African LanguagesHausa

Wani nau’in abincin Turkiyya ne ake kwatantawa a matsayin al’aurar maza

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: al’aurar maza “wadanda aka sace” a Abuja da Lokoja an saida su a matsayin nama kan daloli masu yawa

<strong>Wani nau’in abincin Turkiyya ne ake kwatantawa a matsayin al’aurar maza</strong>

Sakamakon bincike: Hoton da aka yi amfani da shi wajen kwatanta wannan labarin  na wani abincin Turkawa ne da ake kira “Şırdan.” Wannan abincin ba shi da wata alaka da Najeriya bare ma al’aurorin da aka ce an sace a Abuja da Lokoja. Wannan da’awar yaudara ce kawai..

Cikakken bayani

Sahihancin batun satar mazakutar maza na kasancewa sandin rikici a Najeriya, duk da cewa DUBAWA ta taba karyata wasu daga cikin zarge-zargen da aka yi kan labarin.

Kwannan nan aka samu wasu rahotannin da ke cewa an sace kayan aikin maza daga wasu yankunan Abuja, Kogi da Nasarawa, har ma batun ya kai ga hare-hare kan wadanda ake zargi da hannu a wannan matsalar. Duk da cewa akwai wadanda suka hallak sakamakon hare-haren, akwai wadanda suka yi sa’a ‘yan sanda sun iya ‘yan sanda sun iya kwato su kafin su ma su gamu da ajalinsu. Bayan da suka gudanar da bincike, ‘yan sanda sun karyata duk wani zargin irin wannan satar inda suka gargadi al’umma da su guji yayata irin wadannan labaran marsa tushe.

Bayan da aka sami wannan gargadin daga ‘yansanda, Rashidat Yusuf,  wata mai amfani da shafin Facebook ta wallafa cewa da gaske ne “kayan da aka sace din”  an saida su ne a matsayin nama a kan daloli da dama. Daga nan sai ta wallafa hoton nama a cikin wani karon tukunya, ana zargin ya yi kama da al-zakari. Sa’annan akwai wani mutumi cikin hoton yana raba abincin cikin kwanoni.

 that male organs “stolen” in Abuja and Lokoja were allegedly sold as meat for dollars. She shared a photo of meats in a big pot, purportedly resembling male genitals. A man in the same picture seemed to be dishing the meal on a plate.

Ta rubuta cewa, “Mazajen Abuja da Lokoja, ku yi hattara fa! Saboda kada a yi musayar kayayyakin aikinku da dala. Ba abun da turawan nan ba su ci, dubi duk wadanda suka bata a nan.”

Sadda mutane kamar su Aminat Yusuf, Aminat Attah, da Promise Amachagi suka tambaye ta sahihancin wannan zargin na ta, Malama Rashida ta cigaba da cewa kwarai “hotuna ba suwa karya.”

<strong>Wani nau’in abincin Turkiyya ne ake kwatantawa a matsayin al’aurar maza</strong>

Wannan ne hoton da Rashida Yusuf ta wallafa

Ganin irin wannan martanin da Rashida ta maida ne ya sa DUBAWA gudanar da bincike na musamman kan wannan batun.

Tantancewa

Un gudanar da binciken hotuna a manhajar google reverse wanda ya bayyana mana hotuna da ya masu kama da shi kuma dukkansu na da alaka da abincin Turkiyyan da aka fi sani da “Şırdan.”

Şırdan abinci ne da ake hadawa da kayan cikin dabbobin gida kuma abinci ne da ke da farin jini sosai a Turkiyya. A kan dauki tumbin tunkiya ne a jada da shinkafa, da yankakken nama, da albasa da timatiti, da barkono, da gishiri da mahi. Bayan nan sai a dinke shi da zare da allura a dafa shi, in ya nuna sa’annan a raba a ci. Idan ya dafu da kyau, siffar kan fito kamar al-zakarin namiji.

Şırdan abinci ne da ya fito daga yankin Adana, daya daga cikin biranen da suka fi yawan al’umma a Turkiyya. Kamar dai yadda ‘yan Najeriya ke sayar da Suya, wannan abincin ma haka ake saida shi a kan titunan Turkiyya da zarar yamma ta yi.

this street food is mostly sold by local sellers in the evening. 

Bidiyoyin YouTube a shafukan Yemekturkiyecom da Milliyiyici sun bayar da karin bayani kan hanyoyin sarrafa wannan abincin.

A karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa hoton da aka wallafa ba shi da alaka da Najeriya da ma abubuwan da ake zargi sun bata a Abuja da Lokoja. Wannan hoton wani abinci ne da ake ci a Turkiyya mai suna “Şırdan.” Dan haka wannan batu na Ms Yusufu yaudara ce.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button