Dakin Ka’aba. Hakkin Mallaka: Islamic Relief:
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa sabbin takardun Epstein Files, sun tabbatar da cewa an aika wani bangare na mayafin Ka’aba zuwa ga Jeffrey Epstein a Amurka.

Hukunci: Gaskiya ne. Takardun da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka (DOJ) ta fitar sun haɗa da imel da wasiƙu da ke bayyana yadda aka aika mayafin daga Saudiyya zuwa ga Jeffrey Epstein ta hannun wasu ƴan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Cikakken Bayani
Epstein Files wasu tarin manyan takardu ne da suka haɗa da hotuna, imel, bayanan jiragen sama, bayanan kuɗi, da hujjoji da suka shafi gurfanar da mai aikata lalata da yara, Jeffrey Epstein, da kuma waɗanda ke da alaƙa da shi.
A watan Janairun 2026, Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta fitar da wani kundin takardu da ke da alaƙa da shari’ar a matsayin wani ɓangare na aiwatar da dokar Epstein Files Transparency Act.
Bayanan da aka fitar sun ƙunshi miliyoyin shafuka daga bayanai daban-daban, ciki har da imel tsakanin Epstein da abokansa na kusa, abokan kasuwanci, da masu shiga tsakani a sassa daban-daban na duniya.
Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa wasu daga cikin takardun sun nuna an aika wani bangare na Kiswah — mayafin ɗaki mai tsarki da ke rufe Ka’aba a Makka — zuwa gidan Epstein a Amurka.
Mun gano irin waɗannan sakonni da dama a Facebook da X, kamar yadda aka gani a nan, nan, da kuma nan.
Wannan bayani ya tayar da ce-ce-ku-ce da suka haifar da martani mai zafi a cikin al’ummomin Musulmi, ganin cewa Kiswah ba mayafi ne kaɗai ba, alama ce ta ɗaki mai tsarki ga Musulmi.
Ra’ayoyin mutane sun bambanta inda wasu sun ƙi yarda da yiwuwar a aika irin wannan abu mai tsarki zuwa ga mutum irin Epstein. Wasu kuma sun fara tambayar dalilan da suka sa aka aika irin wannan abu.
Ka’Ab Abubakar Zage ya zargi wasu manyan Larabawa da hannu, yana cewa “an yi hakan ne da sani da amincewar larabawa”.
Sai dai Nouradine Daje Gaoudi ya ƙaryata labarin da ke yawo cewa an aika Kiswah zuwa ga Jeffrey Epstein.
Saboda muhimmancin lamarin, DUBAWA ta yanke shawarar tantance gaskiyar ikirarin.
Tantancewa
Don tantance ikirarin, DUBAWA ta binciki kundin bayanai na Ma’aikatar Shari’a ta Amurka.
Mun gano cewa imel da takardun suna nan cikin bayanan da DOJ ta fitar, kuma sun bayyana aka aika sakon Kiswah, kamar yadda aka gani a nan, nan, da kuma nan.
Wadannan sakonnin sun gudana ne tsakanin wata ‘yar kasuwa ‘yar Hadaddiyar Daular Larabawa, Aziza Al-Ahmadi, da wani abokin hulɗa daga Saudiyya, Abdullah Al-Maari, wanda ya shirya a kai kayan zuwa ga Epstein a Amurka.
Takardun sun nuna cewa jigilar ta ƙunshi sassa uku daban-daban na Kiswah, an rubuta bayanansu dalla-dalla tare da jigilar su ta jirgin British Airways daga Saudiyya zuwa Amurka.
Sai dai, takardun ba su yi bayani kan dalilin aika kayan ba, illa dai sun bayyana yadda aka yi jigilar mayafin da wasikun da suka shafe shi.
A Karshe
Ikirarin cewa Epstein Files sun tabbatar da cewa an aika mayafin Ka’aba zuwa ga Jeffrey Epstein Gaskiya ne.
