African LanguagesHausa

Shin ‘ya’yan kashu na bayar da kariya daga cutar daji?

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani shafin Facebook, Mazanjeeya ya yi ikirarin cewa ‘ya’yan kashu na bayar da kariya daga cutar cancer

Shin ‘ya’yan kashu na bayar da kariya daga cutar daji?

Hukunci: Yaudara ce. Binciken Dubawa ya gano cewa babu wata madogara da ta tabbatar da ingancin da’awar a kimiyyance.

Cikakken Bayani

Kashu, ‘ya’yan itace ne mai siffa kamar ta koda da aka samo daga bishiyar cashew – itacen da aka fi samu a Brazil amma yanzu ana noma shi a kasashe daban-daban a fadin duniya.

A nan yankunan Afrika ta yamma mutane da dama na cin sa ko kuma sarrafa shi zuwa abin sha domin saukin amfani da shi. Hakama yara suna kona ‘ya’yan tare da cin sa.

A ranar 14 ga watan Maris, wani shafin Mazanjeeya ya wallafa amfanin da ‘ya’yan Cashew da yadda suke taimaka wa jikin mutum, sai dai abin da ya fi jan hankalin dubawa shine da’awar cewa yana da wasu sinadarai da ke hana kwayoyin cancer girma.

“Kare Cutar Cancer – Suna da antioxidants kamar selenium da vitamin E, waɗanda ke hana ƙwayoyin cancer girma.” a cewar shafin Mazanjeeya.

Wannan bayani ya dauki hankalin sama da mutane 244 da suka yi sharhi (comments) yayin da mutum 457 suka yada (share) shi, kamar yadda muka zakulo a ranar 23 ga watan Maris na 2025.

A kokarin tabbatar da cewa sahihan bayanan lafiya ne al’umma ke tu’ammali da su a shafukan sada zumunta, Dubawa ta yi binciken don tabbatar da gaskiyar wannan da’awar.

Tantancewa

Binciken da Dubawa ta yi a shafin WebMD; shafin da ke wallafa bayanai kan harkar lafiya, ta gano cewa kashu na da muhimmanci sosai ga lafiya, sai dai babu wani bayani da ke tabbatar da cewa yana bai wa mutum kariya daga cutar cancer.

Dubawa ta tuntubi Dr Sani B Abubakar, kwararren likita a asibitin koyarwa ta jami’ar Usman Danfodio dake Sokoto wanda ya ce babu wani bincike da ya tabbatar da cewa ‘ya’yan kashu na kare mutum daga cutar cancer.

“Duk wani abu da aka ce yana magani, sai da aka bi ta hanyar bincike da gwajin kafin a amince da shi a fara aiki da shi a matsayin magani” in ji Dr Sani.

Ya kuma shawarci mutane su kaucewa irin shafukan da ba a tantance ba wadanda ke bayar da shawarwarin lafiya ba kan gado, sa’annan su rika tuntubar masana da likitoci a kan matsalolin da suka shafi kiwon lafiya.

Hakama shafin Healthline na kasar Amurka ya ce akwai karancin bincike akan shi kansa cashew, saboda haka akwai bukatar karin bincike kafin tabbatar da duk wani bayani game da shi.

A Karshe

Yaudara ce! Babu wata madogara a kimiyance da ta tabbatar da cewa ‘ya’yan kashu na kariya daga cutar cancer.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »