Getting your Trinity Audio player ready...
|
Hadakar kungiyoyin yankunan da ke amfani da harshen Hausa a karkashin kungiyar da ake kira Hausa World Congress tare da tallafin makarantar koyon harsunan Afirka da ke karkashin Kungiyar Tarayyar Afirka AU sun kaddamar da wani taroa Ouagadougou, ranar tara ga watan Mayu wanda za’a kammala a ranar 11 ga watan Mayun idan Allah ya kai mu.
Yawancin wadanda ke amfani da harshen Hausar dai na samuwa ne a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar Afirka da wasu kadan daga yankin gabashin nahiyar.

Farfesa Bashir Sallau daga jami’ar Jihar Katsina da ke Dutsen Ma na daga cikin wadanda za su gabatar da takarda a taron kuma kan maganarsa ita ce tsagun gargajiya na hausawa wadanda su kuma suka kasu gida uku wato tsagar gado, tsagar kwalliya da tsagar magani, da dai dukan abubuwan da suka shafi tsaga musamman yadda zamani ke tasiri da addinin musulunci ganin yadda yanzu ba’a cika yi wa yara tsaga ba.
Ana sa ran halartar wakilai kusan 150 daga Kasashe sama da 15, wadanda suka hada da Benin, Burkina Faso, Kamaru, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Kwango Brazaville, Ivory Coasr, Gabon, Ghana, Guinea Bissau, Equatorial Guinea, Mali, Nijar, Najeriya, Senegal, Chadi, Togo da Sudan.
Taron dai wani bangare ne na yunkurin da Kungiyar Tarayyar Afirka ke yi wajen ganin an fadada harsunan Afirka ta yadda za su sami karbuwa a kuma rika amfani da su a harkokin yau da kullun.