African LanguagesHausa

Shin ana iya kamuwa da cutar sanyi ta Gonorrhea a idanu kamar yadda wani mai amfani da shafin X ya nunar?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya wallafa hoton wata mata idanuwanta a kumbure inda ya ce ta kamu ne da cutar sanyi ta Gonorrhea.

Shin ana iya kamuwa da cutar sanyi ta Gonorrhea a idanu kamar yadda wani mai amfani da shafin X ya nunar?

Hukunci: Gaskiya ce! Cutar sanyi  Gonorrhoea na iya shafar idanuwa muddin aka shafi idanuwa da ruwa-ruwan al’aura da ke kunshe da kwayoyin cutar.

Cikakken Sako

Wani mai amfani da shafin X wanda aka bayyana da zama likita a kasar Ghana ya wallafa  posted wani hoto na mace da kumburaren idanu wacce aka gano ta harbu da kwayoyin cutar sanyi ta gonorrhoea a idanunta.

Ta yiwu ta harbu da kwayoyin cutar ne bayan da aka zubar da maniyi a kan fuskarta bayan saduwa da wani namiji da ke dauke da cutar.

An dai samu martani mabanbanta kan wannan batu, wasu sun aminta, wasu kuma na nuna shakkunsu.

Wani mai amfani da shafin @samuel_sesah, yayi nasa tsokaci da cewa “Gonococcal Conjunctivitis. Wani abin dariyar shine ta yiwu zai tafi yana karya cewa ai dama ta tashi ne daga barci ta ga tana da cutar.””

Wani kuwa mai suna, @iamMELMAK, yayi tambaya ne da cewa, cutar sanyi “Gonorrhea a kuma idanu?”

A sakon da ya wallafa @menp3gyimie shima tambaya yayi cewa ta yaya haka za ta yiwu likita?”

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla views miliyan hudu da dubu dari biyu, an samu wadanda suka nuna sha’awarsu  likes, 14,000 sai wadanda suka sake wallafa labarin repost 4,228, da masu kafa hujja quotes 1,517 da da  bookmarks. 2,742.

Banbance-bancen da ake samu na martani da mutane ke yi ya sanya DUBAWA shiga aiki gadan-gadan don tabbatar da ingancin bayanan.

Tantancewa

Cutar sanyi Gonorrhoea sannaniyar cuta ce da ke kama mutane sanadiyar jima’i (STD). Ita ce cuta ta biyu da bacteria ke kawo ta hanyar yin jima’i. Nazarce-nazarce studies da aka yi kan cutar ta Gonorrhea sun nunar da cewa cutar kan kama al’aura ta namiji ko ta mace, sai dai kuma ta kan kama idanu da baki da makogwaro da kasan hanji. Ana kamuwa da cutar ta hanyar jima’i tsakanin gaban namiji da mace ko ta hanyar sanya al’aurar a baki ko dubura.

Wani rahoto report na Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya nunar da cewa an samu sabbin alkaluma na wadanda suka kamu da cutar ta gonorrhoea su miliyan 82.4 a tsakanin baligai da aka tattara bayanansu a 2020.

Gonorrhea na iya kama infect idanuwa wannan ake kira Gonococcal Conjunctivitis. 

A cewar kundin bincike na National Library of Medicine, Gonococcal Conjunctivitis cuta ce da ake kamuwa da ita yayin da idanu ya samu tabuwa da ruwan maniyi. Duk da cewa wannan cuta ana iya maganinta idan aka kyale ta ba tare da kulawa ba tana iya zama ciwon idanu ko ma ta yi sanadi na makancewa.

DUBAWA ya tuntubi Dr Tavershima Adongo, don ji a mahangarsu ta kwararru a fannin na lafiya ko cutar ta gonorrhea za ta iya shafar idanu, sai Mista Adongo yace yanayi da ake samu gonorrhea ke bazuwa zuwa idanu shi ake kira Gonococcal Conjunctivitis.

“Tabbas, gonorrhoea, cutar da ake samu dalilin jima’i (STI) na iya kama idanuwa shi ke zama gonorrhoea conjunctivitis ga baligai. Wanda ke zuwa sanadin maniyin mace ko namiji ya taba idanun abokin saduwa.”

Mun kuma tuntubi babban likita na International SOS., Jeffrey Ajoko. Mista Ajoko ya jaddada cewa Gonorthea na kama al’aura ce kuma tana iya kama wasu sassa na jiki kamar idanu idan maniyi mai dauke da cutar ya shafi idanu.

“ Bisa al’ada cutar sanyin ta Gonorrhea na samuwa ne dalilin haduwar al’aura, sai dai kuma ta kan shafi wasu sassa na jiki idan suka samu shafa bayan fitar da maniyi daga al’aurar da ta kamu da cutar.”

Karshe

Wasu bincike-bincike da aka yi da bayanan da kwararru a fannin lafiya suka yi sun nunar da cewa gonorrhea na iya kama idanun mutum idan suka samu shafa daga maniyin da ya fita daga al’aurar da ke dauke da cutar.

Wannan bincike an yi shine karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararru na Kwame KariKari Fellowship da hadin gwiwar Dataphyte a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »