Hausa

Shin wata kotu a Najeriya ta umurci kamfanin MTN ya biya wani mai amfani da layin wayar nera milliyan 5.5 bayan da ya zarge kamfanin da zame mi shi nera 50?

Zargi: Wani sakon WhatsApp na zargin wai kotun Najeriya ta umurci kamfanin MTN ya biya Emmanuel Anenih, wani mai amfani da layinta Nera miliyan 5.5 bayan da suka cire mi shi nera 50 ba tare da samun amincewarsa ba.

Wani sakon WhatsApp da ke zagaya a dandalolin whatsapp na bayanain wai wani dan Najeriya mai suna Emmanuel Anenih ya yi nasara a karar da ya shigar na MTN bayan da ta karya doka ya zame nera 50 daga wayarsa da cewa wai ya sayi wata ‘yar wakar da ko daya bai saya ba.

Sakamakon wannan sakon da yawa daga cikin masu amfani da manhajan whatsapp na barazanar kai karar kamfanin suna cewa su ma sun taba samun matsala irin ta Mr. Anenih.

Sakon na cewa “wani dan Najeriya mai suna Emmanuel Anenih ya kai kamfanin MTN kara kotu bayan da suka karya doka suka cire nera 50 cikin kudin da ya sayi kati ba da izinin shi ba. Babban kotun a Abuja ya sami MTN da laifi ya kuma umurci kamfanin ya biya Mr. Emmanuek nera milliyan biyar da wani karin dubu dari biyar ya biya kudin lauyoyi da ma matsin lambar da abin da suka aikata ya janyo mi shi. Ina waya ta? Bari ni ma in duba in ga yawan sakonnin da suka aiko mun ni man zan kai MTN kara ranar litin.”

Wani mai amfani da WhasApp ne ya tambayi Dubawa ko za ta iya tantance gaskiyar wannan labarin.

Tantancewa

Da muka yi binciken mahimman kalamai a google, mun gano rahotannin da suka ambaci hukuncin kotun da aka yanke a watan Fabrairun 2020. Bayan da Emmanuel ya kai kamfanin MTN kotu a shekarar 2014 bayan da suka cire mi shi nera 50 ba da izinin shi ba.

Da muka yi karin bincike mun gano wani bidiyo mai tsawon minti biyu na wani labarin da aka sanya a tashar NTA. A cewar labarin, a watan oktoban 2014 Emmanuel Anenih ya kai MTN kotu bayan da suka zame kudi a wayarsa ba tare da izinin shi ba.

Bidiyon ya ce kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan da mai shigar da karar da kamfanin suka yi musayar sakonni dangane da batun. Haka nan kuma kotun ya ce akwai hujjojin da suka nuna rashin gaskiyar kamfanin tunda bayan da ya yi korafin, a daya daga cikin wasikun kamfanin ya  tura mi shi, akwai inda ya ambaci cewa lallai ya cire kudin ba tare da izinin shi ba amma kuma sai suka aika mi shi garabasa na nera 700 a sunan lada saboda ya shafe shekaru 8 ya na amfani da layin na su.

Labarin na NTA ya ce a shari’ar babban alkalin kotun na birnin tarayyar a wancan lokacin, Ishaq cewa ya yi nera 700 bai kai diyyan irin matsalar da suka janyo mi shi ba. Dan haka alkalin ya umurci kamfanin ya biya miliyan biyar a matsayin diyya da wani karin dubu dari biyar a matsayin kudin da zai yi amfani da shi ya biya lauyoyi.

A Karshe

Wannan binciken ya nuna mana cewa kotun Najeirya ya umurci MTN ya biya Emmanuel Anenih nera milliyan biyar da rabi bayan da suka cire nera 50 a wayarsa ba tare da izinin shi ba.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button