Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook cikin wani bidiyon da ya wallafa ya yi da’awar cewa wai wasu ‘yan ta’adda Fulani daga wasu kasashe na daban sun kai hari a Najeriya dan aikata kisar kiyashi.
Hukunci: Yaudara ce! Rahotanni masu sahihanci sun ce Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta yi watsi da wannan zargi ta ce karya ne, kuma babu wadansu rahotannin na daban wadanda ke nuna cewa rahoton ya fito daga shafin BBC ne kamar yadda mai amfani da shafin na Facebook ke da’awa.
Cikakken bayani
Ta’addanci a Najeriya na da dogon tarihi, kuma ya na cigaba da kasancewa babban kalubalen da ke shafar kasar da ma wasu kasashe a duniya. Musamman a yankin arewacin kasar, hare-haren da suka shafi Boko Haram da rikicin Fulani makiyaya sun kai ga rashin rayuka da kaddarori a yankunan da rikicin ya shafa.
Kwanan nan wani mai amfani da shafin Facebook, Critical Thinkers, ko kuma Nazari Mai Zurfi, ya wallafa wani bidiyon da ke nuna wadanda su wadanda ake zargi ‘yan ta’adda ne sun yi dammara da makamai a wani daji, tare da zargin cewa an turo su shiga Najeriya su yi kisar kiyashi.
“Labarai da dumi-duminsu, tashar BBC NEWS ta sanar cewa Fulani daga kasashen Afirka daban-daban sun isa Najeriya dan su gara kashe-kashe,” a cewar taken da aka yi wa bidiyon.
Labarin wanda aka wallafa ranar Juma’a 13 ga watan Satumban 2024 ya sami alamar like shida da tsokaci kuma ma har an sake raba shi ranar 22 ga watan Satumban 2024.
Da muka duba wasu daga cikin tokace-tsokacen da aka yi a kan labarin, DUBAWA ta lura cewa yawancin wadanda suka karanta labarin sun yarda da abin da aka rubuta.
Ganin haka ne ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tantance batun dan fadakar da mutane kan gaskiyar lamarin kafin ya haddasa rudani.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da binciken hotuna kan wasu daga cikin hotunan bidiyon. Sakamakon ya kai mu ga wasu labaran da aka wallafa cikin watan Yulin 2024 tare da bidiyon da take makamancin wannan kamar yadda za ku iya gani a nan da nan.
Da muka cigaba da gudanar da bincike, mun duba mu ga ko lallai BBC ce majiyar labarin. Mun yi amfani da mahimman kalmomi dan tantance hakan, inda muka sa “Rahoton BBC dangane da Najeriya” wanda ya bamu duka rahotannin da tashar labaran ta yi a cikin watan Satumba. Mun yi bitan labaran daki-daki amma babu wanda ya yi bayani mai kama da da’awar da muka gani.
A waje guda kuma, yayin da muke gudanar da bincike dan tantance gaskiyar bidiyon mun gano labarai da dama masu sahihanci.
Misali, jaridar Vanguard ta rawaito ranar 27 ga watan Yunin 2024 cewa ‘Yan sanda sun karyata bidiyon sun ce abun ya faru ne a shekarar 2018. Suka ce an gyara bidyon ne kawai dan sa tsoro cikin zukatan jama’a.
Haka nan kuma gidan talibijin na kasa Nigerian Television Authority (NTA) shi ma ya yi wannan labarain ranar 27 ga watan Yuni.
Bacin haka, mun gano wani labarin da ‘yan sandan Najeriya suka wallafa ranar 26 ga watan Yunin 2024, a kan shafinsu na twitter wato X inda a nan ma suka ce labarin yaudara ce kawai.
Wani bangare na labarin ya yi bayani kamar haka, “Bayan nazari mai zurfi wanda ;yan sandan Najeriya suka yi a ofishinsu na yaki da miyagun laifukan yanar gizo, muna tabbatar mu ku da cewa wannan bidiyon an kikiro da shi an yadatun ranar 28 ga watan Mayun 2028.”
“Bincikenmu ya nuna mana cewa kwanan nan an gyara bidyon ne an wallafa tare da bayanan karya da nufin janyo matsala da haddasa rudani a cikin kasar,” kamar yadda ‘yan sandan suka bayyana.
Haka nan kuma, binciken da muka yi dan ganin ko za mu gano labarin cikin kafofin yada labarai masu sahihanci bai nuna mana wani labari dangane da kutsen Fulanin kasashen Afirka a Najeriya ba.
A Karshe
Bincikenmu ya nuna mana cewa bidiyon yaudara ce kawai, kuma babu hujjar da ta nuna cewa BBC ce ta wallafa labarin ko kuma ma sun goyi bayan labarin.