African LanguagesHausa

Wani labari da aka kaga aka kuma danganta da shugaban kasar Ghana wai yayi da’awar cewa Najeriya ita ke gaba da kasar Ghana

Da’awa:  Nana Akufo-Addo, shugaban kasar Ghana an yi zargin cewa ya wallafa wani labari a shafin X (posted on X)  cewa Najeriya hamshakiyar kasa ce idan aka kwatanta da Ghana ta fuskar kyau da tattalin arziki da harkokin nishadantarwa.

Sakamakon bincike: Labarin kirkirarsa aka yi ta fasahar AI wanda ake kira  “Fake Details.”Wanda hakan ya nunar da cewa ba kawai labarin na yaudara ba tsabar karya ce.

Cikakken sakon

Nuna cewa kowa ya isa a tsakanin mutanen kasashe abu ne da ke zama sananne a kafar sadarwa, inda za ka ga ana ta muhawara kan nuna karfin da kowace kasa ke da shi ta fuskar ci gaban fasaha da tattalin arziki da harkokin nishadi uwa uba ingancin rayuwa.

Kowane bangare za ka ga yana tunkaho da nuna isa cewa kasarsa ce kan gaba, duba da irin wadannan abubuwa. Lamarin da ka iya haifar da muhawara  yayin da irin wannan tattaunawa kan nuna inda kowane mutum ya fito a wani lokacin ta kan haifar da sanya mutane a rudani ko nuna son kai koma haifar da rarrabuwar kawuna.

A baya-bayan nan wani mai amfani da shafin TikTok @dior btc, ya wallafa wani labari da aka dauko ko kwafo hotonsa wanda aka ce jawabi ne ( statement ) da aka raba shi da shafin X na Nana Akufo-Addo, shugaban kasar Ghana, A jawabin ya nunar da yadda shugaban ke gargadin ‘yankasar ta Ghana cewa su guji kalaman batanci ga ‘yan Najeriya inda yayi da’awar cewa Najeriya ta sha gaban Ghana ta fuskar tattalin arziki da harkokin nishadi da kyau.

“Ya ku ‘yankasata Ghana ku dena kalubalantar uwa a gare ku (Najeriya) Kasar ta sha gaban Ghana da kaso dari ta fuskar kudi da harkokin kade-kade da kyau, da Allah ku dena muzanta Najeriya kasancewar zamanta uwa a gare ku.” A cewar sakon.

Da ka kalli jawabin za ka ga bai kama da wanda shugaban kasa zai wallafa ba, amma duk da haka mun ga yadda wasu ke cewa an yaudare su da wannan sako da aka wallafa.

Ga misali mai amfani da shafin na TikTok @princebby_1 ya tabbatar da da’awar kai tsaye inda ya ce “Ni dan kasar Ghana ne kuma duk abin da shugaban kasarmu ya fada a nan gaskiyua ne.”

Wani ma da ya goyi bayan wannan kalami shine, @PrinceBillions, wanda yace shima dan kasar Ghana ne kasarsu “babu komai a cikinta.”

Wannan sako da aka wallafa ya samu masu nuna sha’awa(likes) 6000 da wadanda suka yi tsokaci (comments)1,000 ya zuwa lokacin buga wannan labari. Duba da irin girman matsayin wanda aka raba da labarin da irin tsokaci da ake yi kan wannan labari ya sanya shafin na DUBAWA ya gudanar da bincike kai tsaye.

Tantancewa 

Lokacin da muka shiga aikin tantancewa: Mun ga kura-kurai na zahiri: Akwai rashin bin ka’idojin rubutu a jawabin da yadda ake sake yada labarinma, dama rashin nuna adadi na wadanda suka kalla ko  nuna lokaci. 

