|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Masu amfani da shafin Facebook da dama sun yi da’awa (claim) cewa China ta yi gargadi ga mutanenta su guji zuba jari ko gina kamfanoni na miliyoyin daloli a jihar Legas bayan da mahukunta a jihar suka rushe wasu gine-gine a filin baje koli na jihar.

Hukunci: Karya ce! Babu wata majiya mai tushe da ta wallafa wannan labari daga gwamnatin China ko ofushin jakadancinta. Yayin da a Legas ne ake rushe-rushen, hoton da aka sanya a jikin da’awar hoton taron manema labarai ne a birnin Beijing na China inda mahukunta suka sanya sharuda a hukuncin masu laifin fafutukar awaren Taiwan “’yan aware”.
Cikakken Sakon
A ranar 25 ga watan Satumba,2025 gwamnatin jihar Legas ta rushe (demolished) wasu gine-gine a filin baje koli a karamar hukumar Ojo ta jihar.
”Kwamishinan tsara birane na jihar Oluyinka Olumide a wani sako (statement) da ya fitar ta hanyar daraktan harkokin al’umma a ma’aikatar Mukaila Sanusi, yace rushe-rushen ya zama dole ne “don kaucewa ci gaba da yaduwar gine-gine da basa kan ka’ida a filin baje kolin.”
Yayin da aikin rusau din ya jawo zanga-zanga (protest) da suka (criticism) musamman a tsakanin manyan ‘yansiyasa a Najeriya ita kuwa jihar ta Legas ta kare (defended) kanta inda take kafa hujja da hukuncin kotu na watan Satumba, 2003.
Ana tsaka da wannan rusau sai aka fara samun masu nuna damuwa a jihar, wani mai amfani da shafin Facebook , Joe Vicar…, ya wallafa da’awa (claim) a ranar 7 ga Oktoba,2025 cewa kasar China ta gargadi al’ummarta kada su kuskura su zuba jari ko su sanya miliyoyin daloli wajen samar da kamfanoni a jihar Legas.
Wallafar ta kara da cewa gwamnatin kasar China ta bayyana cewa tana ci gaba da sanya idanu a Legas ta lura da yadda shaguna da harkokin kasuwanci na baki a ke rushe su, kuma mafi akasari wadanda abin ya fi shafa al’ummar Igbo ne.
Ga abin da da’awar ke fadi;: Labari da Dumi-Dumi: China ta yi gargadi kada al’ummarta ta kuskura ta zuba jari ko gina wani kamfani na miliyoyin daloli a Legas, kasancewar gwamnatin jihar Legas ta saba rushewa al’umma gine-gine ta kwace filaye musamman na mutanen da ba ‘yankasa ba kamar al’ummar Igbo” haka ya rubuta.
A wallafar an makala hoto da ke nuna alamar taron manema labarai da kuma wajen da aka yi rusau din.
Ya zuwa ranar 10 ga Oktoba,2025 wallafar ta samu martani 9,100 da tsokaci 7,000 da sake yadawa 2,900.
A baya ga kalamai na kabilanci wasu masu amfani da shafin sun rika yin tambaya ne a game da sahihancin da’awar, wasu kuma na kira ga ‘yan kasar ta China da su je wasu jihohin na Najeriya su zuba jari maimakon jihar ta Legas.
Daya daga cikin masu amfani da shafin Taiwo Orejobi, yayi tsokaci ne da cewa “Ina shawartar ‘yan China su tafi jihar Anambra ko Kano su zuba jarinsu a can.”
Chio Lisa ta rubuta cewa, “Da Allah ku zo Gabshin Najeriya ku gina duk abin da kuke so, zuba jarinku ba shi da wata matsala zai samu kariya.”
Wani mai amfani da shafin, Femi Ade, yayi tambaya ne da cewa “abin sha’awa, shin za ka iya bamu wata kafar yada labarai ta China ko wani sashin gwamnati da ya fitar da sanarwar manema labarai?” dama ranar da aka fitar da wannan sako?
