Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook yayi da’awa cewa idan ana cin ayaba ko agada wacce ke da digo-digo na baki-baki a jikinta, wannan na iya nuna cewa anyi amfani da sinadarin Calcium Carbide wajen nikata.
Sakamakon bincike: YAUDARA CE. Sabanin haifar da cutar daji ita ayaba da agada suna da sinadarin da ke yaki da cutar daji. Takan haifar da cutar daji ne idan aka matsa wajen ganin an nikata ta hanyar amfani da takin zamani mai guba, ko wasu sinadarai, sannan aka dauki lokaci mai tsawo ana cin ta a haka. Sannan binciken kwakwaf da aka gudanar ya gano cewa ayaba da agada da ake samu da baki-baki a jikinsu baya nufin an matsa wajen ganin sun nuna ta hanyar amfani da Calcium Carbide.
Cikakken sakon
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), daya daga cikin mutane shida da ke rasuwa a duniya suna rasuwa ne dalilin cutar daji. Bayan cutar ta daji sai kuma cutar da ke da alaka da zuciya da ke ta’azzara lamura (worse reputation) (daya cikin hudu) a Najeriya. Abin takaici, ita ce daga cikin kasashen Afurka (African countries) da ke da masu cutar daji da yawa, inda take yaki da rashe-rashe da ke da alaka da cutar ta daji 72,000 da wadanda ake ganowa suna da cutar 102,000 a duk shekara, kamar yadda shirin yaki da cutar na kasa National Cancer Control Plan, ya nunar. Wani shafin Facebook mai suna Eastern Pride, ya yada bidiyo (shared) wanda ya dauki mintuna uku da dakika 15 a ranar biyar ga watan Janairu, 2024. Wanda ke jawabi a bidiyon, yayi ikirarin cewa cin ayaba da ke da digo-digo na baki a jikinta na haifar da cutikan daji kala-kala.
Yace “mutane da dama suna fama da cutar ta daji, cutar dajin mama ce ko ta kashi da hunhu duk saboda nau’ikan abinci da muke ci. Idan ka ga irin wadannan nau’ikan ayaba da ke da digon baki kada ka siya tana haifar da cutittika a nan gaba.”
Ya bukaci masu bin shafinsa da kada su rika siyan ayaba mai baki-baki a jikinta kasancewar ana matsa mata ta nuna ko nika ta hanyar amfani da sinadarin calcium carbide. Ya zuwa ranar 21 ga watan Janairu, 2024, wannan bidiyo ya samu masu kallo 251 da masu martani 22 da masu tsokaci uku.
. Duba da irin yanayin da’awar da muhimmancinta ga Najeriya ya sanya dole DUBAWA ya shiga aikin bincike.
Mai bincike ke cewa game da cutar ta daji
Alyssa Tatum, wata masaniyar harhada kayan abinci ta bayyana (mentioned) cewa nama da giya da barasa da kayan kwalan da makulashe na ci da sha da ake samarwa a masana’antu da dangogin biskit da alawa “ba kai tsaye ba” ana alakanta su da yiwuwar haifar da cutar kansa. Duk da haka ta bayyana cewa ba za su haifar da cutar daji ba har sai an ci su ko sha fiye da kima.
”Don kawai ka gasa nama a karshen makon da ya gabata ka ci ,za a ce maka za ka kamu da cutar ta daji yanzu ba haka ba ne,” Ba lallai bane sau daya, idan ana yi ne daga lokaci zuwa lokaci ba kakkautawa. Shine abin lura, abin da ke da muhimmanci shine a rika ci ko sha tsaka-tsaki. A cewar ta.
Baya ga wannan, dangin kayan madara ko nono da kayan da aka soya fiya da kima na iya kara (increase) fargabar haifar da cutar daji saboda hanyoyi da aka bi wajen samar da su suna iya samar da (carcinogens) da kan iya alaka da kwayoyin halitta na DNA ya iya haifar da cutar kansa ta hanyar samar da kwayoyin halittar masu hayayyafa na (cancerous cells.)
