African LanguagesHausa

Shin da gaske ne duka ministocin Tinubu daga yankin Kudu maso yammacin kasar suka fito kamar yadda wani mai amfani da shafin X ke da’awa

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X na da’awar cewa yawancin manyan ma’aikatan da gwamnatin Tinubu ta zaba daga yankin kudum maso yammacin kasar.

Shin da gaske ne duka ministocin Tinubu daga yankin Kudu maso yammacin kasar suka fito kamar yadda wani mai amfani da shafin X ke da’awa

    Hukunci: Yaudara ce! Bayanan da ake samu daga kafafen yada labarai na nuna cewa yawancin wadanda Tinubu ya zaba zuwa manyan mukaman kasar sun fito daga yankuna daban-daban na kasar ne ba kamar yadda ake da’awar cewa sun fito daga yanki daya kadai ba.

    Cikakken bayani

    A ‘yan kwanakin baya-bayan nan, son zuciya da kabilanci na cigaba da kasancewa dalilin damuwa a Najeriya saboda irin yanayin da ya ke dauka. A matsayin kasar da ke da kabilu daban-daban, kabilancin ya haddasa maganganun batanci wadanda ke yawan janyo rashin jituwa tsakanin manyan kabilu ukun da ke kasar.

    Wani mai amfani da shafin X, @Waspapping, ranar Juma’a tara ga watan Agustan 2024 ya yi da’awar cewa mafi yawan manyan mukaman gwamnatin Tinubu na hannun wadanda suka fito daga kabilar da ke da rinjaye a yankin kudu maso yammacin Najeriya.

    Ga dai abin da ya rubuta cikin bayanin, “ Duk wadanda ke rike da manyan mukaman gwamnati a karkashin gwamnatin Tinubu sun fito daga yankin kudu maso yammacin kasar ne. Mu an bar mu da mataimaka da masu bayar da sahwara wato SAs.”

    Tsokacin ya sami alamar like 1156, an sake rabawa sau 112, wasu 42 sun yi amfani da shi, 15 sun adana yayin da alkaluman nuna yawan wadanda suka kalla ke cewa an kalla sau 122.

    Cikin wajen tsokaci wato comment section, wadansu daga cikin masu amfani da manhajar sun goyi bayan da’awar amma kuma akwai wadanda suka karyata hakan.

    “Wannan ne abin da shi ma Buhari ya yi sadda ya ke rike da ragamar mulki. Yanzu lokacin yankin yammacin kasar, babu sauran bin tsarin tarayya a Najeriya,” a cewar @Marylifted.

    Wani shi ma mai amfani da shafin, @jidifeanyi ya ce “abin karba-karba ne ai. Buhari ya yi nasa. A karshe dai son zuciya ce kawai ke nasara.”

    Da ya ke karyata wannan zargin, @Oyeani_Kalu cewa ya yi, “Ba ku da wani abin yi sai haddasa husumi, me ya sa kuke wallafa abin da ku kanku ku san ba gaskiya ba ce? Bacin duk abubuwan da yankin Arewa ya samu a wannan gwamnatin kuna cigaba da korafi? 

    “Wannan ko daya ba daidai ba ne.” in ji @bummiearo.

    Ganin yawan mutanen da suka yi ma’amala da wannan bayanin da ma ra’ayoyi mabanbantan da aka wallafa ya sa DUBAWA gudanar da bincike dan tantance gaskiyar lamarin.

    Tantancewa

    Domin tabbatar da sahihancin wannan labarin, mun fara gudanar da bincike da mahimman kalmomin da ke la’akari da wadanda Tinubu ya bai wa mukaman minista. A nan ne muka gano wani  rahoto  na Gidauniyar Gudanar da Binciken Gaskiya a Labarai wanda ta fitar ranar 17 ga watan Agustan 2023, wanda ke bayani kan ministoci da jihohinsu na ainihi.

    A cikin rahoton, yankin arewa maso yammacin kasar ne ke da mafi yawan ministocin da aka zaba, inda ya ke guda 10, sa’annan ya na biye da yankin kudu maso yammacin wanda shi kuma ya ke tara. Yankunan Arewa maso gabas da Arewa maso tsakiya su kuma su kuma kowannensu na da takwas yayin da yankin kudu maso kudu ke da bakwai shi kuma yankin kudu maso gabashi ke da biyar.

    Daga nan sai mu ka duba sunayen wadannan misnitocin wadanda aka zaba dan ganin ko su ne aka tabbatar a hukumance kuma hakan muka gano tare da tabbacin cewa dukansu ne shugaban kasar Najeriya ya amince da mukaman da aka ba su.

    Haka nan kuma, mun yi bitar wani rahoton tahshar Channels wanda ya tabbatar cewa Tinubu ya zabi wadannan ministocin daga duka yankunan kasar.

    Bugu da kari ma kafofin yada labaran Punch da PM News duk sun dauki labaran a wadannan shafukan, wato da nan da nan.

    A Karshe

    Binciken DUBAWA ya tabbatar cewa ministocin da shugaba Tinubu ya amince da su ba daga wani yanki guda ba ne kamar yadda wani mai sharhi ya bayyana, majalisar ministocin ta kunshi mutane daga duka yankunan kasar, babu yankin da ya fi rinjaye kamar yadda ake zargi.

    Show More

    Related Articles

    Leave a Reply

    Back to top button