African LanguagesHausa

Shin Babangida ya goyi bayan a kama masu neman a kori al’ummar Igbo #IgboMustGo?

Getting your Trinity Audio player ready...

    Da’awa: Wani mai amfani da shafin X yayi da’awar (claim) cewa Ibrahim Babangida yayi kira ga gwamnatin tarayya ta kama mutane da ke neman a kori al’ummar Igbo..

    Shin Babangida ya goyi bayan a kama masu neman a kori al’ummar Igbo #IgboMustGo?

    Hukunci: Karya ce. DUBAWA ta gano babu wata hujja cewa Babangida yayi kira da a kama mutane da ke son ganin an kori al’ummar Igbo, mai magana da yawunsa yayi fatali da ikirarin.

    Cikakken Sako

    A baya-bayan nan akwai kiraye-kiraye a shafukan sada zumunta (social media campaign) musamman shafin X inda ake neman a tilasta ficewar al’ummar Igbo daga Legas zuwa wata jiha a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya .

    Wannan kiraye-kiraye mai lakabin #IgboMustGo ya ja hankali sosai saboda wasu sun yi amanna cewa Igbo sun taimaka a yayin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta #EndBadGovernance. 

    A ranar 2 ga watan Agusta, 2024 wani mai amfani da shafin X yayi da’awa (claimed) cewa tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Babangida ya fada wa gwamnatin Tinubu cewa ta kama mutanen da suke jagorantar fafutukar ganin an kori Igbo a fafutukarsu mai taken #IgboMustGo.

    A rubutun yana mai cewa “Rashin mutuntawa da tsana da ake wa al’ummar Igbo bai kamata a goyi baya ba, daga kowane yanki ne kuwa.”

    “A matsayinmu na ‘yan Najeriya ya kamata mu rungumi son juna da zaman lafiya da daraja juna, ina kira ga gwamnatin Najeriya ta kama wadanda ke fafukar ganin an kori Igbo #IgboMustGo,”

    Ya zuwa ranar Talata 20 ga watan Agusta,2024 wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla su 264,000 da wadanda suka nuna sa’awarsu 3,750 da wadanda suka sake wallafa da’awar 1,249 da masu kafa hujja 77 da masu son sake bibiya 84.

    Ganin yadda wannan wallafa ta dauki hankali ta sanya DUBAWA shiga aikin tantance sahihancin wallafar.

    Tantancewa

    DUBAWA ta gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi don tantance ko da’awar ta gaske ke ce amma babu wata alama da ta gasgata bayanan.

    Da jaridar ta nitsa a bincike kan shafin X na tsohon shugaban mulkin sojan na Najeriya amma sai ta lura cewa babu shafin da hukumance Babangida ke amfani da shi.

    DUBAWA sai kuma ta shiga bincike kan shafin na X da aka wallafa labarain sai ta gano cewa na bogi ne.

    “ Ba tsohon shugaban sojan Najeriya ba tsakanin 1985 zuwa 1993…..”wani bangare na abin da aka rubuta a shafin kenan.

    Did Babangida support #IgboMustGo advocates’ arrest?

    Hoton da aka dauko daga shafin na bogi da aka ce na Babangida ne. 

    DUBAWA ta duba ko da za a ga wata kafar yada labarai da ta wallafa labarin sahihiya amma babu.

    A karshe sai muka tuntubi mai magana da yawunsa Kassim Afegbua, a dangane da wannan kalami, ya fada wa DUBAWA cewa duk wani abu da aka wallafa da sunan Babangida a intanet ka da ku aminta da shi.

     Yace “Yi watsi da duk wani abu da aka alakanta da Janar IBB a shafin X ko wata kafar sadarwar zamani, yaudara ce, da dagula tunani, an fitar da abu da gangan don a alakanta da shi, abin da kuma bai ce ba. Bashi da wani shafi na X ko Facebook ko Instagram.”

    Karshe

    Bincike da jaridar DUBAWA ta gudanar ya gano cewa babu wata sheda ko hujja da ta nunar da cewa abin da mai da’awar ke fadi ya fito ne daga Mista Babangida.

    Show More

    Related Articles

    Leave a Reply

    Back to top button