Fact CheckHausa

Shin Da Gaske Ne Gemun Masara Na Warkar Da Cututtuka A Jikin Dan Adam?

Zargi: Wani bidiyo da aka saka a shafin nishadantarwa a yanar gizo TikTok wanda mutane suka rika rarraba shi a shafin WhatsApp, wai gemun masara na warkar da cututtuka masu yawa a jikin Dan Adam. 

Gaskiyar Magana: Bincike mai zurfi ya nuna akwai sauran bincike da za a yi tukunna kafin ya tabbatar da haka ko akasi.

Cikakken Bayani

Kwararru sun ce yanzu salon bayar da magunguna da kula da marasa lafiya ya sauya daga amfani da matakan da aka riga aka tantance da ma hujjojin da aka samu na yadda suke tasiri a jikin mutum, zuwa amfani da kayan abinci dabamdabam, inda a nan ma kwararru da ma mutane masu zaman kansu ke fadakar da jama’a kan kula da lafiyar jiki da kuma kaucewa cututtuka ta hanyar amfani da abinci mai gina jiki, ganyayyaki ko kayan lambu da dai sauran su wadanda ke tare da mutane a koda yaushe.

Duk da cewa cin abinci mai gina jiki na da matukar amfani wajen warkar da cututtuka sannan da kiwon lafiya, hujjoji masu karfi sun tabbata cewa lallai cin abinci mai nagarta na taimakawa wajen warkewar cututtuka irin su cutar daji/kansa da wasu cututtukan da ake fargaba da gudun kamuwa da su.

Wani bidiyo wanda ya yi ta yawo a WhatsApp a Najeriya na bayanin cewa gemun masara dake cikin bawon ta wao wacce ba a budeta ba na warkar da cututtuka da dama. Bidiyon mai tsawon dakiku 35 ya nuna wata mata na bayanin yadda ake gyara gemun masara domin a yi magani da shi. Ta fara da gaya wa masu kallon bidiyon cewa “Ku tafasa ruwa sannan ku bayan kun tuttuge gemun masaran sai ku saka shi ciki. 

Bayan haka sai a kashe wutar girkin abarshi cikin tukunyar ta sallace, wato ta dan huce. Bayan minti 30 sai asha ruwan.” Daga nan matar ta ci gaba da cewa wannan ruwan da aka dafa da gemun masara yana da kyau wajen warkar da cutar mara da kuma koda. Yana kuma warkar da ciwon zuciya, da kumburin mafitsara da ma ciwon suga ko kuma diabetes. A karshe ta ce “Abubuwan da ke ganin ba wasu abin arziki bane ko kuma basu da amfani ke samar da waraka a jikin mutum a lokutta da dama” Sannan sai ta yi kira ga mutane su gwada wannan magani su gani.

Tantancewa

Dubawa ta yi bincike a manhajan TikTok inda ta gano bidiyon a shafin matar da tayi bidiyon mai suna Sharon. Tana amfani @eden.health a matsayin sunan shafin wanda ke da mabiya 548, 000. Akalla mutum miliyan 2 suka nuna alamun amincewa da shawarar da ta bayar a bidiyon. Taken ta shi ne “Ku bar abinci ya zama maganinku, maganinku kuma ya kasance abinci”

A shafin nata Dubawa ta gano cewa wannan bidiyon da ta yi kan masara kashi biyu ne, na farkon mutane sun kalla sau 515,000 sai dai abin da ke ciki bai banbanta da na biyu ba, bayanin da ta kara daya ne kawai inda ta ce masu kallo su sha kofi daya ko biyu a wuni daya ne bayan ya huce babu

Da yawa daga cikin masu bin shafinta ‘yan Asalin yankin Asiya sun ce lallai sun tuna kakanninsu a baya sun rika shan shayin gemun masara. A yayin da wasu ke dokin cewa za su su gwada wannan dabara, wasu kuma hankalinsu bai kwanta ba game da sahihancin sa.

Mene ne gemun masara kuma me ya ke yi?

Gemun masara wani abu ne dake tsurowa cikin masara, masu kama da fure, wadanda ke da launin ruwan kwai da ruwan kasa. An dade ana amfani da shi a matsayin magani a yankin Asiya na wani tsawon lokaci.

A wani binciken da aka wallafa a 2012 a kasidar Molecules, marubutan, Hasanudin, Hashim da Mustafa sun ce ana iya amfani da wannan gemun masara a matsayin maganin inganta garkuwar jiki, ko na rage damuwa, ko rage gajiya, ko kuma rage yawan fitsari da kuma cutar suga – wanda ke tabbatar da zargin da Sharon ta yi a bidiyonta na TikTok. To sai dai masu binciken sun kammala rahotonsu da cewa “yana da mahimmanci a gudanar da bincike na kimiya domin tabbatar da wannan ta yadda zai baiwa mai sha’awar amfani da shi karfin gwiwar yin hakan.” Wannan na nufin masu binciken sun fahimci cewa dole ne a yi karin bincike kafin a dauke shi a matsayin maganin da dan adam zai iya amfani da shi a hukumance.

Haka nan kuma, masu bincike Maksimović, Malencić and Kovacević, a wani rahoton binciken da suka wallafa a 2005, sun tabbatar da alfanun da ke tattare da amfani da gashin masarar amma su ma sun ce ya kamata a kara yin bincike “dan tantance sinadaren da ke cikin gashin masaran da kuma abin da suinadaran ke yi domin wata sa’a karfin aikin tsimin da aka yi da gashin ya danganci inda masarar ta fito.” Wannan na nufin akwai banbanci tsakanin ire-iren gashin masaran da mutane ke da shi, wanda kuma yake da babban tasiri ga irn alfanun da za’a samu. Wannan ne ma matsayar wasu masu binciken wadanda suka wallafa na su sakamakon a 2015 a wata kasida ta abinci.

Yayin da ya ke tofa albarkacin bakin shi dangane da dacewar amfani da gemun masara a matsayin abinci ko kuma magani, Dr Akeem Babalola Kadiri, malami a sashen ilimin ganyayyaki dake jami’ar Legas, ya ce hakika ana ambatan cewa gemun masara na maganin cututtuka da dama har da wadanda suka shafi ido kamar glaucoma sai dai “duk rade-radi ne wadanda ke bukatar bincike da hujjoji”

Ita ma babbar malama a sashen ilimin ganyayyaki a jami’ar Legas Dr. Temitope Onuminya ta bayyana wa Dubawa cewa ko da aka gwada karfin aikin gemun masara, a kan beraye aka yi ba dan adam ba. Ta kuma ja hankali kan cewa abu ne wanda “idan aka sha shi ya wuce kima zai iya yi wa hantar mutum lahani kuma “Yana iya yin kutse ga aikin magungunan da masu fama da cutar suga ko hawan jini”

Sai dai Dr Onuminya ta ce a yanzu ana amfani da shi a wasu kasashe a matsayin abin dake inganta abinci kuma ana iya shan shi sau biyu zuwa uku a rana muddin yana tsakanin mil 400 zuwa 450

A Karshe

Ana bukatar karin bayani game da ko mahukunta da masu gudanar da bincike sun amince dan adam na iya amfani da dafaffen ruwan gemun masara a matsayin magani domin yawancin binciken da aka yi a kan beraye ne. Akwai kuma bukatar tantance ko ana iya amfani da shi a matayin shayi ko wani sinadari na inganta abinci da ma yadda mutane za su iya amfani da shi ba tare da an fada cikin matsaloli na kiwon lafiya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button