Rashin samun daidaito na Oxidative stress na iya haifar da cutar kansa don haka ake son mutane su rika amfani da kayan marmari masu yaki da rashin daidaiton na (anti-oxidants). Ayaba da agada suna da sinadaran magnesium da vitamin E, sinadaran na taimakawa a yaki rashin dadaiton na (oxidative stress.)
Fatar bayansu da ke zama ta yi duhu, daya ne daga cikin alamu na cewa kayan marmarin sun nuna. Idan kuma nunar ta yi yawa ya nuna cewa sun samu sinadaran da ke hana rashin daidaiton na antioxidants da sinadaran da ke sa girma na tryptophan wadanda kan taimaka wajen rage damuwa da hana kwayoyin halittar su lalace.
Ayaba da ake nikawa da sinadarin Carbide
Duk da cewa tsawon lokaci ana ta samun bayanai daban-daban kan batun na nika ayaba ko agada da sinadarin na calcium carbide.
Shi mai wannan da’awa a rahoton yana cewa ne idan aka ga baki-baki a fatar ayabar yana nuna cewa an tilasta nikarta ne ta hanyar amfani da wancan sinadari. Wani mai da’awar kuma na cewa ne idan aka ga reshenta kore shine alamar anyi amfani da sinadarin wajen ganin ayabar ta nuna kamar anan (here) a 2019 ko nan (here) a 2021.
Har-ila-yau bincike-bincike da aka gudanar kan wannan da’awa ya nuna cewa ba lallai bane a amince da bayanan da aka fada idan ana so a gano ko ayaba ta nuna da kanta kamar yadda Allah Ya tsara ko kuwa an yi amfani da wasu sinadarai.
Za a iya gano wasu binciken na kwa-kwaf da aka yi, masu kama da wannan a wadannan kafofi Full Fact da USA Today da Reuters da AFP Factcheck.
Ra’ayin kwararru
Shafin DUBAWA ya tattauna da Temiloluwa Omotosho, kwararriyar masaniya kan hada abinci, kan ko cin ayaba da ta nuna da yawa na iya haifar da cutar daji. Sai tace “ai idan ayaba ta nuna sosai wannan ke nuna cewa akwai sinadarin sukari a cikinta, ita cutar kansa ko daji na iya faruwa idan dama mutum na da kwayoyin halittar da ke haifar da ita.”
Sai dai ta kara da cewa kansa na samuwa idan kwayoyin halittar ta kansa suka samu azalzala daga kayan marmari wadanda aka tilasta nunarsu ta hanyar amfani da wasu sinadarai masu hadari ko da takin zamani.
Ta kara da cewa “Hanya daya da za a iya kamuwa da cutar ta kansar ko daji idan aka tilasta amfani da sinadari kamar na carbide ko takin zamanin, kuma aka ci gaba da amfani da ayabar ba tsayawa. ”
Tessy Ahmadu, kwararryar masaniya kan cutar ta daji a Cibiyar kwararrun masana a fannin lafiya (Federal Medical Centre, Jabi,) ta yi watsi da wannan da’awa duk da cewa sinadarin Glucose na karuwa a ayaba ko agada, “Mutane da dama sun aminta da cewa cutar kansa na samun abinci daga glucose, daga nan ne mai wannan da’awa ya samo abin dogaronta, amma ba shine a gaba ba wajen jawo cutar kansa. “
Ms Tessy ta kara bayyana muhimmancin cin ayaba da ta nuna sosai tace tana kunshe da sinadaran potassium da magnesium. Kuma suna da glucose, wanda ta ce watakila shi ake dogaro da shi a akafa hujja, amma hakan ba gaskiya bane, kasancewar ba a kai ga tabbatar da hakan ba a kimiyance,” a cewarta.
A Karshe
Ayaba da agada da suka nuna sosai ba sa haifar da cutar kansa. Ita ayaba tana zama bai kamata a ci ba, idan aka ga alamun tsutsa a ciki ko tana doyi, Don haka da’awar cewa idan ayaba ta nuna da yawa kuma tana da baki-baki a jikinta tana kawo cutar kansa ko daji karya ne kuma yaudara ce.