A sakon da aka alakanta da shugaban kasa, wallafawar ta nuna an sake yadawa sau  “9786558 retweets”  ga masu nuna sha’awa “97753747 likes.” Yadda aka jera lambobin ya saba ka’idar X aga yawan adadi daruruwa haka. Ga misali maimakon a rubuta 3,000 likes. A shafin X za a rubuta shi kamar haka ne 3K likes. Idan kuwa adadin ya kai miliyan a X za ka ga an rubuta 9.7 M retweets da 9.7M likes.

Har ila yau akwai wata murdiyar kuma. Idan aka kalli wannan da’awa, X na amfani da wasu alamu da za su sadar da bayanai na likes da retweets ba kamar yadda aka nuna ba a hoton da aka kwafo.

Idan aka kalli batun na lokaci “AM” ko “PM” ana rubutawa ne da manyan harufa, wannan labarin da aka wallafa kuwa ya saba hakan. An rubuta “am” da kananan baki.

Wannan ya sake fito da zargi, cewa wannan rubutu da aka wallafa da sunan shugaban kasa na iya zama kirkirarre. Mun binciki sunan wanda ya wallafa labarin a shafin na X sai ya kaimu ga wani shafin wanda ba a tantance ba (parody account) wanda ke da masu binsa 223. Sako da aka wallafa na baya-bayan nan kan wannan shafi an yi shine a ranar 5 ga watan Oktoba, 2020, wanda ya sha banban da ranar da aka ce shugaban ya rubuta wadancan kalamai wato 6 ga watan Janairu, 2024. A bangare guda kuma shafin Mista Akufo-Addo official account, ya kasance yana da mabiya da suka kai miliyan biyu da dubu dari shida, yana kuma da alama da ke nuna cewa shafin X ya tantance shi.

Har ila yau mun kuma gano wasu kura-kuran biyu a hoton da aka kwafo da ke yaduwa, shafin da aka yi amfani da shi na dauke ne da tambari da ke launin shudi, haka kuma sunan mahaifin shugaban babu karan dori a yadda aka rubuta, sabanin asalin sunan sa, haka kuma an nuna cewa shafin ba halastacce ba ne.

Wannan ya tabbatar da cewa jawaban ba daga shafin X na asali na shugaban ya fito ba, abin da ya tabbatar da cewa kirkira ce mara inganci. 

Gano wallafa ta bogi

Ci gaban fasaha da bayyanar mutum-mutumi mai kwakwalwa (artificial intelligence) ya sake bayyanar da gano labaru na karya ta hanayar abin da ake kira gano wallafa ta bogi (“fake post generator.”)

Tattaunawa ta karya da yada labaran karya na ba da dama ga masu amfani da shafukan sada zumunta su rika hira ko wallafa wani labari da zai kama da na gaske amma karya ne.

 Irin wadannan dabaru ana amfani da su ne don nishadantarwa, ko zolaya ko a kirkiri wani labari don wata manufa, yayin da wasu ba su da illa ana amfani da su don raha, wasu ana amfani da su da gangan don yada labaran karya, kamar yadda wasu da ba a san suwaye ba ke amfani da su a intanet.

Ana amfani da dabaru a bada bayanai na karya  Fake Details. Daga Email zuwa Facebook da WhatsApp da Instagram da X da TikTok da YouTube, Bayanan na karya ana iya amfani da su a kirkiri sakonni ayi musayar bayanai da wallafa bayanai wadanda za ka gansu kamar na gaske, sai an yi masu kallo na tsanaki ne a gano karyar da ke ciki. Sanadin murdiyar da aka sanya. 

 Abin sha’awa a labarin da aka zargi ya fito daga shafin X na Mr Akufo-Addo an yi shine da irin wannan fasaha ta amfani da bayanan na karya. Saboda haka shima shafinmu yayi amfani da ba da irin wadancan bayanan karyar a shafin na (fake details) inda ya kirkiri wallafa a shafin X na gangan da sunan DUBAWA.

Kammalawa

Kalaman da aka danganta da Mr Akufo-Addo karya ne. Wallafar da aka kirkira a shafin na X  ba ta gaskiya ba ce, an yi amfani da bayanan karya (Fake Details) don cimma wata manufa ce.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button