayyana yadda Sanata Natasha ta zarge shi da yin lalata da ita a cikin fadar shugaban kasa dake Aso Rock. 

Hakazalika, Joy Nunieh, tsohuwar manajan darakta mai kula da hukumar yankin Neja Delta (NDDC), ta yi zargin cewa a watan Yulin 2020, ta mari Akpabio a lokacin da ya nemi yin lalata da ita a gidansa da ke Abuja. A wancan lokacin, shugaban majalisar dattawan shine ministan harkokin Neja Delta.

Ikon da tsarin mulki ya bai wa Majalisar Dattawa

Duk da cewa ta karbo wani umarnin wucin gadi daga kotu, wanda ya umurci kwamitin majalisar dattijai da kada ya yi binciken kan lamarin, majalisar dattawa ta dakatar da Sanatar Kogi ta Tsakiya na tsawon watanni shida bisa zarginta da nuna rashin da’a.

A baya dai dan majalisar ta gabatar da korafi a hukumance kan zargin cin zarafinta da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya yi, amma majalisar ta ki karbar korafin. Sai dai ta sake gabatar da batun a gaban majalisar, inda daga nan ne aka mika korafin ga kwamitin da’a don gudanar da bincike tare da gabatar da rahoto ga majalisar nan da makonni hudu.

Binciken DUBAWA ya nuna cewa a sashe na 60 na kundin tsarin mulkin Najeriya, Majalisar Dattawa ko ta Wakilai na da ikon tsara yadda za su gudanar da ayyukansu, ciki har da yin kiranye. Wannan yana nuna cewa majalisun biyu suna da ikon sanya ƙa’idodin da za su tafiyar da majalisar, ciki har da na dakatarwa.

Hakazalika, mun yi nazari kan sashe na 88 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya, inda muka gano cewa ya baiwa majalisar dokokin kasar damar gudanar da bincike kan al’amuran da suka shafi ayyukanta, wadanda kwamitin da’a ne ke da ikon sauraron irin wadannan batutuwa.

Hakama, doka ta 97 (4) (a), da (b) da (c) na Dokokin Majalisar Dattawa na 2015 ta bai wa kwamitin da’a da karbar korafi na majalisar dattawa ikon yin duba akan duk koke-koken da ake gabatar masa bisa ga tanadin doka.

Shin an dakatar da Natasha kan doka ?

Cece-kuce ya barke a fadin kasar tun bayan da aka dakatar da Natasha. Masu suka dai sun yi tsokaci kan hukuncin da kotu ta yanke a baya kan irin wannan dakatarwar, suna masu cewa majalisar dokokin Najeriya ba ta da hurumin dakatar da kowane dan majalisa sama da kwanaki 14. 

Yaya gaskiyar wannan batun? Mun gano wani hukunci da mai shari’a Nnamdi Dimgba na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yanke a watan Mayun 2018, inda ya dogara da sashe na 21 (2) na dokar majalisar dokoki (bangaren iko da gata). Dokar ta kayyade kwanaki 14 a matsayin lokacin da majalisa za ta iya dakatar da memba da ya yi laifi. 

Hakazalika, Deji Adeyanju, wani lauya mazaunin Abuja, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook

“Yan majalisa sun jahilci doka. Majalisar dattijai ba za ta iya dakatar da dan majalisa sama da kwanaki 14 na majalisa ba.” Inji shi.

DUBAWA ta kuma tuntubi wani lauya Sidi Bello, inda ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar ba ta da madogara a cikin kundin tsarin mulki na dakatar da duk wani dan majalisa. Ya bayar da misali da shari’ar Abdulmumini Jibril, dan majalisa mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a jihar Kano, inda kotu ta yi watsi da dakatarwar da aka yi masa.

“Ba zan iya kawar da cewa Majalisar Dokoki ta kasa tana da wasu dokoki (na gudanar da ayyukansu) ba, amma majalisar dattawa ta mayar da kwamitin da’a tamkar wata kotu, kuma ba su da hurumin yin hakan,” inji shi.

Lauyan ya lura karaya ko da cewa abinda Natasha ta yi ya saba wa ka’idojin majalisar, bai kamata majalisar dattawa ta yi bincike akanta ba, sai dai kamata ya yi ta sanya wata hukuma mai zaman kanta ta yi binciken tare da ladabtar da ita.

DUBAWA ta tuntubi Yemi Adaramodu, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yada labarai, da mataimakinsa, Afolabi Salisu, sai dai babu wanda ya mayar da martani.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »