Getting your Trinity Audio player ready...
|
A wajen da ke da taron jama’a da hayaniya, mutane biyu wadanda baki ne ga junansu, idan akwai harshe da ake yada bayanai za su iya haduwa nan take, a samu wata dama ta kulla alaka, a samu aminta da juna, amma a wannan zamani da ake yada bayanai ta intanet, wannan amintar da juna ana mayar da ita makamin yaki, kasancewar ana yada labaran karya cikin gaggawa, wannan ya sanya harshe ya zama wani makamin yaki mai karfi.
Kafafan sadarwar zamani kamar X (da a baya a ke kira Twitter) da Facebook da TikTok sun karfafa wannan batu ta hanyar hade wata al’umma da ke amfani da harshe guda a kafar ta intanet inda suka yi hadaka a harshe da aminta da juna. Mutane suna taruwa zagaye da wani mai karfin fada aji wanda ke magana da harshensu.-Wanda ta hanyar ba da bayanai yake iya juya lamura da janhankula na mutanen. Idan da’awa ta karya ta bayyana a irin wannan yanayi tana bazuwa kamar wutar daji a harshen da mutane ke ji sau tari ba tare da ma sun bincika ba.
Idan mutane na jin harshen juna ba makawa sai a samu fahimta da mutanen da suke yarensu ko ke baza bayanai da al’adu irin nasu. Kamar yadda bayanan masu suka nunar ne da irin tasirin hakan, haka kuma tasirin maimaita magana (Illusory Truth Effect), yawaita yayata bayanai na sanya mutane su aminta da abin da ake fada.Idan aka yada bayanan karya a harshen da mutane suke fahimta, musamman a cikin al’umma da ke a can kasa, suna jin cewa wadannan bayanai na gaskiya ne, wannan ya sanya harshen ya zama makami na sanya al’umma su aminta da bayanai ko kuma a yaudare su da shi.
“Masu yada bayanai na karya ta hanyar harshen da suke amfani da shi, na yaudarar mutane ta hanyar lalata asalin bayanin ko labarin su shigar da tasu manufa.’ Acewar Hamza Ibrahim, kwararren masani kan harkokin yada labarai na karya da ake yadawa.
“Su kan amfani da wasu dabaru kala-kala ta hanyar kari ko cire wasu muhimman bayanai sai a sanya wasu abubuwan ko kara tsara wasu bayanan ko yin sharhi ta yadda labarin karyar zai zama karbabbe mutane su yi ta sharhi akansa.”
“Idan mutane suka ji wani bayani a harshen su na uwa, sun fi saurin aminta da shi ” a cewar Danjuma Hassan masanin harsuna kuma masanin halayyar dan Adam, kalmomin da ka saba da su kafi samun nutsuwa da bayanan da aka yi da su, haka kuma kafi saurin amincewa da su. saboda wadanda suke saurara basa neman karin bayani ko da kuwa bayanan da suka ji na karya ne. ”
Masu fada aji a shafukan na intanet ko (Digital influencers) a Turance suna taka muhimmiyar rawa a wannan tsari. Ko da a ce farfaganda ce ta siyasa ko bayanan karya da suka shafi fannin lafiya ko bayanan karya da suka shafi tarihi, bayanan da aka ji a harshen na uwa ana saukin fahimtarsu, wanda kuma su kan zama da wahala masu aikin gano gaskiyar labari su gansu su yi aiki akansu su fayyace gaskiya.
TikTok da Harshe da Kwaskwarima
A wani bidiyo da ya yadu a shafin TikTok video na @Sani Aliyu638, ya nuna akwai tarin jama’a na hayaniya da ihu a harshen Hausa: “Sojoji muke so! Sojoji muke so!” yayin da hannu guda kuma suna daga tutar kasar Rasha, wannan bidio ya nuna yadda al’umma a can kasa suke kaunar ganin sojoji sun zo sun karbe mulki inda suke nuna ko za su samu goyon bayan wata kasa ta ketare.
A shafin na TikTok, bidiyo irin wannan na aiki a matsayin farfaganda inda yake nuna irin tasirin bidiyo da irin kalaman da ake fada da wadanda al’umma ke fahimta kai tsaye. Amfani da harshen na Hausa, harshen da ake amfani da shi a arewacin Najeriya da Nijar da wasu kasashe na yankin Sahel, kan sanya sakon ya isa ga al’umma a can kasa, duba da yanayin da ake ciki a wannan yanki sakon da suke son isarwa shine a nuna cewa al’umma a wannan bidiyo suna nuna bacin rai da suke ciki da damuwa da sha’awarsu ta mulkin soja maimakon mulkin dimukuradiya.
Yadda TikTok ke aiki yana daga bayanai ne, ko yayata su, baya banbancewa tsakanin asalin abin da aka wallafa da wanda aka yiwa kwaskwarima ko wasu ‘yandabaru. Da zarar abin da aka wallafa ya samu masu nuna sha’awarsu, zai ci gaba da yayatawa abin da ka iya illa ga dimukuradiyya.
Ga wasu shafukan ma irin su Sanialiyu638, nasi1germany, directorkano, danib714, danmakaranta62, sadeeqaminu90, hajjims_fashion_empire, ke3307077114701, user5272798653617, nansglobal, abubakarsadeec2, shamsuadamu8, farin_gani_furniture, oppicialbuk, play_station_and_xbox, ahmadmuhammad3398, kabir4331, lawanson190, ashirashir793, 03okasha, idrees_a_yareeko, princesaraki1, jaridararewa, a.y.el.mubarak.textile, daddy__jan__wuya01, da oppicialbuksuna yada bayanai inda acikin a salin bayanan sai su yi cushe da wasu bayanan karya na ketare da ake son cusawa al’umma.
Da dama irin wannan wallafa na samun tsokaci na masu amfani da shafukan masu jin harshen Hausa a wata fuskar kuma suna jinjina ga abin da suka gani a bidiyon.
Alal misali, Oppicialbuk ya yada wani bidiyon da ya dauki kansa a bayansa kuma ga dandazon matasa masu zanga-zanga tsadar rayuwa inda mutane ke yin tofin alatsine ga mulkin shugaban kasa yayin da hannu guda kuma suke daga tutar kasar Rasha.
Daya daga masu mayar da martanin ya rubuta cewa, “Allah ya baku nasara.” Wasu daga cikin masu amfani da shafin sun yi amfani da nuna hotuna da ke nuna jinjina wasu na yabawa yunkurin.
Nasi1germany, wanda ke da masu bibiya da dama kan wannan wallafa da yayi a dangane da zanga-zangar akwai wadanda suka kalla sama da 836,000 (views) da wadanda suka sake yadawa 9,337 (shares), da wadanda suka nuna alama ta cewa za a sake nazari a gaba 5,550 (bookmarks) da masu yin sharhi 3,885 (comments) da wadanda suka nuna sha’awarsu 60,000 (likes). Wannan guda kenan daga cikin tarin abubuwan da yake wallafawa a shafinsa na TikTok. Ga ma wasu misalai here, here, here, here, here, here.
Yayin da za a kalli wannan da fari a matsayin wani kamfe ko fafutukar kambama kasar Rasha, wadannan shafuka na yada labarai kala-kala da ke zama na karya ko wadanda aka yi amfani da fasahar AI wajen samar da wasu bayanai na yaki da dimukuradiyya da wasu bayanai da suka shafi al’ada, wadanda duk labaran bogi ne. Wani abun tashin hankalin shine an lura cewa a tsakanin irin wadannan shafuka wasu an tsara ne da gangan ana yada wasu bayanai cikin sani ko akasin haka, inda za ka ga mutum na yin wani kamfe da ma bai da masaniya a kansa ko irin illar da zai haifar anan gaba.
Hassan ya kara bayani da cewa sake maimata bayanai a harshen da mutane ke fahimta zai kara karfafa amincewarsu, musamman idan aka hada labarin da bidiyo ya kuma zama mai cike da ba da tausayi ko na daga hankali.
“Yadda TikTok ke aiki zai kara karfafa wannan tasiri inda zai ci gaba da kawowa mutum irin bidiyon da ya gani abin da zai kara karfafa masa gwiwa kan abin da ya kalla tun da fari, irin wannan bayani za a ci gaba da yada shi ba tare da sanin ma cewa ana yada labaran karya ne ba. A cewarsa.
“Mutane da dama na yada labaran karya ba tare da ma sun sani ba, suna yadawa ne don a tunaninsu labarin gaskiya ne, saboda ya dace da yadda suke kallon duniya dama tafiya da al’adarsu.Wannan ya sanya yada labaran karya cikin harshen uwa yafi saurin bazuwa saboda mutane na dauka labaran nasu ne kuma suna da alaka da su ta sosai.” A cewar Hassan.
DUBAWA ta lura da wasu kalmomi muhimmai (hashtags) da wasu inkiya da ake yawan amfani da su idan ana maganar siyasa don yada manufofi na masu iko a shafin na TikTok. Bincikenmu ya fahimci akwai wasu kalmomi da suke jan hankali, musamman a lokacin wasu abubuwa, cikin irin wadannan kalmomi sanannu sun hadar da
‘Gwamnatin Najeriya’ (Nigerian government), Zabe (election), Zangazanga (protest), Rikicin siyasa (political conflict), Yada karya (spreading lies), Talakawa (common people), and Daurin talauci (poverty entrapment), hadi da Russiya (Russia) da Arewa (Northern Nigeria), da yadda a ke nuna alaka da siyasar bangaranci ko karfin fada ajin wani yanki.
Jadawalin (Stacked Bar chart) na nuna yadda wadannan muhimman kalmomi ke yaduwa a shafin na TikTok
DUBAWA tagano wasu shafuka guda hudu a TikTok (nansglobal,kabir4331, lawanson190, jaridararewa, Nasi1germany) wadanda ke jan hankalin al’umma bisa kiraye-kirayen sojoji su zo su karbi iko, ta nazarci irin abin da ake cewa. Da dama cikin masu sharhi suna nuna goyon baya ne , inda suke neman sauya tsarin mulki zuwa na soja idan aka kwatanta da wadanda ke a tsakiya ko wadanda ke adawa da tsarin.wannan ya tabbatar da yadda mutane ke mayar da martani da ma nuna yadda harshe ke tasiri wajen yadda al’umma ke daukar bangare.
Wannan jadawali na infographic da ke a kasa ya nuna yadda wannan lamari ke jujjuyawa inda aka rarrabe tsakanuin muhawarar da ke nuna goyon baya da masu adawa da ‘yan ba ruwansu.
Wannan jadawali na Stacked column chart ya nuna yadda ake sharhi a shafin na TikTok a tsakanin shafukan guda hudu.
Wannan ya nuna yadda harshe da sabo da harshe ke rinjayar al’umma su dauki bangaranci, Ibrahim ya kara bayani kan yadda yadda masu yada labaran karya ke ribatar al’umma ta hanyar amfani da harshen ko yaren da suka fi fahimta, musamman a duniyar shafukan sada zumunta a inda al’umma suke.
Kasancewar wadannan daidaikun mutane basu ilimi na aikin yada labarai, nan da nan za a iya amfani da su wajen yada labarai marasa kan gado, ana yada labaran karya da yawa a shafin WhatsApp da Facebook, sau tari irin wadannan labaran ana isar da su ne ta harshen uwa da al’umma ke fahimta a juya tunaninsu da yadda za su yi wani aiki.” A cewarsa.
“Ana yada labaran karya a yaudari al’umma saboda ana tattaunawa a harshen da suka fi fahimta, musamman a shafukan na sada zumunta inda al’umma da dama suke tofa nasu ra’ayin.”
Tasiri cikin Al’umma
Yayin da shafin na TikTok da sauran kafofin sadarwar na zamani ke ci gaba da zama dandali na kyankyasar labaran karya, tasirin irin wadannan labarai bai tsaya a kafafan na intanet ba a arewacin Najeriya inda harshe da al’ada ke tafiya kafada da kafada, bazuwar labaran karya ana yinsa a harshen uwa wanda kuma bai tsaya ba a shafukan intanet: A tattauna akansa a cikin al’umma, abin da ke sauya tunanin mutane da yadda siyasarsu take har ma da batun tsaro.
Yanayi yadda iyaka take tsakanin Najeriya da makociyarta Nijar ya sanya cikin sauki mutane da kayayyaki da ma bayanai ana musayarsu. Da dama mutane daga Nijar na yin kaura su shiga Najeriya don yin ayyuka da kasuwanci da huldar zamantakewa tsakanin juna, hakan ya sanya al’umma ke sajewa da juna saboda yadda suke fahimtar juna a harshen Hausa da Kanuri.
Wannan al’ada da ke tsakanin bangarorin biyu ta taimaka wajen yada labaran karya cikin sauki, kai har ma da wadanda basa amfani da shafukan na intanet. Sakonni da aka yada su a shafukan TikTok kafin ka ce meye wannan na iya bazuwa ayi ta muhawara a kansu a kasuwanni da masallatai da tashoshin mota inda za su yadu a fatar bakin al’umma. Irin wadannan bayanai bayan lokaci sai ka ga sun samu karbuwa a tsakanin al’umma a rika ganin ma gaskiya ne don sun shige cikin al’umma sun saje.
“Harshe ba kawai makamin sadar da bayanai ba ne, makami ne na sauya tunanin al’umma a gargadin da Hassan yayi. “Abin da ya fara a matsayin jita-jita a harshen Hausa da Kanuri sannu a hankali al’umma ke karbarsa su dauke shi a matsayin gaskiya ya zama abin da ake tattaunawa yau da kullum ya sauya tunanin al’umma da ayyukan da suke yi a rayuwa ta zahiri. ”
Wa ke amfana daga bayanan karya da ake yadawa a harshen uwa?
Yada labarai ko bayanan karya a harshen da al’umma suka fi fahimta ko harshen uwa mutane da dama ne suke amfana daga shi, wannan ya hadar da masu alaka da kasashen ketare da ‘yansiyasa na cikin gida da wasu masu ra’ayi na daban. Ta hanyar yada labarai na karya a harshen da mutane suka fi yi wannan zai iya taimakawa a cimma manufofi da dama:
- Cusa bin ra’ayin wata siyasa: Labaran karya da aka yada a harshen da mutane ke fahimta kamar Hausa da Kanuri na iya sauya yadda mutane ke tunani kan harkokin shugabanci da zabe da kawayen kasashe na ketare. Ga misali kiran soja su karbi mulki ko kawo daukin wata kasa ta waje, wannan na iya girgiza tafiyar dimukuradiyya
- Fadada manufa: Masu tsatstsauran ra’ayi , masu yada farfagandar kasasen waje da masu wargaza sha’anin siyasa, sau tari suna amfani da harshe ne da al’umma suka fi fahimta don neman magoya baya ko su nemi masu adawa da gwamnati. Amfani da harshen da mutane suka fi iyawa na iya sawa su ji cewa abin da ake fada nasu ne, sai su ji fafutukar da ake tasu ce.
- Samar da tasiri da ke tsallaka iyaka: Da irin iyakar da ake da ita a arewacin Najeriya musamman a Nijar da Kamru da Chadi yaduwar bayanan karya a tsakanin wadannan kasashe abu ne mai sauki. Labari da ya yawaita a wata kasa zai iya tsallakawa zuwa wata kasar, abin da ka iya kawo hargitsi a yanki, ya kawo rashin aminta da gwamnati ko samar da wani bigire da ka iya kawo tasirin kasashen ketare na cusa wata manufa.
Karshe
Bayanan karya da ake yadawa ba suna tsayawa a iya kafar intanet ba ne , suna ratsawa cikin al’umma a zahiri musamman a yankunan da suke da iyaka da juna wadanda ke fahimtar harshe guda da al’adu irin guda. A arewacin Najeriya bayanai da suka fita daga wata kasa makociya kamar Nijar na iya jawo rashin gamsuwa da masu mulkin siyasa da ma ita kanta gwamnatin. Idan wannan ya ci gaba zai iya haifar da rashin zaman lafiya ya bude kofa ta tasirin kasashen ketare. Kawo karshen wannan na bukatar ilimantar da al’umma kan yadda ake yada labarai da gudanar da bincike na masu aikin gano gaskiyar labari a harsunan uwa da daukar matakai kafin lamura su yi karfi.