Asalin hoton: Chude Jideonwo
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X yayi da’awa a wani bidiyo cewa wata mata da aka nuna a bidiyo na juyayin kisan mamba a iyalin da ta fito bayan kashe-kashe da aka yi a birnin Jos.

Hukunci: Yaudara ce! Bidiyon da aka nuna tsoho ne, an dauko shine daga wani fim na tarihi da Chude Jidenowo yayi shi a watan Disamba,2025.
Cikakken Labarin
Fiye da shekaru 20 jihar Plateau da ke yankin Tsakiya a Najeriya na ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula inda ake samun yawaitar rasa rayukan mutane, wasu da dama na kauracewa muhallansu.
A ranar Lahadi 29 ga watan Maris,2026, wasu ‘yanbindiga sun kai farmaki a Gari Ya Waye wani yanki na garin Jos inda akalla mutane 20 suka rasa rayukansu. A cewar mazauna garin na Gari Ya Waye a yankin Angwan Rukuba wasu mutane dauke da makamai sun shiga garin inda suka yi ta harbe-harbe na kan mai uwa da wabi.
A ranar 30 ga Maris,2026 wani mai amfani da shafin X SIZWE-BANSI (@SizweBansii) ya yada wani bidiyo inda ya nuna wata mata na juyayi. Mai da’awar ya nunar da cewa wata mata ce ta rasa danta a harin da aka yi a baya-bayan nan a garin Jos na jihar Plateau.
A bidiyon mai tsawon mintuna biyu, matar na zaune a dandabaryar kasa tana kururuwa a wani yanki na fim din, inda Chude Jideonwo dan Najeriya ke tambaya don neman karin bayani game da halin da ake ciki.
A waccan wallafa an rubuta taken labarin da ke cewa “ “yanta’adda masu da’awa da sunan addini sun halaka mata yaro da mijinta a garin Jos na Najeriya. Mabiya addinin Kirista na fuskantar gallazawar ‘yanta’adda da sunan Musulinci inda mutane da dama suka rasa rayukansu, tsawon wane loka za a dauka ana irin wannan ta’addanci?”
Ya zuwa ranar 30 ga watan Maris,2026 wannan bidiyo ya samu wadanda suka kalla sama da 489,000 da wadanda suka nuna sha’awarsu 22,000 da wadanda suka sake yadawa 11,000 da masu tsokaci sama da mutum 1,000.
Da yake tsokaci a dangane da wannan bidiyo A.Paul (@embracelovetv) yace “wayyo Allah Ya kawo wa wannan mata dauki tare da iyalanta fiye da yadda dan’Adam ke tunani. Wannan abu yayi mata yawa.”
Wani shima mai amfani da shafin mai suna king wings (@wings_6070), yayi nasa tsokaci cikin tausayawa “danta da mijinta sun mutu a Jos, lokaci ne na tausayawa.”
Jinin wadanda basu ji ba basu gani ba yana kwaranya, yaushe za a kawo karshen haka?”
Duba da yadda wannan da’awa take ta yaduwa DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan bidiyon da abin da ake fadi.
Tantancewa
Domin tantance wannan bidiyo, DUBAWA ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi ta bincika ko za ta ga wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da wannan rahoto amma babu ko daya da ta alakanta wannan bidiyo da kisan na Jos.
Mun kuma dauko bidiyon don tantance shi da Google Images da InVID.
Sakamakon sai ya kaimu ga tashar Chude ta YouTube inda aka ga cewa wannan bidiyo tsoho ne kuma yana nan a shafin intanet tun kafin ma watan na Maris, 2026 lokacin da aka yi kisan na Jos. Mun kuma ga cewa asalin bidiyon an wallafa shi a ranar 12 ga Disamba, 2025.
Chude ya fitar da wani labari na tarihi a watan Disamba inda ya ziyarci jihar ta Plateau don bincike ko shin da gaske ne a kwai kisan kiyashi da akewa mabiya addinin Kirista a Najeriya.
Yayin da a kafafan yada labarai da dama suka wallafa labarin kisan da aka yi a Jos, babu wata kafa da ta fitar da labari da ya nuna bidiyo da yayi daidai da wannan da ake yadawa.
A Karshe
Bincikenmu ya gano cewa bidiyon da ake yadawa na yaudara ne, tsohon bidiyo ne aka fito da shi ake sake yadawa ana alakanta shi da kisan da aka yi a jihar Plateau.
