Facebook/Shugaban Najeriya Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wasu shafukan yada labarai sun ce gwamnatin Najeriya za ta fitar da wasu dokoki da kowane malami mai wa’azi zai bi kafin ya fara wa’azi.

Hukunci: Karya ce! Babu wani yunkuri da gwamnatin Najeriya ke yi a yanzu na sanya dokoki da kowane malami mai wa’azi zai bi kafin ya fara wa’azi.
Cikakken Bayani
Kasa da kwanaki 24 kafin soma azumin watan Ramada da musulmi ke yi a kowace shekara, wasu shafukan yada labarai a dandalin Facebook ciki har da Duniyar labarai da Wakiliya sun wallafa wani labarin da ke cewa gwamnatin Najeriya za ta fitar da wasu dokoki da kowane malami mai wa’azi zai bi kafin ya fara wa’azi.
Wani bangare na labarin da aka wallafa na cewa: “YANZU YANZU: Azumi Saura kwanaki 24 Gwamnatin tarayya ta saka Sabbin Dokoki ga malamai Masu yin Wa’azi da Azumi wanda Gomnatin Bola Tinubu Zata Kafa Ga Masu Yin Wa’azi A Nigeria
Anba da shawarar kafa dokoki da sharuɗɗa kafin malami ya fara wa’azi a Nigeria kamar haka.”
- Hoton da aka zakulo a Facebook
Labarin ya dauki hankalin al’umma musamman musulmi wadanda su ne dokokin za su shafa, lamarin da ya sa fiye da mutane dari daya a shafin Wakilar da ke dandalin Facebook, suka yi ta tsokaci da kuma tofa albarkacin bakinsu akai.
Ganin yadda al’umma ke daukar lamarin da ya shafi addini da muhimmanci sosai, ya sa Dubawa bin diddigin wannan labarin domin tabbatar da sahihancinsa.
Tantancewa
Watan Ramadan shi ne wata na 8 a kalandar musulunci, watan da al’ummar musulmi ke gudanar da ibadar azumi kuma malamai ke yin wa’azi dare da rana domin isar da sakon Allah (SWT).
Tashin farko mun gano cewa wannan labarin jaridu da dama na kasar ba su wallafa shi ba kuma mun saka bayanan wannan dokar a shafin nema na goggle ba tare ganin bayani akan haka ba.
Bayan garzayawa a shafin masu taimaka wa Shugaba Tinubu kan yada labarai da suka hada da Bayo Onanuga da Daniel Bwala, babu wata sanarwa ko bayanin da suka fitar a ‘yan kwanakinnan wanda ya nuna cewa gwamnatin Najeriya na shirin sanya dokoki ga masu yin wa’azi.
Mun tuntubi babban mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya kan yada labarai Abdulaziz Abdulaziz, wanda ya shaida wa Dubawa cewa labarin wai gwamnatin Najeriya za ta fitar da wasu dokoki da kowane malami mai wa’azi zai bi kafin ya fara wa’azi, ba gaskiya ba ne.
“Babu wani abu kamar wannan” in ji Abdulaziz.
Haka kuma binciken Dubawa ya gano cewa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya yi tanadin ‘yancin yin addini da kowane mutum yake so ba tare da tsangwama ba. “Kowane mutum na da ‘yancin yin addininsu ko bin imaninsu ba tare da tilastawa ko nuna wariya ba” a cewar wani shafin da ake wallafa dokokin kundin tsarin wato Nigerianconstitution.com.
Sai dai akwai wasu jihohin kasar musamman na arewaci sun yi tanadin dokokin shari’ar musulunci, yayinda jihohi irinsu Kaduna sun yi dokoki akan yadda malaman addinin musulunci za su rika yin wa’azi a shekara ta 2019 (Premium Times report).
To amma duk da haka akwai wasu ‘yan kasar dake ganin ya kamata a samar da dokar da za ta lura da yadda malamai na addini ke yin wa’azi kamar yadda wannan makala da aka wallafa a jaridar Dailytrust ta nuna (Opinion Dailytrust).
A Karshe
Karya ce! Binciken Dubawa ya gano cewa babu wani yunkuri da gwamnatin Najeriya ke yi na fitar da wasu dokoki da kowane malami mai wa’azi zai bi kafin ya fara wa’azi.