Abu ne muhimmi a gudanar da bincike kan wannan jawabi kamar a anan.’
Za a iya ganin wannan da’awa a shafin na Facebook kamar a wadannan wurare (here, here, here, here. Haka ma Instagram here, here, da X.)
DUBAWA ta shirya gudanar da bincike kan wannan da’awa don tabbatar da ingancinta da tasiri na yada labaran da ba haka suke ba, dama duba alakar Najeriya da China da batun zuba jari.
Tantancewa
Mun lura da cewa wannan wallafa an danganata da jami’ai na kasar China kamar yadda aka rubuta cewa “Idan har gwamnati za ta yi wa al’ummarta wannan, ta yaya baki za su samu nutsuwa idan suka zuba jari? Abin da ke faruwa da ‘yan Najeriya a Legas idan baki ne daga ketare lamarin sai ya fi muni. Muna kallon abin da ke faruwa. Idan har ‘yan Najeriya zaa yi masu haka a lalata masu kasuwanci, masu zuba jari sai sun ninka taka tsantsan da suke yi,” (kamar yadda ya rubuta).
Sai dai babu inda aka samu irin wannan bayani daga gwamnatin kasar China ko ofishin jakadanci. A bayanin da aka zakulo ta Google ya nuna (traced) sun fito daga wallafar da aka yi a shafin sada zumunta.
DUBAWA ya kuma duba wasu kafafan yada labarai sahihai irinsu China Global Television Network, Xinhua, China Daily, South China Morning Post da Global Times, amma babu wani abu mai kama da wannan batu da aka samu.
Mun kuma duba wasu shafuka na jami’an gwamnatin China kamar wadannan here, here, da here. Babu wani jawabi a hukumance da aka samu kan wannan da’awa.
Ofishin jakadancin China a Najeriya ya fitar (issues ) da jawabi kan abin da ya shafi ‘yan China amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani gargadi akan zuba jari a Legas.
Mun gudanar da bincikar hoton da aka sanya a da’awar, bincikenmu ya kuma gano hoto ne na taron manema labarai (press conference) a birnin Beijing na China da aka yi a ranar 21 ga Yuni,2024, inda mahukunta suka sanya sharuda na hukunci kan masu fafutukar aware na Taiwan “‘yan aware”.
Wannan taron manema labarai ba shi da alaka da cewa gwamnatin China ta yi gargadin cewa kada ‘yan China su gina kamfanoni a Legas, haka nan mun ga hoton cikin (Getty Images).
Haka kuma hoto na biyum da aka gani hoto ne na ainihin wurun da aka yi rusau a filin baje kolin. Wannan kuma za a iya ganinsa a Premium Times, The Cable, da The Sun Nigeria, baya ga wasu kafofi muhimmai na yada labarai a Najeriya.
Waye mai da’awar?
Da fari mun duba shafin mai da’awar, binciken gano gaskiya ya nunar da cewa shafin mai shi ya fito ne daga Amurka, sannan dan asalin Igbo an sauya sunan mai shafin sau biyu tun bayan da aka bude shafin a ranar 25 ga Janairu,2024. Wannan ya sanya shi kansa shafin akwai tantama a kansa.

Hoton shafin Facebook na mai da’awar bayan binciken gaskiya a kansa.
Karshe
Da’awa cewa China ta gargadi al’ummarta kada su kuskura su zuba jari ko gina kamfanoni na miliyoyin dala a Legas karya ce. Babu wata kafa sahihiya da ta fitar da wannan kalami daga bangaren gwamnati ko ofishin jakadanci.
Haka kuma hoto na biyu rusau din ya faru ne a Legas, hoton farko kuwa da aka makala taron manema labarai ne a birnin Beijing na China lokacin da mahukunta ke bayyana sharudan hukunci ga masu neman awaren Taiwan “‘yan aware.”




