African LanguagesHausa

Bidiyon Manajan Daraktan NNPC L yana watsi da batun ba da tallafin mai yaudara ce

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awa (claims) cewa manajan darakta a kamfanin mai na NNPC L ya karyata batun ba da tallafin manfetir

Bidiyon Manajan Daraktan NNPC L yana watsi da batun ba da tallafin mai yaudara ce

Hukunci: Yaudara ce. Ko da yake bidiyon da ya nunar da manajan daraktan na magana kan batun janye tallafin manfetir din gaskiya ne amma an dauki bidiyon ne a watan Oktoba,2023. Sabanin yadda mai da’awar ke nuna cewa maganar sabuwa ce, ba ta da alaka da cece-ku-ce da ake faman yi a baya-bayan nan. 

Cikakken Sako

A baya-bayan nan an rika caccaka (public criticism) ga bangaren gwamnatin tarayya (government) a dangane da batun ci gaba da biyan kudin tallafin manfetir, bayan kuwa tun da fari a ranar 1 ga watan Mayu,2023 Shugaba Bola Tinubu ya bayyana janye tallafin manfetir. Ana tsaka da haka ne sai ga wani mai amfani da shafin Facebook Abdullahi Anrihi ya wallafa bidiyo na babban jami’i a kamfanin na Nigeria National Petroleum Company (NNPCl), Mele Kyari, na karyata ci gaba da biyan kudin tallafin manfetir daga gwamnatin tarayya.

“Babu wani kudin tallafin manfetir da ake biya kowane irine kuwa. Ku yi watsi da labaran karya ” cewar Mele Kyari,” Haka mai amfani da shafin na Facebook ya nakalto shugaban na fadi.

Ya zuwa ranar 23 ga watan Agusta,2024, wannan wallafa ta samu wadanda suka nuna sha’awarsu 5 da mamsu sharhi 8 da masu sake wallafawa su 2.

A bangare guda kuma sai ga wannan bidiyo  da labari irinsa an sake wallafa shi a shafin X kamar anan (here da here) dama shafin Facebook (here da here).

Duba da irin muhimmanci na wannan wallafa DUBAWA ta ga dacewar gano sahihanci na wannan bidiyo da ake yadawa.

Tantancewa

Da aka yi amfani da dabarun gano asalin bidiyo ta hanyar (Google Reverse Image) an samu cikakken bidiyon da kafar yada labaran Channels ta wallafa a ranar 9 ga Oktoba, 2023, a wallafar da Channels ta yi tace Mista Kyari ya fadi cewa babu batun biyan kudin tallafin manfetir.

DUBAWA ta gudanar da bincike ko wata kafar yada lanbarai ta fidda rahoto kan kalaman na babban manajan darakta kan batun na janye tallafiin manfetir a 2023. A ranar 9 ga watan Oktoba, 2023 jaridar  Premium Times  ta ba da rahoto cewa Mista Kyari bayan ganawa da Shugaba Tinubu ya fada wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa gwamnatin tarayya ba ta dawo da biyan kudin tallafin manfetir ba.

Mun kuma gano wani rahoton mai kama da wannan kafar yada labaran Arise News da Vanguard sun wallafa labarin a ranar dai ta 9 ga Oktoba,2023. 

Karshe

Bidiyon da mai da’awar ya fitar da ya nuna babban manajan daraktan na cewa babu batu na biyan tallafin manfetir ba maganar yanzu ba ce, kamar yadda mai da’awar ya nunar. Rahotanni daga kafafan yada labarai sahihai sun nunar da cewa lamarin ya faru ne a watan Oktoba, 2023.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button